Breaking News

SAI A LAHIRA 9


 *🎀SAI A LAHIRA🎀*


              *NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




               *🅿️age 9*




*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 

*_____________________________________*






.......Baby tayiwa kofar dakin zuru da ido don taga me shigowa inda karisha da bashir suka shigo sai wata Mata Yar gayu da kwalisa na biye dasu inda kamshin ta ya cika dakin sai dai damuwar dake shimfide a fuskar ta ya kassara komai don jikinta ma asanyaye yake inda baby tabita da kallo suka zauna akan kujera tana gaishe da karisha da bashir kafin ta dubi baby ta gaisheta cikin sanyin murya inda haka Nan baby taji wani tausayin ta ya kamata duk da Bata San kowacece ba ta amsa Mata tana yi Mata sannu da zuwa yayin da ta wurgawa karisha wata matsiyaciyar harara don ta na ganin karishar ce silar kaita hotel har akayi nasarar keta Mata haddi da alfarma sai take Jin lallai ne sai ta dauki fansa akan karisha wadda ta zamo jakadiyar hada barna da fasadi


Karisha ta dubi matar Nan Yar gayu ta soma magana

"Najla dama abinda yasa aka dauko ki don ki San abinda ke faruwa bangis ne yayi hadarin mota wadda tayi ajalin shi inda motar da yayi ha tsarin ta kone da wuta kurmus ko gawar shi  ba asamu gani ba sai dai Nan aka yayyafa ruwa aka sallace shi aka bizne don haka bangis ya rigamu gidan gaskiya sai ki dauki hakuri da dangana 


Baby da taji karyar da karisha ta sharara wa wannan Mata me suna najla sai ta ida tabbatar wa Babu tsoron Allah acikin lamarin su bashir me yasa suka biyewa matar Nan gaskiyar lamari? Sai taji kamar ta fasa kwan dalilin mutuwar bangis din sai Kuma ta Gane ita zatayi wa kanta bankada tunda dai shi tashi ta Kare itace aruwa don haka sai tayi gum tana Kara tausayin najla inda taga najlar na hawaye kanta Duke tana zubar hawaye


Inda Kuma Bashir ya Dora da karatun gaba

"Kiyi hakuri najla mutuwa Bata yin hanzari sai dai mun yanke shawarar Ni Zan maye gurbin bangis akanki don in har na barki banyi Miki adalci ba saboda kin Saba da Jin Dadi bai kamata mu juya Miki baya ba  don haka sai ki zauna anan zanje gida in samu su baba da batun in yaso da kin gama takaba sai a daura Mana aure don yadda na dauki bangis to ba Zan taba Bari iyalan shi suyi kuka ko Rashi ba


Najla ta dago kanta Jin yadda ake Shirin mayar da ita matar gado Kuma ma mijin gadon irin mijin da ta Dade tana fatan Ubangiji ya nuna musu mummunar makomar su tun aduniya 

Ta dubi Bashir tace 

"Gaskiya bana muradi zanfi son ku barni inyi tunanin abinda ya dace don auren bangis yasa min tsanar aure don haka abani lokaci inyi nazari


Karisha ta tareta "in Banda abinki najla ke da Kika samu wannan tagoma shi wane nazari kuma ? Me DUNIYA ya tafi me DUNIYA ya dawo to me zai dameki? 

Najla ta dubi idon karisha

"Rayuwar ce ta fice min arai don nafi son LAHIRA ta Akan wannan duniyar da Bata da tabbas

"Da ace duniya tana da tabbas da bangis bai mutu a yanzu ba don baya kawowa ranshi mutuwa ma a Rayuwa sai gashi Yana tsaka da Jin dadin ta ta nuna mishi halin nata na Dan mangwaro don haka kuyi min afuwa ko zanyi aure gaskiya ba Zan auri irin ahalin ku ba don nasan ku na San ko suwaye ku to ladar ta Isa haka


Karisha ta kyalkyale da dariya har tana tafa hannunta

"Eh lallai najla bakin ki ya bude da yawa ko dayake Ashe fa bangis ya bar duniya

Ta dubi bashir "me DUNIYA sai fa an sake sabon aiki don wancan ya bi ruwa....

Najla ta Mike tana rataya Jakarta akafada

"Ni Zan wuce komai kenan Zan kiraku ta dubi baby 

"Madam sai anjima Bata saurari amsawar ta ba tafice

Inda karisha ke Mata dariyar keta


"Haba yariya ai ko wa yaci ladar kuturu Dole yayi mishi aski kuma duk akuyar da taci dusarmu sai mun farke cikinta mun fiddo abin mu


Bashir ya Mike Yana fadin lallai shifa son najlar yakeyi Kuma sai ya aureta da haka suka fice suna fadin maganganun da baby Bata fahimta Koko rudanin da suka gama jefata ne ya Hana Mata fahimtar su? Oho


Sai dai minti biyar da fitar najla sai gata ta dawo wurin baby

"Yar uwa don Allah kizo ki nuna min hanyar da Zan fita wallahi na rude ne na kasa gano kofar da  na shigo

Baby ta taso suka fito inda zata nuna Mata kofar fita 

Ta dubeta

"Baiwar Allah mijinki fa Babu wani hadari da yayi Ina me tabbatar Miki nice nayi ajalin mijin ki Kuma yanzu haka gawar shi tana cikin gidan Nan sun boyeta don haka kisan matakin dauka duk da dai na kula kamar kinyi murna  da mutuwar....

"Kwarai kuwa nayi murna da mutuwar bangis domin kuwa na San kin ga irin kalar su da alkiblar da suke kallo don haka kamar Baki bukatar Karin haske So Ni godewa Allah ma nake da ya fara nuna  musu lallai Yana Nan amadakata Kuma su gama tsiyar su zasu koma gareshi don haka yanzu kece abin barka  don naji tausayin ki  araina musamman da na hango wani bakin dare da ya faru kaina na Kuma San kema hakance ta faru kanki


Baby ta riko hannun ta tana hawaye"inama ace mu zauna dake ko na awa daya ne don Ina bukatar Karin haske don ni din bakuwace ban gama sanin abinda suke kullawa ba Amma ko akan batunki Zan fahimci alkiblar......

Ganin doguwar tafiyar da suke yine yasa najla tace "Wai har yanzu bamu kawo kofar ba ne? Sai kawai sukaji muryar karisha na fadin "Ai kar kubawa kanku wahala domin kuwa baku da idon ganin kofar gidan Nan idan kuwa zaku iya to ga fili ga me doki ta juya abinta tana musu dariyar keta

Inda najla ta riko hannun baby 

"Mu koma ciki Yar uwa nasan su sunfi da haka Amma mun rike igiyar Allah wadda Bata tsinkewa Kuma da sannu gaskiya zata bayyana 

Suka juyo zuwa dakin inda suka tabbatar da lallai Basu da idon ganin kofar bare ficewa acikinta......


To fa wata sabuwa inji Yan caca. Zanci gaba in Sha Allah

No comments