FURUCI 59-60
🗡 *FURUCI*🗡
💔💔
*(Murd'add'iyar Soyayya)* 💓❣💘
Story and written
By
NPEEDY A AJI 🌸mamyn Zarah🌸
🅿️59 to 60
Dedicated
To
My lovely
*Ummi*
and
Lovely
Daughter
*ZARAH*
My Novels
*NAYI RAYUWA DAKE*
*SANADIN ACCIDENT*
*SAKAYAR CUTA*
*RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*HAYATUL MAHAYAT*
*MUGUN SARTSE*
Loading....🖊
🗡💔FURUCI!!!!💔🗡
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
🅿 59 to 60
seda Iftahal tasake kwana cikin Asibitin sannan akabasu sallama kafin wani lokaci labarin haihauwar Iftahal yabazu ko ina Umma tanaji tace ay Ina itakam se USA su Abba kuwa jigin safe sukabiyo kafin wani lokaci tuni baqi sunfara sauka su Uncle kuwa tun kafin subaro Asibitin sukaje jama'a kuwa wasuma ba'asan suba amma sunzo ganin yan 4 Iftahal labarin haihuwar Iftahal ya iske Hjy Himla zaune take amma seda tami'ke tadaji cewar Iftahal ta haifi yara 4 wata irin ajiyar zuciya tasauke tace " yara 4 hmmm lalle yau kowa Yana cikin farinciki amma bandani dasannu zansaka kowa cikin tashin hankali " duban Abdul tayi dake gefanta tace " Abdul zanje USA barkar haihuwar Iftahal " murmushi yayi yace " tayay Momy bayan ayanzu mun manta dasu Suma sun manta damu karki manta tunda mukataho babu d'aya daga cikin su wanda yazo yace muyi haquri mukoma nide aganina karkije Momy sabida idan kikaje komi zai iya faruwa mubarsu kamar yadda muka kudurta " shiru Hjy Himla tayi tace kumafa hakane da wani shiri nike qullawa to amma yanzu katunasar dani idan naje na aywatar dawani abu to tabbas za'a zargeni tunda kowa yasan akwai takun saqa tsakanina da Saraki "
Jinjina Kai Abdul yayi yace " kingani kenan yauwa Momy mahaifin Lubna yacemin naturo iyayena sekiyima su Abba magana kinga kenan nakusa zama hamshaqin attajiri tunda dama sunce senayi aure zasubani dukiyata da mahaifina yabarmin Momy nankusa zan taka duk wani wanda naga dama amma abin haushina 1 har yanzu banida matsayin taka Saraki " duban shi Hjy Himla tayi tasaki ajiyar zuciya tace " hakane Sabida shi yariga yahad'a komi amma akwai wanda zamu had'a qarfi dashi wajan quntatama duk wani makusancin Saraki shine Alhaji Tukur " tsaki Abdul yayi yace " haba Momy wannan maikamada gawan tsayin watanni Yana kwance babu lafiya tayaya zamusamu abinda mukeso agun shi ? " Murmushi Hjy Himla tayi tace
" Yaro kenan ay seyatashi zamuyi komi Kuma yana gaf datashi sabida ayanzu haka munfitar dashi zuwa qasar daza'a yimai ayki yatashi " murmushi Abdul yayi yace " aha lalle zuciyata takusa warkewa daga baqin cikin danike ciki " dafashi hjy Himla tayi tace " qware kuwa "
Aunty Bahijjat zaune saman cushion ta d'aura baby saman cinyarta fuskarta d'auke da murmushi sanad'in jin haihauwar Iftahal jitake kamar tatashi sama taganta a USA yanzu sallama Akeey Zaffar yayi yashigo dubansu yayi yasaki murmushi yace " kaga uwa da 'yarta duk lokacin danashigo inajin farinciki marar misali musamman idan naga uwa da yarta agu d'aya Ina godiya ga Allah daya mallakamin wannan family Alhamdulillah " kafin Aunty Bahijjat tayi magana abokin Akeey Zaffar dake tsaye bakin qofar yashigo sallama yayi sannan yace " kabarni inatafaman tsayuwa kadage sefaman zuba kakeyi bakada niyyar yimin iso tonashigo Amarya kigafarceni "
