KIBIYAR AJALI 11
*11*
*Ranar* wata sanyayyar asabar da damina, Muka tashi da babban tashin hankali a karkarar mu ta Durbun. Bayan na temawa jinjiri mun gogewa Baffan mu jiki, Na bashi magani yasha, Sai na lallaba na tafi gidan Bara’atu koyo dinki. Gab da la’asar naji gaba d’aya banajin da’din jiki na. Daman haka na
Kwana jiya ban rintsa ba Ina tunani, Haka kawai na shiga zaryar hawaye daren jiya. Shin meyake damuna? Bansani ba.Mik’ewa nai kawai Bara’atu ta tsaya tana kallo na, Harhada
kayan dinkin na shigayi ina cusawa a leda,
“Dije! Meye haka?”
“Gida zani Bara’atu.
Raina sam babu dadi wallahi.”
“Subhan’Allah! Kiyita
addu’a kinji!? Amma ki dakata ki kammala dinke kafadar mana?”
“Aa Bara’atu. Sauri
nake yi wallahi. Bazan samu nutsuwa na Idan ban koma ba. Nagode sai kinji ni.”
Bantaba sanin wannan itace kalmar karshe da zata kara
had’ani da Bara’atu ba akan dinki. Banta’ba sanin wannan ce rana ta karshe da
zan sake zuwa gidan Bara’atu ba. Sallama
na mata na fuce, gaba na sai tsananta bugu yake. Tamkar zai fadi kasa, Haka na
kara sa gida gaba d’aya jiki na ya kara sanyi. Bantaba sanin wannan ce bakar
rana da rayuwata zata kara shiga ha’ulai ba. Bantaba sanin yau ne zan shiga
stage na biyu a fagen sabuwar rayuwata ba.
Baffan mu na tsakar gida a yashe, Fuskar sa tamkar yana
murmushi. Na karasa kusa dashi na zauna a gefen sa,
“Baffa na... Na
dawo.”
A duk lokacin da na dawo hakan nake yi, Dake bashi da nauyin
bacci, Dana fad’i haka zai farka yace min Sannu da dawowa yar Baffan ta. Na
sake matsawa kusa dashi na kamo hannun sa na dama, Tamkar na dau kara sam babu
nauyi kuma ya saki.
“Baffa na.. Baffa ga
Ummin ka fa! “
Nan ma shiru ba amsa. Gaba na ya tsananta bugu, idanuwana
suka kawo ruwa.
“Nashiga uku! Baffa
na. Gaji! Gajiyalle.. Ga Baffa baya motsi fa.”
Haka naita fada ina kai kawo a farfajiyar gidan mu.
Gajiyalle ta fito daga d’aki tana hamma hade da daga hannuwa tayi mika,
“Ya akai? Kincikawa
mutane kunnuwa da kururuwa, Meya faru.?”
Cikin hawaye shab’e sha’be na tsugunna ina rike kai na,
“Gaji! Baffa baya
motsi. Ki tayani mu dauke shi mu kaishi asibiti.”
“Asibiti? Can birni!?
Baki da hankali.”
Tsayawa tai akan baffan mu tana sakatar hanci,
“Bashari! Bashari!
Kai bashari! Meye haka ne.?? “
Kafa tasa ta shure shi, Ya rigingina bako motsi. Banbi
takanta ba na fuce ko dankwali babu, Na hango dandazon masu bin mai gari da shi
kansa mai gari jamilun da alamun daga zagayen gonaki suke,
“Mai gari! Dan Allah
kuzo kuga baffan mu baya motsi.”
“Assha gamu nan.”
Komawa nai ciki da sauri na zura hijabi gaba a baya. Gaba
d’aya bana cikin hayyaci na, Su mai gari suka shigo, dube duben su sukai. kafin
su mike kowanne jikin sa a sanyaye. (Allah ya jikan iyayen mu da rahama.)
“Ai Bashari dan
aljanna ne da yardar Allah. Kiyi hak’uri Dije, Duk kan mai rai mamaci ne, Yau
ga wanin ka, Gobe gare ka. Idan lokaci yayi dole a tafi. Kai Rabilu ku kama shi
ku sashi a dakin can ko, Domin a kintsa shi. Ungo Musa zoka yanko likafani,
Kace Malam na Masallaci suzo za’ sallaci Malam Bashari rai yayi halin sa, Ku
auno tsawonsa ku taho da makara.”
Kan baffan mu nayi, Matan da suka shigo suka rirrike ni, Na
kwace na rungume shi ina kuka,
“Wayyo Allah na Baffa
na. Dan Allah kakka tafi. Babba ka tsaya, Wayyo Allah na baffa. Shikenan gaba
da Baya bani da iyaye. Umma ta tarasu, Gashi Baffa sai ka tafi ka bar Dijen ka?
