Breaking News

SAI A LAHIRA 6


 *🎀SAI A LAHIRA🎀*


              *NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*



                *🅿️age 6*




*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






Bazan taba manta wa da haj Saliha abubkar abdllh Zaria ba saboda tayi min halacci Allah ya Kara lafiya da daukaka


......... Tamkar ta amaye zuciyar ta takeji yayin da ta kasa matsawa daga jikin mutumin Wanda ke shafa ta tamkar yadda akewa karamin yaron da ake rarrashi 

Duk yadda take Jin tsanar mutumin Bata iya zame kanta ba har sai da ya tashi ya SHIGA ban daki ya shimfidar da ita

hawaye ne kawai ke zarya akan fuskarta Bata taba jin ko ganin irin wannan Al amari dake faruwa kanta ya faru ko ga duniyar dabbobi ba don Suma kansu dabbobin suna da kishi sai gashi yau wani mutum da Ubangiji ya karrama da da baiwar mutum taka da Kuma hankali Wai shine ke Mika matar sunnar shi ga abokai tamkar haya ko ranting ga matar da ko Daren farkonta bai gani ba ita kuwa wace SHIGA UKU CE ta kaita auren bashir ? Wane tsautsayi ne ko asara? Sai dai ita da kanta tasan Bata da kaico dama ance Ramin mugunta ba a Gina shi da tsayi idan kuwa kayi me tsayi to kanka


Ayau takejin aurenta da Bashir zai bakunci kiyama don ba Yar iska bace ita da zata Kare da kwana da asararru da gantalallu 

Tana cikin zance da zuciyarta abokin kwananta ya fito daga bandaki daure da tawul Yana taje sumar shi inda yake Bata hakuri akan kukan da ya kula tanayi

Ta dago kanta da sauri ta dubeshi Jin hausar shi ma Bata fita sai kawai idonta ya sauka Kan sarkar cross dake rataye a wuyan shi inda gabanta ya yi wata muguwar faduwa

Ba sai an fada Mata kowaye ba da addinin da yake biye wato Cristian 

Wace irin kwamacala CE haka?

Lallai bashir ya yaudareta ta Kuma tabbatar ba banza suke ba akan kudin su da sunan da karisha take Kiran su wato masu DUNIYA da Kuma Jan idon su da wannan dabbancin da suke sauke shi akanta. Idan ta fahimce su  maza Sha wani Abu aka aurowa ita kenan? Ta Mike tana Jin wata muguwar nadama da Dana sani a Rayuwar ta


Kamar kullum yayo Mata oder abin breakfast me Rai da motsi cikin gwalanton hausa yake fada Mata taci abincin kar ya huce

Ba ta ko dube shi ba bare tayi nufin yin abinda yake magana akai

Tunanin ta yafi tafiya ne akan yadda ake yaudarar ta har ake keta haddin ta inda ta Gane ko shakka batayi wani siddabarun suke yi Mata Wanda ke sakata baccin Dole 

To a yau zata kawo karshen wasan da cewa kurunkus Kan Dan bera


Yana Shirin fita ta biyo bayan shi da nufin ficewa inda yaja ya tsaya Yana Bata hakuri......

Cikin karaji ta katseshi 

"Ka bude min kofa in wuce kaj"

"Kayi hakuri my oga yazo Nima gida Zan wuce please and please madam.....


Duk yadda yaso ta fahimce shi abin yaki yuwuwa Dole ya Kira wayar bashir ya fada mishi abinda ke faruwa daga karshe yace abata wayar


Ya Miko Mata wayar tabishi da kallo kamar ba zata karba ba inda Bashir din ke faman hello hello

Ta karbi wayar tana Kiran sunan bashir


"Kana jina bashir? "Ina jinki baby me ke faruwa.....


"Allah ya tsine maka Bashir , 

Ta antaka mishi ashariya

"Me yasa ka boye min ko Kai waye sai da na aureka nagane Kai din azzalumin mugu ne?

"Ina so ka bashi umarnin bude Ni in Kama gabana idan kuwa ba haka ba na rantse maka da Wanda ya halicce Ni shine Allah zanyi ajalinku ku duka tunda na Gane aikin da kuke kullawa acikin bakin duhu...


Ta cika dakin da hayaniya da hargowa Bata ma jira ya Ida maganar shi ba ta saki wayar akasa ta tarwatse ta soma baza ido adakin da son tayi ido biyu da wuka ko bindiga

Sai dai Abu ga dakin hotel Babu yawaitar tarkace  Babu wani takamaiman makami sai tangarayen da aka zubo Mata abincin na alfarma da kure adaka.

Don haka ta Suri tangaran din da abincin cikin shi sai akan goshin shi inda jini yayo sallama Yana Kiran Jesus Yana dafe goshi

Aiko baby ta haukace mishi ganin tana Shirin keta shi yasa ya bude dakin don ya kaucewa abinda ka iya riskar shi 

Fitowar shi yayi daidai da zuwan Bashir da karisha


"A a yau ba lafiya me DUNIYA Amarya ta haukace....

"Yau Zaki ga hauka cewar zainab da kalaman karisha ya Ida haukatata.

Aiko tayi ta jeho duk abinda ya tari gabanta cikin sa a kuwa ta rotse Bashir da karisha

Shi dai bashir a goshi ta sameshi da kofin gilashi ita kuwa Karisha abaki ta jehota da guntun gilashin tangaran 

Da sauri abokan bashir dake makotaka da dakin suka fito suna kallon ikon Allah


Har dai daga karshe bashir da goshi kewa yoyon jini yayi nasarar damkota ya Danna mota tana dura mishi ashar da son fitowa a motar Amma ya murza key kofofin motar suka rufe ruf

Don haka sai kawai ya hau titi daga kaduna zuwa Abuja


"Allah ya daidaita ku ya Toni asirinku Kai da shegun abokanka Ubangiji yasa kuyi sabani da ALHERI kuyi gamo da dukkan wata musiba da Bala 'i

Bashir bai tanka Mata ba yaci gaba da tukin shi jini na diga agoshin sa ganin ya ba banza ajiyar ta sai ta kar rikicewa har tana fizgar sitiyarin motar da son Kada su inda ya yi namijin kokarin dafe sitiyarin taci gaba da auna mishi ashar da nema mishi musibun DUNIYA da LAHIRA Amma bai tanka Mata ba har suka shigo garin Abuja

Tun daga kaduna har Abuja bakinta baiyi shuru ba har ya shigar da motar cikin katafaren gidan me kama da mazaunin shugaban kasa wato billa.


Ba don taso ba sai don Babu yadda zatayi yasa ta fitowa daga motar inda girman gidan ya Bata tsoro daular da aka shinfida tasata yardarwa kanta ta kawo kanta inda Babu mamaki namanta za aci ko jinin jikinta za a zuke ko Kuma kanta dungurugum za a fille musamman da ta hango wani katon mutum me katon ciki Amma kanshi kamar sisi ya durfafo su cikin wata tafiya ta kasaisata sai taji fitsari na Shirin kubce Mata a tsaye ba tare da ta shirya ba........

No comments