Murmushi Aunty Bahijjat tayi shima Akeey Zaffar haka sannan yace " yi haquri ga guri zauna kasan duk mutumin dayasamu kyakkyawan family to idan yashigo gida mantawa yakeyi dakowa my dear wannan abokinane bamujima tare sosaiba shiyasa bakisanshi ba shidin police ne mataimakin Comishinan 'yan Sanda nanan munhadune sakamakon yarinyar shi dayakawo Hospital d'ina sunan shi Kabir Kabir yaude gaka cikin gidana " murmushi Aunty Bahijjat tayi suka gaisa sannan tamiqe taje kawome abun motsa baki binta Baby tayi aguje murmushi Kabir yayi yace
" Lalle baby kamar bakiga dady ba kinbi Momy " murmushi Akeey Zaffar yayi yace " hmmm inde baby ce bazata zaunaba sede idan Momyn tata tana wajan " jinjina kai Kabir yayi yace " to amma Zaffar kace ko shekara bakayi dayin aure ba ? amma gaku da 'ya wadda akintacena zatakai 5 yes ko ? " ajiyar zuciya Akeey Zaffar yayi yace " eh tabbas baby 'yatace tacikina amma Bahijjat ba'itace Mahaifiyar taba tata Mahaifiyar tadad'e darasuwa tun wajan haihuwar ta amma yanzu gashi baby tasamu wata uwar tamkar itace tahaifeta idan banine nafad'aba ko Wanda yasani babu maiganewa "
" jinjina Kai Kabir yayi yace Masha Allah tabbas kayi dacen mata " dede lokacin Aunty Bahijjat takawo musu ruwa da kayan ciyeciye " tsayin lokaci Kabir Yana gidan Akeey Zaffar sannan yayi musu sallama yatafi bayan yayima baby alkairi da kud'i masu yawa bayan fitar Kabir Akeey Zaffar yadubi Aunty Bahijjat yace kushirya gobe zamutafi USA ganin yan 4 " tsalle aunty Bahijjat tayi ta rungumai shi had'ida manna mai kiss a kuncin shi
Cikin masarauta kuwa kowa yace zashi hakan yasaka kaka cewa Sarki Zaid yatafi shida Umma dasu Aunty Faheemat su saje shida mama daga baya hakan kuwa akayi
USA
Su Abba nasauka daga jirgi akazo tarbarsu anashigowa cikin harabar gidan Abba yadubi Ummi yace " ikon Allah kenan lalle yau duk wata tantamata ansharemin ita wajan mamakin kud'in sadakin da Maher yabiya akan Iftahal wannan irin gida haka " murmushi Ummi tayi kafin tayi magana aka bud'e musu murfin mota suka fito har cikin part d'in su Iftahal akakaisu kwance Iftahal take amma cikin sauri tami'ke danufin Isa wajan su Ummi juwar dataji tad'ibaita yasata dole takoma tazauna cikin sauri Ummi taqaraso ta rungumai Iftahal hakama Abba kukan farinciki Iftahal tasaki tsayin lokaci suna ahaka sannan suka zauna kafin wani lokaci akacikasu da nau'in abinci kalakala babu jimawa Sarki Zaid da Umma dasu Aunty Faheemat suka iso suna shiga Akeey Zaffar da Aunty Bahijjat da baby su Suma suka iso kafin wani lokaci gida yacika da d'inbin jama'a kamar yadda Abba yayi alqawari Kuma yacika shine wanda yatauna dabino yabama kowane jariri sosai su Maimartaba sukayi murnar ganin Abba cike dafarin ciki agun 'yarshi bayan yagama yadubi Maher yace " kayi musu huduba " cikin jin kunya Maher yace " a a Abba nabaku dama " murmushi Abba yayi yace to Ina godiya da wannan kyauta to amma wane suna kaza'bar musu ? murmushi Maher yayi yace " mazande kasamusu Abba na da Abbee na amma matan nabaku dama dubada su 3 ne kakannin nasu ga Umma ta gakuma Ummi na sannan kuma Ammi na bansan waze ha'kura ba "
Dariya kowa yasaki cikin murmushi Ummi tace a a ni nahaqura zuwa gaba nasamu tawa takwarar " dariya suka sake saki duban Sarki Zaid Abba yayi yace " to nabarmaka matan kayi musu huduba kaine kasan sunayen nasu kaga kenan kai tsaf dakai kasamu wasu matan yara shakaf " dariya akasaki bayan angama huduba Zaid Ishaq Karimat Batol duban Iftahal Sarki Zaid yayi yace to " gimbiya nasan dele zakusaka musu wani sunan na alkunya wannan kuma kece yakamata kifitar " cikin jin kunya tace " nabama su Aunty dama "