Wayyo Allah nashiga uku na lalace. Wayyo mutuwa mai yankan k’auna”
Wannan sune ka’dai kalaman da zan iya tunawa na fade su.
Daganan ban sake sanin inda kai na yake ba. Na yanke jiki na fadi. Ban farfad’o
ba sai bayan an kai ni asibiti a birni. Kwanaki uku mu kai acan nida tsahare
yar ladingo sannan muka dawo gida. Ranar sadakan ukun Baffa na. Addua kadai
nake iyayi sai kuka, abinci kuwa sai yan uwa na matsamin nake tsaku na, Duk
wani buri na wa na duniya na yanke shi. Jira kawai nake nima tazo ta dauke ni.
Astagfirullah Yaa Allah amma nikam nasan shikenan rayuwa ta yanzu zata kara
shiga cikin jarabawa.
Haka akaita zaman makoki har na tsawon kwana ki bakwai.
Gajiyalle tace wa mai gari tanada magana,
“Azo ai rabiyar gado.
Amma fa wani hanzari ba gudu ba, Mai rasuwar nan kafin rasuwar sa yace ya barwa
Mudi gidan nan wai yayi aure ya zauna.”
A razane na juya ina kallon ta, Yaushe sukai haka?! Allah ya
saka masa. Yan zaman makoki kowa ya shiga tofa albarkacin bakin sa. Mai gari
yai gyaran murya,
“Toh salamatu. Hakan
yayi. Amma ina rubutaccen kyautar da yayi.?”
“Yo wane rubutu?
Malam ya iya rubutu ne! Kai ma mai gari da tsohon kinibibin ka ta yaya Bashari
zai iya rubutu?”
Mai gari yai murmushin takaici yana gyara rawanin sa,
“Toh ina shedu?
Agaban wa da wa akai kyautar?”
Gajiyalle ta sosa kai tana zare idanu,
“Daga ni sai shi akai
haka, Zan yi k’arya ne?”
“Assha! Yaushe zan
karya ta ki a matsayin matarsa.? Kawai dai irin wannan babbar kyauta haka
yakamata ace akwai ta a rubuce ko anyi ta gaban shedu.”
“Toh dai na baka ta
rabaka da kayan ka. Wannan gida dai na Mudi ne.”
“Gaskia bai badu ba,
Domin ko gaban alkali zaki abinda zai sanar dake kenan. Saboda haka kiyi
hak’uri kawai, Domin Mudi ma Ai ba ‘dan cikin sa bane Salamatu. Ya zaai ga
diyar cikin sa duk duniya ita kadai ce jal. Ace ya tsallaketa ya baiwa agola
kyautar gidan sa sukutum? Wannan magana bata kamawa bace kiyi hak’uri. Gado dai
yau zuwa gobe Za’a raba shi. Ke ki nada tumunin takabar sa ita kuma diyar sa
tana gadon sa. Za’a raba ko dan saboda a sauke masa nauyin dake Kan sa.”
Gajiyalle ta dire tsallen albarka ta shiga zundumawa mai
gari ashariya tana karkada masa hannu. Mai gari ya murtuke fuska ya fice
mabiyan sa na bin sa a baya. Ba jimawa dangin Ummana suka Zo, Domin sai jiya
aka sanar musu. Sunyi mamakin ganin girma na, Ni kuwa na shiga raba idanu ina
binsu da kallo, Yan gayu ne sosai wanda suka shaki ilimin boko dana addini. Sun
jima sosai kafin su tafi bayan sun dire mana kayan abinci fal, Suka ce zasu
dawo nan ba da jimawa ba.
<><><>.
<><><>.
<><><>.
Bayan rasuwar Baffa
da wata biyu abubuwa da dama sun faru, Kamar raba gadon Baffan mu da akayi.
Gajiyalle ta samu gidan da muke ciki a matsayin tumunin takabarta ni kuma gado
na shine ragowar gonar Baffa guda d’aya dake bayan gari. Tunda ta samu gidan
nan yazo a gadonta na shiga 3, shiga dari fita dari sai tamin gori, Kamar ba
ubana ne ya rasu ta gada ba, Ta rata kawai nake. Kullum cikin addua nake. Allah
ya nema min mafita kawai. Gaba zatai dana sani. Haka rayuwar ta cigaba da
garawa. Kullum ta Allah sai na zubarda hawayen rashin iyaye na. Abincin da yan
uwan Umma na suka kawo ma ta siyar da rabi ta b’oye wasu.
<><> ••.
<><>••.
<><>••.
Ina cikin
da’ki ina kwance wajen shabiyu da rabi na dare. Na jiyo an bude asaberin dake
jikin kyauren dakin da na ke. Na nemi cocilan na rasa dakyar na ganta a gefen
hijabi na,
“Waye.?”
