Breaking News

DUK NISAN JIFA 50


 🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾

          *DUK NISAN JIFA*

           _(K'asa zai dawo)_

🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾🎾


            _RUBUTAWA_


               *SAJIDA*


        *SADAUKARWA*


                   *GA*


           *MASOYA NA*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_




                            50



Hisham yi ya yi tamkar bai ji shi ba hakan ya sa ya tuka su har gaban katuwar pharmaci mai sunna NWALA


HISHAM din ne da kansa ya sauka cikin nutsuwa ya nufi wajen Pharmaci din 

Bai jima ba ya fito ya dawo bangarensa ya bude ya shiga sannan ya amshi ledar da yaron wajen ya riko masa yana daga masa hannu


Ajiyewa ya yi yana sauraron shashekar kukanta a hankali ya lumshe  idannuwansa yana sauraronta Kader kuwa na fafala gudu a saman kwontaciyar kwaltar suka nufi gidan


Sunna zuwa Hisham ya dubi kader muryarsa dai cen ciki ya ce" To koma gidan ka gama bikin ko? "


Kader ya kale shi  da mamaki harda rike baki ya ce" Ai ba haka muka yi da kai ba na fada maka na tsara mana wuni da abokanai kuma harma fareeda ta cajeni kudin kitso yanzu in baka je ba laifina zata gani, kuma da kace na je na wuni da mutane yo nine angon hala? "


Hisham ya dan yatsina bakinsa a hankali ya ce" Ai dama ni bance maka ka yi wani wuni na rashin aikin yi ba, kuma farida ta ga laifinka mana ina ruwana, ka ga ka tafi ba zan fitar da ita kana tsaye kana irga min takuna ba dan bakar jaraba!"


Kader ya gyada kansa ya kankance ido ya ce" Ka yi da mutun Hishamu! Da ni kake zancen kuma sai na koma na sa an zo an dauki marainiyar Allah kar a shiga hakinta!"


Shi dai yana kallonsa ya gama bude buden cofre din motar sai kuma ya juyo yana kallonsa  ya sasauta muryarsa ya ce" Dan Allah bani kudin kabou kaboun ka ji? "


Hisham ya yi dan murmushi ya karkata ya ciro gaba daya cenjin aljihunsa ya mikawa Kader


Kader ya dan zarro ido da sauri ya yi raf da kudin ya bude ya fita, sai da ya dan yi nisa ya ce" Ka kuwa ga kudin da ka jibga min? " 


Hisham ya dan dafe gaban goshinsa kafin da yan yatsunsa ya masa nunin ya tafi


Daria Kader ya yi yana jinjina ya ce" Kai dama kulun ake daura aure ka yi ta bani wannan Allahma ko"


Kasancewar kasan katuwar runfar motocin ya ajiye su ya saka ba rana sai inuwa duda ba mai sanyi bace inuwar aman kuma bata da zafi


A hankali ya sauke ajiyar zuciyar tunanin da ya sha kansa a nitse ya bude ledar nan


Bai ce komai ba ya fitar da yar kwalbar garin allurar sannan ya fitar da ruwan da sering

A nitse ya zuki ruwan ya bale farin marfin dalmar garin allurar ya soka ta saka ya fesa ruwan ciki

Dan jijiga shi ya yi da kyau sannan ya kuma zuka a cikin seringer din sannan ya dora farin marfin allurar ya rufe ya saka a gaban aljihunsa a hankali


Cikin nutsuwa ya buda bangaren da yake zaune wanda hakan ya yi daidai da bugawar zuciyarta domin a jikin kujerar take a jingine idannuwanta lumshe ba wai barci ne take yi ba idannuwanta bude kuma dukan motsinsu tana ji hakama dukan motsinsa daidai da bugawar zuciyarta ne


Bata ji kamar numfashinta zai tsinke ba sai da ta ji ya bude bangaren da take , da sauri da sauri kuma numfashin nata ya shiga bugu, abin lafayar da ta saka ta rufe fuskarta sai ta ji tana neman hanna mata numfashi, gaba daya sai ta ji kofofin hancin nata sunna neman donewa 

 

Da sauri ta saka hannunta ta janye abin tana mai bude manyan idannuwanta tana neman janyo numfashi daga bakinta dan ta daidaita kanta