Tana rufe baki " Aunty Bahijjat tace " toni zanfara fad'in nawa Irfan " murmushi kowa yayi yace Masha Allah cikin sanyin murya Aunty kurrat tace " kaga yarinya wato yau kece babba ko ? shikenan tonima naza'bi Ibban " masha Allah kowa yace se Aunty Faheemat tace " nikuma Islam " Nanma Masha Allah sukace se Aunty Sumeer tace " nikuma Iman " Masha Allah nanfa kowa yacika dafarinciki Zaid shine Irfan Ishaq Ibban Karimat Islam Batol Iman "fad'in irin shagalin da'akasha bazai yiyuba Amma kunsan ansha shi'ani
Akwana atashi asarar mai rai bayan wasu shekaru Maher yakammala Skul d'in shi hakama Iftahal amma sunqi komawa Egypt shikam Maher ayanzu yashihara inde sari'ace tofa baya ta'ba fad'uwa ayanzu qasashe ake zuwa d'aukar shi tsayawa sari'a yara sunyi girma sosai se yanzu Iftahal tasamu wani cikin tofa Alhaji Tukur yawarke kuma Yana nan akan bakarshi hakama Hjy Himla Aunty Bahijjat kuwa itama se yanzu tasamu ciki ayanzu cikin nata 2 months yana matuqar wahalar da ita sosai Aunty Shukura ayanzu yaranta 2 Ummi itace babba se Junior me sunan dadyn Zayyat shikuma Yaya Ibrahim yaranshi duka mazane Sadeeq da Haidar
Egy
Baby an girma misalin 8 safiyar litinin tuni Akeey Zaffar yafita hospital cikin shagwa'ba baby tace " Momy gaskiya yau kece zaki kaimin abinci Skul Ina shi'awar haka " murmushi Aunty Bahijjat tayi tace " angama baby na zan kawo miki haka kuwa akayi dakanta takai mata abincin misalin 5 pm Akeey Zaffar yadawo shida abokinshi kabir suna shigowa baby tadawo rungumai Aunty Bahijjat tayi sannan Akeey Zaffar se Kabir sannan tashiga cikin bedroom d'in ta abinci Aunty Bahijjat tashiga kitchen ta d'akko Mata takaimata sannan tafito abinci takawomasu Akeey Zaffar sannan takoma bedroom d'in ta kamar 20 minutes sukaji ihun baby cikin bedroom saurin tashi sukayi sukanufi bedroom d'in itama Aunty Bahijjat cikin sauri tafito suna Isa suka tadda baby kwance saman Carpet tariqe ciki wani irin farin kumfa yana fita daga bakinta cikin sauri sukayi kanta aguje Akeey Zaffar yafito kayan kwaji yad'auka cikin sauri da rud'ewa yake dubata amma Ina kafin wani lokaci baby tace ga duniyar ku nan cikin tashin hankali Akeey Zaffar yadubi Aunty Bahijjat yace " my dear guba acikin abincin Baby daga Ina " cikin gigita Aunty Bahijjat tace " guba Kuma jinjina Mata Kai yayi yace tabbas " kuba baby taci irin kumfan bakinta ya'isa tabbatar dahaka kuka Aunty Bahijjat tasaki tace " wallahi bansan daga Ina akasamu guba ba " sosai Kabir yadubeta yace " kamaryafa Bahijjat amma kuma idan bakisaniba tayaya abinci yazama kala 2 wanda Kika bamu daban na baby Kuma daban ? " Cikin tashin hankali matuqa tace " wancan Wanda nayi da ranane shine nakaimata Skul ganin taci irinshi darana yasa senayi Mata wani " sake dubanta Kabir yayi yace dama kin safa yimata haka ? " girgiza kai tayi cikin tashin hankali cije lips d'in shi yayi yace " kenan sabida yau kin shirya wani abu shine kikayi hakan ? Cikin furgici Aunty Bahijjat tace " bangane Mai kake nufiba Kabir ?" Cikin fusata Akeey Zaffar yadubi Kabir yace wannan tambayoyin naka mesuke nufi kana nufin kace Bahijjat itace tasaka guba cikin abincin baby ? Ina Bahijjat bazata ta'ba kashe baby ba itada 'yarta "
Jinjina Kai Kabir yayi sannan yace " to ayanzu Kam sekabari bincike ya tabbatar dahaka "
Comments please

No comments