“Sssh! Ni ne nan.
Kwantar da hankalin ko. Had’in kai kawai
zaki bani. Na miki alk’awarin komai.”
Ta muryar sa na gane ko wanene?! Torchlight na kunna na
haske shi,
“Mudi.. Me kakeyi a
daki na a daren nan?”
Kasa magana yai sai kiciniyar cire riga da yai ya jefar ya
yo kai na na mike da sauri ina zura hijabi na,
“Mudi meye hakan.”
“Kiyi shiru dan
Allah! Wallahi zan miki duk abunda kikeso. “
Murya na rawa na shjga bashi hak’uri ina damke hijabi na.
Yayo kai na ya fincike zanin jiki na,
“Wayyo Allah na
gajiyalle..”
Ban karasa ba yai taku biyu ya rufemin baki,
“Ki saurare ni
yammata.. Ga ki da kayan aiki a tare dake, Karki zama mai duhun kai man-“
“Yayana ne fa kai
Mudi.”
“Uwa muka raba, Uba
kuma Kowa da nasa. Kingane? Ma’ana bamu hada jini dake ba.”
“Dan Allah karka
lalatamun rayuwa Mudi.”
Inata k’ok’arin kwace kai na, Shi kuma yana ko’karin ciremin
hijabi. Kafata nasa na tattake na dirka masa ita a gaban sa. Ya tsugunna ya
rike wajen da hannu biyu yana matse idanu, Ficewa mai da sauri ina kiran
Gajiyalle da mamaki na hangeta a kofar dakin tana lab’e, Tana gani na ta dubibi
ce tana haske hasken fitila, Ha’din baki ne? Ko kuwa so take ya lalata ni tamin
sharri da hakan? Ficewa nai da sauri banbi takan riko ni da take ba. Da tsakar
daren nan na tafi gidan mai gari, Dakin Ummita matar sa na shiga bayan anmin
iso, Na sheda mata komai, Wajen Kwana ta bani tace na kwanta da safe zata
sanarwa mai gari.
*WASHE-GARI*
Kiran sallar farko na asubah sai ga Gajiyalle tazo gidan mai
gari. Ta faffada masa karya da gaskiya, Mai gari ya kirawo ni da Mudi, akace
kowa ya maimaita abunda ya faru. Lalle Mudi yaban mamaki ya murtuke fuska yace
shi wallahi bai shigo gari bama sai safiyar yau. Naci kuka sosai, Bayan tafiyar
su Mai gari yaban hak’uri yace yasan ni ce mai gaskiya. Kwanana goma a gidan
Mai gari. Kafin na koma gidan Gajiyalle a ‘darare.
++ A kuma satin
ne jarabawar mu ta fito. Sai ga Malama Mardiyya har gida ta kawomin nawa.
Hakika nagodewa Allah domin bantaba kawo result dina zaiyi kyau haka ba. Ban boyewa
Malama Mardiyya komai ba na sheda mata. Taji rasuwar Baffan mu kwarai matuk’a.
A ramar ta sa na shirya mukaje birni na zana jarabawar jamb ta shiga Jami’a.
Sannan ta sani a mota na dawo gida. Tunda na dawo Gajiyalle ke hantara ta tana
yadamin magana kan naje yawon ta zubar. Ni kuwa murna nake na zana jarabawar
shiga jamia. Na cike gurbin masscom/journalism. A jamiar dake birni. Allah yasa
inada rabo amin.
Haka rayuwa taita garawa, Safiya ta zama rana, Rana ta zama
yammaci, Yammaci ya zama dare. Naci jarabawar shiga jamia karo ta farko, Na
samu gurbin jami’ar, Nanma Malama Mardiyya ta sake d’auka na ta kaini na zana
ta biyu wato post-utme. Alhamdulillah Allah abun godia. Kamar da wasa itama ta
fito na haye. Cikin haka yan uwan Ummana suka turo da maganar zasu turo a tafi
dani na koma wajen su. Gajiyalle ranar wuni tayi tana bakin rai. Na fita kitso
na dawo na tarar ta yiwa kayana fata-fata. Na kira Malama Mardiyya da y’ar
wayata mai torchlight na sheda mata komai tace nayi hak’uri.
Domin bafa masifa na dena
ba ko kad’an, Kawai dai na girma na kara sanin yadda rayuwa take. Duk
irin mugun bakin da take yimin nasan bazai taba kama ni ba domin mahakurci
mawadacine. A satin na wanke kayana tatas na goge na zuba su a ghana must go.
Gajiyalle ta wuni tana harara ta, Na shiga band’aki na fito naga igiyar dana
shanya underwear’s dina an yankota kayan sun zube. Tamkar an barbada musu toka
ma. Dauke su nayi na sake wanke wa saboda banason neman magana.