Gaba daya fuskarta da yannayinta yake kallo daga irin rankwafawar da ya yi a jikin motar hakan ya sa itama ta dago dara daran idannuwanta ta saka cikin nasa


Idan ba gizo take ba gani take kamar gaba dayansa rufowa kanta yake neman yi, hakan ya sa nan da na  ta tsayar da dan hakin da take ta kurawa kyakyawan sajen fuskarsa da jajayen lebunansa ido tana gannin yadda yake kara kure mata waje 

Bata ankara ba ta ji kamar an mata wani wawan tsimko a cinyarta wajen da bata san a lokacin da har ya yaye mata shi ba har ya tara wajen nama ya soka tsinin allurarsa a hankali ya matsa ruwan ciki


Wani irin ihu ta saka hakan ya sa da sauri ya zare bayan ya gama zuba ruwan allurar ya rufe allurar da sauri ya duka wajen da ta rinrintse ido tana rawar jiki gaba daya tana murzawa da dukan karfinta ya dora hannunsa saman hannun nata a hankali ya dauke ragamar murzawar ya shiga murzawa a hankali tare da hannunta stil yanna kallon fuskarta da lebunnanta da take cijewa har sun kara ja a kan kalarsu ta pink color


A hankali ya lumshe idannuwansa muryarsa cen ciki a sanyaye ya ce" I'm sorry angel, i'm so sorry"


Kuma zubawa fuskarsa ido ta yi wadda ita kanta bata sannin da ta aikata hakan , a hankali yale cire idannuwansa daga cikin nata har ya kai kansa saman cinyoyinta da ya janye doguwar rigar dake jikinta mai santsi da laushi fara kal wace tati ta cenza mata bakar ta jiya


A hankali ya zubawa cinyoyin ido, fararen cinyoyin nata da basa dauke da gashi a jikinsu sai yan hudojin gashishikan wa'inda bata barin jikinta da gashi du kuwa da irin yadda take da saurin fitar da gashi da izgar gashi a jikinta baki daya

A hankali ya dora hannun nasa da kyau kafin ya shiga dan shafa wajen allurar maimakun murza matan da yake da farko


Zabura ta yi a bayane ta ce" HAMMA ya daina zafin zan tashi "


Ta fada tana saka hannunta cike da kunya da tsoro tana jan rigar tata da kyau dan rufewa


A hankali ya dago dubansa  ya dora saman fuskarta wadda hakan ya saka mata faduwar gaba sakamakon gannin yadda idannuwansa suke lumshewa haka kuma sunna dan kankancewa ga wani cenza kala da suka yi sannan suka bushe , sai dai ta dake sosai tana sauke boyayiyar ajiyar zuciya


A hankali ya dauke hannunsa ta ringa ja tana rufewa tana kara jan rigar tana ta jimke hannayenta


A sanyaye ya muke tsaye sannan ya saka hannunsa ya kamo tafin hannunta a hankali ya janyota ya fitar da ita


Kanshin turaren da take ya rasa wanene , haka kuma sosai kanshin ke shiga jikinsa bai san dalili ba


A nitse ya shiga tafia da ita sunna jere yana rike da hannun nata yana dan murzawa yana jin zafin jikin nata ta haka


Gidan take dan bi da kallo , irin shuke shuken gidan kwarai ya bata sha'awa, haka kuma ta kasa hanna kanta bin bayansa har sai da suka zo kofar baban falon ya saka hannunsa a wajen budewar ya bude ya fara shiga a lokacin ne da ya sakar mata hannu ta iya ja ta tsaya ba tare sa ta bi shi ciki kamar rakumi da akala ba


Daga inda take tsaye sansanyan kanshin turaran wuta da sanyin AC ne ya huro mata, hakan ya saka ta kara zuba ido tana kallon yadda yake tafia, tsayinsa fafadan samansa wajen kafadunsa, rikaken kugunsa ginanun kafafuwansa, dogayan hannayensa da ko a cikin rigar basu boye kansu ba gashin da ya dan fara fito masa irin ya fara taruwa da dan yawan nan sai shadar jikinsa dake maiko


Ja ya yi ya tsaya a lokacin da muryar mace ta fara amsa salamarsa a sanyaye hannunta rike da jug


Da sauri Bilkisu ta dan rike wajen garun tana jin yadda zuciyarta ke dokawa da karfin balaki kamar zata balo kirjinta ta fito haka take ji


A sanyaye Aisha da ta wuni cikin yannayi na rashin jin dadin ranar haka kawai sakamakon sannin da ta yi cewar mijinta ya tafi daurin auren abar kaunarsa ta ce" Aa, Docter gajiya ce ta koro min kai tun yanzu?"


