Breaking News

A GIDA DAYA 41-42

 


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


      🌹A GIDA D'AYA🌹

            🏘️🏘️


🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾




    Story & written by mmn fareesa





🅿️ 41&42



......Abinda bazai tab'a yuyuwa ba kenan! khairat ta fad'a ahasale tana jifansa da wani irin kallo.kafin tace"nikaina banida burin Tara yara da yawa"atsarina yara 3 zanyi

suma sbd mahaifiyata naso tunda nikad'ai iyayena suka mallaka.kaga kuwa bbu maganar zubar da ciki indai shine.

Mahaifiyata burinta taga d'ana ko y'ata....kingama tatsuniyar?"yafad'a Yana tashi tsaye yatunkarota"cikin b'acin rai yace"mahaifiyarki bata Isa tasani ko hanani abinda naga damaba.ayanzun ta k'arfi zamuje asibiti inhar shine azubar dashi "sbd bana buk'atar sa.inkin Isa ki hana faruwar hakan"

       fashewa da kuka khairat tayi"tace wlh bantab'a zaton haka kake da mugun haliba!dabazan aurekaba"hhhhhhhh bakiga komaiba a halina sai anan gaba"natabbata saikinyi nadamar datafi haka wlh.yana fad'in hakan yafinciki hannunta suka shige bedroom d'inta.da tsiya yasata ta wanke jikinta "tasaka mayafi suka nufi asibiti...


Gwajin farko doctor yatabbat tanada ciki na sati 3"Jamil yace za'a iya zubar dashi doctor?


Doctor yace"subahanallahi muba ma zubar da ciki anan"sannan Yana a sperm d'insa bezama jiniba"wasu k'wayoyi zatasha shikenan zai fita....uffan kharat bataceba tana sauraronsu har Dr yagama bayaninsa.jamil yadubeta yace".tashi muje"batace komai ba tabishi suka fice"a reception yace ta zauna ta jirashi"hakan kuwa yayiwa khairat dad'i.yana b'acewa ganinta da sauri ta tashi ta fice...


     Cikin sa'a tasami adaidaita "tasanar mishi anguwar su bayan tashiga.

Bayan ta sauka tasallameshi ta shiga cikin gida.

    Hjy rabi da abban kharat na tsaye da alama rakkiya ta mishi zai fita "saiga khairat kamar anjehota"tasaki kuka had'e da fad'awa jikin mama tace wlh nagama Zama da jamil.baya Sona sai azabatar Dani yakeyi"yanzunma gudowa nayi dg asibiti yasaka azubar min da ciki na sati 3....Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un!  Hjy rabi da abban suka fad'a atare.abba cikin b'acin rai yace"dama ni kwata kwata yaron nan be kwantamunba.kece kika nace rabi sbd son abin duniya naki.to ga abinda yasaka mana dashi.ke kad'ai muka mallaka"zamuso muga y'a'yan ki"sbd haka saidai in kurabu akan azubba cikin nan wlh.abba yafad'a cikin b'acin rai.hjy rabi k'asa cewa komai tayi sbd jikinta yayi mugun sanyi.khairai kuwa kuka taitayi.abba yaja tsaki had'e da cewa Nina fita ko yazo karki bishi sai yayi mgn Dani tukum.bejira cewar suba yafice dg gida...


Jikin hjy rabi asansaye tace wa khairat ta wuce ciki ta kwanta "in kuluwa Mai aiki tagama aikace aikace zata yimata abun marmari...


Jamil kuwa lokacin dayaga bega kharat ba"ransa yabashi guduwa tayi"hakan yasa yatura mata text message kamar haka....

*wlh inma guduwa kikayi zubardashi bbu fashi "Kuma agabansu su iyayen naki zanmiki dukan dazai zube.kafin nabaki saki 3.banza wawiya y'ar gidan matsiyata masu kwad'ayi*...