Ana sauran kwanaki biyu na tafi, Na zazzaga ya ko’ina a karkarar
mu duk gidan dana sani na shiga nayi musu sallama. Mai gari ya siyar mun da
gonata ya aikomin da kudin yace na sai kayan aure a birni. Na nannade kud’in a
cikin kaya na. Ranar da zan tafi ina duba kayan na nemi kudin na rasa, na fito
tsakar gida na hangi Gajiyalle da Mudi sun tasa jarida cikinta fal tsire ne
suna ci.
“Gaji! Waya daukar
min ku’di na acikin ku?”
Tamkar na zuba mata ruwan zafi haka ta mike tana surfamin
masifa, Kuma wallahi sune suka dauka, Na girgiza kai kawai na koma ciki na
dakko jakata dai dai lokacin da direban da aka aiko dauka ta ya shigo yana cewa
na fito,
“Gani nan! Ina
zuwa..”
Na fada masa, ya
gyad’a yai ya fuce bayan ya kinkimi jakar kayana. Duba na na mayar kan
Gajiyalle da Mudi.
“Shekara da shekaru
tun ina kankanuwa har na mallaki hankalin kai na, Baki dena kuntatamin ba, Kin
uzzurawa rayuwata. Kin sani cikin uqubar rayuwa. Sam bakyasan ganin cigaba na
sai dai lalacewa ta. Keda dan ki kuka hada baki don ya raba ni da martaba ta,
Allah ya tseratar da ni, Alhamdulillah na rabu da iyayen da suka kawo ni duniya
lapia, Tun Baffa na yana raye har yau rayuwata bata lalace ba duk da
kwadaituwar son lalacewar da kikeso kiga nayi. Duk sharrin da kike nema na
dashi baya samu na, Hmm sharri dan aike ne, Duk inda zai zaga sai ya dawo wajen
ka,
“Shin wannan bai isheki ishara ba? Kisani kwakwalwar yaro
bata manta duk abubuwan da aka yi mata na dadi ko akasinta. Ni Nana Khadija na
zamar miki kainuwa dashen Allah, Duk da yadda ba taso na rashin uwa ba
kyakkyawar tarbiyya hakan bai sa na lalace ba, Ni Nana Khadija na zamar miki
murucin kan dutse ban fito ba sai dana shirya, Nan gani nan bari wallahi
Gajiyalle, Na zama dakalin majina dole a hau ni a zame, Ni Nana Khadija na
zamar miki *KIBIYAR AJALI* wadda (sulke baya tare ta sai da ta wuce) Daukaka
yanzu na fara ta. Duk abubuwan da ki kai min na bar ki da mahaliccin mu, Zai
mana sakayya ranar sakamako, Kudi kuma da kuka sata kun dauki kudin cizo, Kina
ganin keda dan ki kunci bulus? Allah ya kara miki tsahon rai ki, Ki dade kiyi
‘karko kamar bishiyar dabino, Ki saurari dawowata Durbun, Zaki madaukakin
mamaki mai wuyar fassarawa. “
Ina gama magana nai ficewa ta na bar su a daskare kamar
shekararriyar kankara. Direba ya budemin mota na shiga muka dau hanyar birni.
Wannan ce rana ta karshe dana saka Durbun a idanu na. Munata wuce dajin Allah
bishiyo gasunan a jere da manyan duwarwatsu. Allah gwanin hikima!
“Ya Allah kasa na
shiga birni a sa’a, Allah kasa su karb’e ni hannu dubu. Allah ka bani ikon
cigaba da karatu na. Allah ka shiga lamura na. Kai ka iya, Kai zaka yi Ya
Allah! Ka temaki mareniyar baiwar ka Nana Khadija..”
Ina kammala addu’ar na shafa a fuska ta, Kafin na janyo
carbina na shiga azkhar na yamma, Na fada kogin tunanin yadda zan yi rayuwata
ta biyu, Sabuwar rayuwa a dangin Umma ta..
*KANO STATE*
*DR ISMA’EL MUHAMMAD SINGA RESIDENCE*
...
Ainihin labarin yanzu zamu tsoma ‘kafa cikin sa🥰😍❤️...
Oya put ya belts.. 😉The start of something new🏌️♀️🥂
ASHA HUTUN SUNDAY LAPIA❤️🥰..ZAFAFA FAM😘👋
______________________
KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN
BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.
To kuzo ga dama ta samu💃🏻💃🏻.
Ina ma'abota son a tallata musu
hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.
Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku
ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da
saƙo ta dalilin shafukan littatafai.
Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a
shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers
0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin
kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma
wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai
sauƙin gaske🤓.
Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike
neman sauƙi😻😻😄🤗.

No comments