Hisham dake kallonta ya kai kugunsa zaune da dan murmushi a fuskarsa ya juya dan bai ji ta yi magana da Bilkisu ba bayan ya san tare suka shigo


Hango Bilkisun da ya yo tsaye tana kallonsu ne ya saka shi shan jinnin jikinsa, aman sai ya dake ya ce" Ki shigo mana Billy ?"


Aisha gabanta ya fadi ta juya wajen da ya kalla ya yi magana a hankali ta ce" Billy? "


Sai kuma ta yi gagawar cijewa tana dan fitar da idannuwanta na mamakin nan ta ce" Aa, amaryarmu? Ya haka zaki coge a kofa kamar ba gidanki ba? Shigo mana..... ta faada tana nufo kofar da Bilkisu ke tsaye wace gaba daya komai a kan idannuwanta haka kuma a cikin kunnayenta


Da karfin hali Aisha dake sanye da atampa golding an mata dinkin riga da zani sosai sun karbi jikinta ta kamo hannun Bilkisu  tana fadin" Aa, ya haka jikin nake ji kamar da zafi likita lafia? Daga kuke haka ka ji jikinta da zafi fa?"


HISHAM dake zaune ya gyara zamansa yana aikin da ya fi kwarewa a shi watau kallo, ya zuba masu maganadisu yana mai binsu da kallo uwa uba fuskar Bilkisu yake kallo yana so dole dole ya ganne yannayin da take ciki bayan sam ta ki bada damar haka, hasalima tun ihun da ta yi ya ji muryarta sai shahsekar kukan da yake ji nata shi kansa ya ji muryarta sai inda ta cewa tati a maidota da wuri


Aisha ta zaunar da ita saman kujera tana fadin" Aya bara na dauko maki magani wannan zafin jiki ai sai ya ilata mutun


A sanyaye Bilkisu take binta da kallo ta ce" Aa, ba sai kin dauko ba Aisha an min allura"


Aisha ta ja ta tsaya ta juyo tana sakar mata dan murmushi ta ce" To bara na kawo maki jus ki sha ki ci abinci ko zaki ji sauki "


Bilkisu da ta fara kosawa da bada amsar ta dan rike lafayar dake son sauka daga saman kanta ta shiga kiciniyar tashi har ta mike tsaye ta ce" Aa fa, kin ga ai na karya kuma gida zan koma yanzun ki barshi walahi na gode sosai"


Kara gyara zamansa ya yi yana kallonta da gannin iya gudun ruwanta


Aisha kuwa itama ta dubeta da mamaki ta ce" Gida kuma? Daga zuwa sai tafia? Na zatama ko kin zo ne irin nawa? Ke da gidanki kuma daga zuwa sai tafia ?"


Bilkisu  na kallonta tana jin dukan magamgannunta kamar da biyu ne sakamakon haushonsu da take ji su dukansu ta dan kalli yannayin katon falon mai dauke da manyan labulaye da katuwar TV da kafet tafkeke mai kwai, da table da tsakiyar falon da manya manyan po na gilas masu wani irin ado ta maida dubanta kanta , a hankali ta kakaro murmushi ta lumshe idannuwanta ta ce" AA, wannan din gidanki ne "


Aisha bata dadara ba domin ita ta yi mamakin ya ce yau ne daurin auren harma ya hannata zuwa ya ce ta zauna ya je ya dawo kuma sun dawo tare ga kuma maganar da take fada sai take son sannin shin an daura din ne ko yaya, dan haka sai ta ce" Gidan mijinki ai gidanki ne kanwata, ki zauna ki huta ko lafia baki da kin gani"


Bilkisu ta kuma sakar mata murmushi wannan karron amsar ta mijinta ce ba tata ba dan haka a gajarce ta ce" Mijinki dai, ni bani da miji, ya sake ni sai na samo wani"


Tana gama fada ta sauke dubanta a kan fuskarsa kafin ta juya a hankali tana jin wani irin daci a zuciyarta ta shiga tafia


