SAI A LAHIRA 10
*🎀SAI A LAHIRA🎀*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
*🅿️age 10*
*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*
*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*
_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE 1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_
_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
.......Suka dawo dakin baby suka zauna inda baby ke fatan su zauna tare ko don ta tambayi najla tarihin su bashir da abokan shi
Sai dai duk yadda taso su zauna tare ba a Basu wannan damar ba domin ko karisha ta zo ta tafi da najla tun daga lokacin Bata Kuma saka najla idonta ba abinda ta kawowa ranta sun kashe najla don kar ta tona asirin su don ta San komai tunda har take fadin tasan su tasan ko suwaye
Kwana biyu tanata jimamin najla da tunanin wata Kil ta tsufa LAHIRA sai taji tana Jin tausayin najla kuma agefe guda tana yi Mata barka da rabuwa wannan bakin cikin na cikin duniya da kesa bawa Jin tamkar zai hadiye zuciya iya ta shigo kawo Mata abin Karin kummallo ta aje Mata tana Shirin ficewa ta kirawota
"Iya Dan tsaya don Allah " iya ta dawo ta zauna akan kujera tana fuskantar ta
"Gani hajiya Allah yasa dai lafiya?
"Lafiya Lau iya tambayar da kikace Zaki amsa min ne nake so in tambaye ki......
Iyar ta tashi taje ta rufo kofar dakin kafin ta sauke ajiyar zuciya ta dubi baby
"Ina jinki hajiya me kike son sani?
Baby tace "iya wane sirri ne aka haneki tonawa? Wanene bashir da abokan shi? Me suke nufi da girmama abotar su?
Iya ta sake sauke ajiyar zuciya
"To kafin in Baki amsar ki kin San nace zanyi Miki wata tambaya ko? Baby ta amsa tana gyada kanta
"To ko Baki fada min ba nasan wata Kil abin duniya ya rudeki har Kika auri me gidan Nan ko? Baby ta gyada kanta hawaye na biyowa idonta kafin ta fashe da kuka inda iya ta zuba Mata ido tana kallon ta don haka sai ta tsayar da ita......
"Kinga hajiya share hawayenki kar su jiyomu don kin San bamu da lokaci kafin ki gaya min haduwar ki da Bashir in Baki amsarki
"Bashir dai da kike gani matsafi ne Wanda tsafin shi ne ya Tara mishi wannan dukiyar da kike gani haka Kuma kece mace ta bakwai da ya auro ya kawo cikin gidan Nan Kuma dukkan Matan Nan da suka shigo gidan Nan Babu wacce ta fita don duk wacce tsautsayi ya kawota to tamkar ajalinta ne ya kirawota don kina sanyo kafarki to Babu fita ko da ko mutuwa kikayi ko gawar ki ba zata fita ba
Manufar su kuwa shine sukan hallatawa abokan su Matan su saboda wata manufar su da su kadai ne suka San abin su haka Kuma nasan Kinga wani Abu Atare dasu na bawa abokai dama akanki to shima wata manuface suke da ita wadda sai Nan gaba Zaki fahimce su duk dai acikin tsafin su haka Kuma in ba su suka so ki fita daga gidan Nan ba to duk yadda Kika so fita to kofar gidan zata bacewa ganinki idan ma kin samu ficewa to Babu abinda Zaki riska face kangurmin daji me dauke da miyagun namun dawa Babu Kuma inda zakije Zasu gano ki shiyasa nace Miki Baki da mafitar da ta wuce addua Nima nasan zakice me ya kawoni har na San wannan sirrin?
"To aikatau na shigo gari nema inda Allah da ikon shi ya kaddaro min fadowa agidan Nan tun matar farko da me gidan ya auro wadda Bata boye min halin da ta samu kanta ba ga abokan Bashir tun daga tarayyar abokan Bashir akanta har zuwa abinda idonta ya gano Mata na tsafe wani yaro da aka shigo dashi gidan Nan inda daga karshe ta haihu aka karbi Dan aka tsafe inda itama daga karshe suka kasheta suka Kuma tsafe gawar ta har yau har Kuma gobe iyayenta da Yan uwanta Basu San ta mutu ba don Babu Wanda yasan inda take saboda bai Bari aka rakota ba shi ya daukota da kanshi Kinga kenan Babu Ranar da zasu fahimci hakan to in takaice Miki magana dai haka sauran Matan da ya auro suka bi bayan matar shi ta farko Kuma kowace sai ta haihu saboda tarayyar abokan shi Wanda dama haka suka shirya don dodon tsafin su idan yasha jinin jaririn da sukayi tarayya wurin samarwa zasu Kara shahar dukiyar su ta Kara habaka kema haka suke fata da buri sai ki dage da addua
Ni kuwa da dai suka Gane na San komai sai aka gargadeni da rufe sirrin gidan Nan inda akace idan na tona to abakin Raina kinji amsar tambayar ki abinda na kawowa Raina akan Matan da yake daukowa shine kwadayi da buri saboda son DUNIYA da hadamar zuciya duk da wasu daga cikin Matan da auro ba son abin duniya bane ya kaisu sai don biyayyar iyaye iyayen da sune aka yiwa yayyafi da abin duniya har idon su ya rufe su tursasa ya'ya su auren da Basu San wacce irin sana a ce ta Tara wancan dukiyar ba Amma Kuma da yawan Matan son abin duniya ne ya saka su fadawa hadari da halaka don haka Nima Ina rokon Allah da ya kawo min mafita don Ina son komawa ga iyali na yau shekaru na takwas ban San halin da ya'ya na ke ciki ba Suma na San suna can suna tunanin abinda ya boyeni koma suna zaton na mutu
Baby da ta Dora hannuwan ta biyu akanta tamkar zata kurmo ihu saboda tsabar rudani da tashin hankali sai Kuma ta sauke hannuwanta ta toshe bakinta tana Hana kukan dake son ta sakoshi ya fito
Iya ta soma rarrashin ta tana Kuma nuna Mata idan aka San sun kebe to Babu ko shakka kwanan su ya Kare
Don haka ta takawa kukan ta burki inda silar komai na haduwa da Bashir ya dawo Mata tamkar yanzu ne abin ke faruwa ta dubi iya
"Iya Bari kiji sanadin fadowata wannan halakar ta haduwa da Bashir Wanda Nima son DUNIYA da hadamar zuciya ya kawoni Nan Wanda bani da kaico zanma iya cewa alhakine ya kawoni Nan
Ta soma kwancewa tsohuwa iya jakar sirrin.......

No comments