Da misalin k'arfe 2:30 na rana"khairat na zaune kan kujera tana cin alalan wake "tajawo wayarta da nufin ta shiga what's app"taci Karo da text message d'in Jamil...wasu hawaye masu zafi suka wanke Mata fuska.afili tace iya sanina Jamil banmaka komaiba arayuwa !Amma zaka sakamun da haka harda iyayena.kai tir da auren me kud'i indai haka yake.natabba  inyaya mahmod ne bazaimun hakaba.tunda na auri Jamil banyi wani farinciki ba sai nasamun dukiya..kewai lfy kike surutu ke d'aya?cewar hjy rabi dake k'ok'arin zama kan kujera.cikin kuka khairat tace"Jamil ne yaturo sak'o nacin mutunci da zagi hardaku.... sbd yana d'an iska!me yace to?karantawa mata message d'in tayi.hjy rabi tasaki salati tana cewa anyi matsiyacin yaro...hmmm komenene mama bakece kikajaba"Ina rayuwa da hariki tunda akayi auren nan banji dad'i da kwanciyar hankali ba.na tabbatar inda Yaya mahmod ne bazaimun hakaba...gaba d'aya sbd kunya kasa cewa komai hjy rabi tayi.saima ta fad'a tunanin abinda suka aikawata y'ar uwarta nacin fuska.yanzun ta tabbatar in hjy hakeema taji saitamusu dariya.sbd rabanta da hjy hakimah kusan wata d'aya kenan.ko biki batazoba da gidan khairat duk batajeba.


Ajiye alalan tayi ta tashi ta wuce d'akin mama tasaki kukan bak'in ciki.


*Maharkurci mawadaci*


Zaune Khadija take agefen katifarsu"Yaya mahmod yayi matashin kai da cinyarta"idanunsa alumshe da alama bacci yad'aukesa.sbd Khadija takira sunanshi sau2 taji shiru.

Tunani takeyi aranta"jiyafa mlm yagama yiwa Yaya Mahmoud saukar alk'ur'ani Mai girma da rubucemishi shi"Yana wankewa da zamzam da ganyen magarya abashi yasha"yakuma shafawa idanunsa...

        Yaya mahmod kuwa baccin daya jashi acikin 5 minit"yayi mafarki gashinan shida Khadija acikin wani lambu"suna sanye da fararen Kaya ajikinsu.agefensu kuma yara ne 3"maza 2 mace 1suna zagaye dasu.yadubi Khadija yace alhmdllh my khady duk Ina ganinku da idanunawa na....hakan tsab acikin kunnan Khadija da sauri ta dubesa taga still idonsa arufe bakinsa na motsi...zumbur yatashi zaune Yana k'arewa d'akin kallo Yana murza idanunsa sa.

Khadija ta dubesa cike da mamaki da al'ajabi tace....


B'angaren kharat kuwa da misalin k'arfe 8:30 na dare Jamil yayi parking akofar gidan su"bbu neman izini yatura kansa acikin get d'in gidan.get man bece komaiba sbd yasan shine mijin khairat.


Awaiting parlour yashiga bbu ko sallama"fuskarsa ahad'e.cike da mamaki Abba da mama rabi kebinsa da kallo"Rai b'ace Abba yace"kaiiiiiiii!lfy zaka shigo Mana tamkar gidanka bbu ko sallama sbd jahilci kome?

Cikin isgili yace duk yadda kazata to kad'auka hakane.ina y'arku take?"nazo ne da kaina na zubar da cikin agabanku nakuma sallameta.kafin taga baya tasami wani Mai kud'i ta aura kobbu komai nasan namaida ita K'aramar bazawara"Kuma ke uwarta bakin samu kud'in dakike kiranta ta waya ta aikomiki dasuba.


Cikin fad'uwar gaba hjy rabi tace"sharri zakamun Kai d'an iska ammaka Rana kayiwa mutane dare...karki koma zagina"agidana inada CTV camera" komai da komai Ina gani... sannan....fitarmun dg gida kafin ranka yab'aci.abba yafad'a cikin fushi"sbd Jamil yakaishi mak'ura.zanfita Amma saina zubar da cikina dake jikin y'arku...Yana fad'in hakan yayi k'ok'arin shiga wani d'aki.hakan yasa Abba mikewa. Tsaye yanamishi tsawa "besaurareshi ba...da sauri mama ta fito ta k'walawa Mai gadi kira.aikuwa asukwane yayo iso da sandarsa a hannu"alokacin Kuma kharat na d'aki tana bacci taji Jamil ya wanketa da wani gigitaccen mari"tasaki k'ara arud'e ta farka taganshi agabanta...adedenan Abba yashigo d'akin Yana cewa"Kai wane irin matsiyacin yaro ne Wai?ka Isa kashigo mun gida kagayan mgn kadoki y'ata harka fita lfy bazai yuyuba.koda kaganni a dattijo lokacin kuruciyata banajin mgn.abba na fad'in hakan ya fisgo hannun Jamil ya wankeshi da Mari Mai Rai da lafiya.afusace Jamil yad'ago da nufin yacakumi Abba "megadi yabuga mishi sanda atsakar baya"yasaki k'arar azaba.abba najan tsaki yace fitomun dashi anan parlour.dole police  suka mashi"Banga wanda ya Isa yazo har gidana yacimun zarafi nida iyalina.yana fad'in hakan suka fito parlour baki dayansu.mai gadi yasaka rawaninsa yad'aure  wa Jamil hannuwa.abba yakira police yamusu bayani atak'aice"kafin yadubi Mai gadi yace"jashi ku tsaya a bakin get.sai huci Jamil keyi sbd yatsorata betab'a zaton haka zai faruba Aida ta lalama yazomusu "bayan yazubar da cikin saiya saketa.jansa yyi har bakin get.