Bata san yaushe ya mike ba, batama san ya iso inda take tafiarta ba sai ji ta yi ya kama hannunta ya juyo da ita gaba dayanta ta yada tana kallon kofar shigowa sai da ta dawo kallon TV cen falon 


A hankali ya dora hannunsa a kan habarta ya dago da dubanta ido cikin ido muryarsa a sanyaye ya ce" *NI NE MIJIN KI BILLY AM, BAKI ZAMA DAYA DAGA CIKIN SHAIDUN DA MUHAMMAD  YA AMSHI AURENKI A HANNUN ABA JAURO BA?* "


Idannuwanta ta lumse, du irin yadda gabanta ke faduwa, hankalinta ke  tashi, tsoronsa ke shigarta duda a sanyaye yake mata magana a nitse ba tare d aya mata hargagi ba ko muguwar magana ba aman a hankalce take da girman bacin ransa kuma a sgirye take da ta dakatar da neman fitinarsa a kowani lokaci idan har ta gane lokacin hakan ya yi ta hanyar cenzawar yannayinsa

Fuskarta ta kwashashagwabe sosai ta dora dubanta a kan hannunsa da ya riketa da karfi a cen kasan makoshi ta ce" AUSH zafi hama am, ka sasauta min rikon kar na ji ciwo"


Irin yadda ta ajiye maganar ta hanyar kara jan kalaman sai da tsigar jikinsa ta tashi, ya shagalta kwarai da kallonta yana jin inama inama, inama a duniyar baki daya daga shi sai ita ne, da yana tunanin filin da wuya ya iya isasu zagaye, da yana tunanin lokacin ba zai ishe su zama ba , gadajen duniyar da sun masu kadan, shi yasa  yake auna kalamansa yana tunanin ta inda zai fara? 


A sanyaye ya ce" ME YASA KIKE SON WAHALAR DA NI BAYAN KIN SAN RAGO NE NI A GABANKI, ME YASA KIKE SON KI BANI WAHALA BAYAN KIN FI KOWA SANNIN BANI DA WANI KUZARI A GABANKI?"


Sosai ta cije ta samu kwarin gwuiwa da karfin jiki tana dubansa a hankali hawaye suka shiga zarya a kumatunta ta ce"  HAMANA ina cikin tashin hankali da rudu ne, shin ina maganar MUN SHA NONO DAYA da Hammana ne?, shin ina maganar da kake fada min kaine magabacina kai zaka sama min miji ne ? Wai an daura min aure da yayana?, yayana fa? Hamma am ina zan shiga da wannan abin tashin hankalin abin kunyar?, kawayena fa ce masu nake ubana ne hammana uwarmu daya ubanmu daya ina zan shiga da wannan nauyin, aure fa? Wani kalar zamu raya da hammana ko bani da rabon zaman aure ne ni?, hammana tausayinka nake ji gannin tun ban kai ko'ina ba za'a fara irga min aure idan ka fita cikin mutane a ce shine wancen ne aka kuma yiwa auren da kanwarsa shima ya sauta, Hammana har an fara tunanin ko wani lamari ke tatare da ni marar kyau?, hammana yaushema ka santala aurw da auntyna?, ina zaka shiga da mace biyu, hammana mijin Aisha ne ba Bilkisu ba, tunanina na neman tsayawa ne bayan na san a yanzu na fara raja'a alkibilata a kan wanin hammana sai suka yi maka haka?, Hammana ba laifina bane, kuma ka tambayi Aba, hammana ka sawake min a laluma zan je na fadawa Allah ya shiga lamarina ina da damuwa Hammana gani zan zama bazawara ta biyu bayan ni ba zan taba hada miji da kowa ba?, ni bana son mijin wata ko wanene............nawa nake so hammana kuma zawara ta ina zan fara nema?, wannan shine ya hadasa min ciwo, ciwo na damun zuciyata hammana............." ta karashe tana mai rintse idon matsar dake kara shiga hannayenta da wani irin zafiin da bata shirya ji a yadda jikinta ke dandatsarta ba, sai dai ta dauri niya daga shi har matarsa sai ta karyata masu tunaninsu a kanta, idan tunaninsu ta mace a soyayar Hammanta ne? To bismillah


Dan ihu mai hade da dan kuka tana fido idannuwanta ta nemi saki da dan karfi ta ce"







😁😁😁😁😁😁😁

No comments