SAI A LAHIRA 5
*🎀SAI A LAHIRA🎀*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
*🅿️age 5*
*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*
*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*
_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE 1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_
_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
*K* arisha ta dafa kafadarta ta Dan girgizata "idon ki biyu ne Amarya don duk me kaunar ki ba zai so hakan ya zamo mafarki ba kamar yadda kike fata
"Ke kuwa idan hakan ya zamo mafarki wace asara CE ta zarta hakan asara? Baki San sai Allah Yana son ka yake hadaka da me arziki ba? "Duk macen da Kika gani fatan ta da BURIN ta tayi AUREN huce haushi da ta kaici. Baki San yanzu Kan Mata ya waye ba SHIGA suke su fita don samun maza irin masu DUNIYA ba? Aike mamar ki ta iya haihuwa tunda ta haifo macen da ta dauki hankalin masu DUNIYA. Don yanzu na tabbata maman ki dake ta dogara don ki agaza Mata da irin duniyar da Kika tsinta asama. So kar ki dumu kanki da abunda me DUNIYA yayi Miki idan sauran ma suna bukata bisu ku huta meye cikin ido Banda ruwa? Ko Ni masu DUNIYA ke muradin hutawa da ita Zan bi yarima mu Sha kida don na San dai kakata ta yanke sakarta sunana Kuma ya fita DUNIYA don nayi tarayya da masu DUNIYA.
Zainab ta dubeta da Jin wani sabon dabbanci da dulmiyewa halaka. "Ni din ba irin ki bace da ban iya banbance Haram da halak. "Ni din na taso gidan da ake gudun abun kunya da abin fada "na tashi agidan da ake kyamar Zina da dukkan wata kaba ira bare ace da aure na wani namiji ya neme Ni don dai kawai daudar DUNIYA........
"To Amma Amarya kamar duniyar tasu CE ta rudeki tun farko ko? Atake lamarin ya dawo Mata tamkar a faifan garmaho hawaye ya biyo gurbin idon ta
"Tabbas hadamar zuciya da son azurta Kai da Kuma kerewa talauci shi yayi min jagora har na samu kaina a garken zakuna da kuraye. Amma ba kowa ya cuceni ba face bashir da ya jinginar da Ni a hotel tamkar wata karuwa har ake keta haddina .......
"A a amarya Ni na rasa me kike ta tattalawa wannan ango naki Wanda da kin San yadda yake girmama shi wannan aboki da kike ta shelar yaci Amana Ina me tabbatar Miki zai iya sadaukar dake gare shi indai ya na son hakan.......
Zainab tabi karisha da wani matsiyacin kallo tana zaro idanu
"NA SHIGA UKU Ni zainab me Nike shirin ji ko gani? Karisha ta jawo ledar kayan da tazo Mata da su ta turo Mata harda kayan kwalliya dasu makilin da turare.
"Kinga Amarya kar ki tsaya Bata lokacin ki da son banbance halak da Haram don in dare yayi dare ma gyare ma nama ne.
Haram nawa ake tatawa a wannan duniyar? Ke dai Yi kokarin Tara abinda Zakiyi hannun Riga da talauci Mata da yawa na neman irin damar da Kika samu sun kasa samunta
"Gaya min aikin da zai Tara Miki wadan Nan dalolin da suka Baki a wannan Nigeriar? Gaki afuska kamar wayayya Amma Zaki zamo wata kidahuma? Ko da masu DUNIYA Basu nema ba tallata musu don ki samu duniyar
"Don haka ga Kaya Nan ki sauya ki Kuma dauko kwalliya ta tashin Sens kiga inda ake SHIGA a talauce afito a azurce. Don haka ga Kati na idan kina son wani Abu sai ki kwala min waya in garzayo don Nima yanzu Ina son inci arzikin ki wurin masu DUNIYA.
Haka tafice inda zainab ta rakata da wani kallo idon ta taf da hawaye kafin ta fashe da kuka
Kukan tausayin Kai don ta tabbatar da akwai wani mugun qulli da su bashir suke kullawa acikin bakin duhu Wanda SAI A LAHIRA ko zata fahimta ko SAI A LAHIRA Ubangiji zaiyi Sakayya
Haka ta wuni cikin laluben mafita don itama karisha da tafita sai da ta kulle ta adakin inda ta gama yarda ta fado wani hadari Wanda sai dai Allah ya fidda ita.
Sai Kuma taji zuciyar ta na tambayar ta Allah ya fiddaki? To ke kinyi abinda Allah zai fidda ki acikin wannan lamarin?
Sai Kuma ta tabbatar lallai batayi abinda Ubangiji zai kawo Mata dauki ba domin ko shi da kanshi yace ya haramta zalinci akanshi ya kuma Sanya shi haram abin haramtawa ga bayin shi
Lallai son zuciya kin zuciya
Haka ta wuni saka da warwara ta Kuma yini neman layin bashir in ma har tayi nasarar samun shi baya daga kiranta ta kuma kasa hakura taga yadda yake nufi da ita. Ba don taso ba taci abincin da ake ta turereniyar kawo Mata don kar yunwa ta kassara ta
Babu Wanda yasake shigo Mata daki har bayan Isha I inda tajiyo magan ganunsu Amma babu Wanda ya ko taba kyauren dakin bare ya shigo
Ta jawo wayar ta don ta Kira goggo Hime sai ta Tara's da cajin wayar ya sauka gashi Bata da wata cajar
Dole ta maida wayar ta aje inda a yau tayi nufin kwana zaune don tace ba zata Kuma Bari a yaudare ta ba
Sai dai akace ba acin bashin bacci in ma anci sai an biya don haka ta soma gyangyadi daga zaune in tayi kamar zata Fadi sai ta wartsake har dai Bata San lokacin da takai kasa ba.
Tamkar cikin mafarki Wanda ake son farkawa don tantance gaskiya ta ke hango lamarin sai dai taso farkawa inda tajita tamkar Yar maye Wanda bisa Dole ta hakurewa farkawa Amma fa abinda take gani ba don yanayiwa zuciyar ta Dadi ba Amma ya ta iya? SAI A LAHIRA kawai don haka tanajin komai sai dai Bata da ikon motsi bare Hana abinda ranta bai mata Dadi ba
Har gari ya waye inda taji tana iya motsawa ta bude idonta tarwai inda Kuma tayi arba da wani daga cikin abokan Bashir Wanda Kuma ba mutumin jiya bane wani ne daga abokan Bashir shima din Yana makale da ita akirjin shi
Ayau ihun ma Bata samu sararin yin shi ba inda take Jin tamkar tayi Aman zuciyar ta saboda bakin ciki
Wai ma tsaya me suke nufi da ita? Bashir su ya aurowa ita ko kuwa kanshi? Idan ma su din ya aurowa awace duniyar CE hakan ke faruwa? ???????
To mubi muga wannan ikon Allah dake faruwa tamkar awata duniya da ba mu tabajin labarin ta ba
Nidai GIDAN IKO shine sunana kecewa saduwar alkhairi
Ma assalamm

No comments