Kharat na gefe na kukan nadamar sanin Jamil"yanzun da babanta ba jarumi bane"Jamil zai iya dukansa kenan?


Abba yadubi mama cikin b'acin rai yace"rabi duk abinda yaron nan yafad'a nasan zaki aikata"sbd nasan halin ki nason abin duniya"ga abinda yakaiku.kinzubar Mana da mutunci da k'ima a idon yaro akan mugun kwad'ayinki"bbu nasihar dabanmiki ba akan kibari ta auri mahmod "yaron y'ar uwarki"inada yak'inin ko bayan ranmu zai kula da ita.amma saikikace ai bayada lafiya bazata aureshiba.haka Allah yak'addara saita aure matsiyacin yaron nan.aigashi nan abinda yabiyo baya.inzama ishara gareki ruwanki! inkuma zaki d'ora dg inda kika tsaya damuwarki...iya nan yatsaya yaji jiniyar motar police hakan yasa yafita waje..


Jikin hjy rabi yyi sanyi"gaba d'aya nadama da Dana sanice aranta.ta dubi kharat saikuka takeyi"cike da tausayawa tace"kiyi hakuri khairat komai yafaru nice silar komai.uffan kharat batace ba ta nufi d'aki da gudu.


Abakin get kuwa saida"Jamil yarubutawa kharat  sakinta sannan aka wuce dashi police station.akan da safe Abba zaizo.bayan yasanar musu abinda Jamil yazo yamusu harda dukan kharat dason b'arar Mata da cikin sati 3.tun anan suka bawa Jamil rashin gsky sbd yataka doka.na zuwa har gidan mutum Kuma surikinsa yayi wannan rashin mutuncin.hakan yasa suka tafi dashi station...Da zumar da safe Abba zaije police station azuba mgn..


Cikin Isa alh mudi yafito dg cikin motarsa da aka bud'e mishi yafito"Yana wani baza malun malun..alh Ayuba yabiyo bayansa da sauran yaransa zasu shiga wani keb'antaccen guri da alama meeting zasuji".bayan shigarsu ibbi ma driver nashi yayi parking"ahankali yabud'e k'ofar motar" Yana zaune atsakkiyar y'an matansa su biyu(karuwai)yawanku cikin shigar k'ananun Kaya"yadad'e da eye glass black"Yana wani basarwa tamkar mace yafito yabar y'an matan acikin motar"


Abokansa su 2 dasuke tare dashi sbd abin hannunsa"suka biyoshi suna wasashi da kod'ashi had'e da fasa mishi Kai"suka nufi gurin taron...alh mudi na tsaye Yana brocal d'in turancinsa"Yana ta sakar musu k'arya da musu alk'awarirrika zaiyi kaza da kaza...yaji tamkar anwatsa mishi yaji a ido.da sauri yasaka hannunsa Yana murzawa"


Shiru yyi sbd ganin duhu duhu a idonsa.ihu yasaki had'e da cewa meyake faruwa jama'a duhu nake gani?"


arikice alh Ayuba yadubesa Yana k'ok'arin mgn yaji abinda alh mudi yaji a idanunsa....ihu yasaki Yana murza idanunsa..acikin wasu mintina Gurin yakaure da hayaniyar kace nace"gaba d'aya yaran alh mudi sunyi k'ok'arin sanin meyafaru dasu su duka duk sunzube akan Basu gani.hankali tashe ibbi yanufi securities d'in gurin yasaka suka tsaida hayaniyar da akeyi awajan.


Alh Ayuba nata zunduma ihu Yana Kiran ibbi"dacewa wlh baya ganin kumai.alh mudi kuwa tsabar tashin hankali suma yayi.hakan yasa akayi asibiti dasu.anan Kuma Nura yasami labarin komai"yyi vedio yyi rubutu bayan yayiwa wasu da abun suka faru agabansu tambayayi..saidai Kuma hankalinsana Gurin abokinsa.yana tunanin inhar mahmod ya warke to tabbas asiri kenan sukayimishi...da wannan tunanin yashige mota yanufi gidan mlm na Allah.


Khadija ta dubesa cike da mamaki da al'ajabi tace"....✍️

No comments