Breaking News

SAI A LAHIRA 4


 *🎀SAI A LAHIRA🎀*


              *NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*



            *🅿️age 4*




*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



*




*G* abanta yaci gaba da faduwa idon ta akan mutumin dake kwance Yana sharar bacci. Ta Yaya akayi Mata wannan yaudarar? Me hakan ke nufi ? Bata ko shakka Bashir baida masaniya akan abinda ya faru. To Wai ma ina Bashir din ya tafi da har abokin shi ya samu SHIGA dakin har ya kwana da matar da ya tabbatar da dauruwar aurenta da abokinshi? Bata San lokacin da bakin ciki ya sa ta fashewa da kuka ba.

Kukan nadama da da na sani 

Kukan bakin ciki da yadda aka keta haddin ta da auren ta Amma abokin muji ya karbe martabar da kowace mace ke tunkahon kaiwa mijinta.

Wai ina bashi ya tafi ya barta da har abokin shi ya zagayo yaci amanar shi?


Kukan ta ya farkar dashi ya dubeta sai sheka kuka take tamkar wadda aka sanarwa mutuwar iyaye.

Ya sauko Yana dubanta inda ya dire agabanta da son rarrashin ta. Hannunta yake kokarin rikowa inda tayi saurin daga mishi hannu.

"Dakata malam kar ka tabani ta fada da Amon murya.

"Don ka ganni a hotel ya baka damar keta min haddi bayan kasan an daura min aure da abokinka?  "Na rantse maka da Allah ba Zan taba yarda ba sai na bi hakki na na keta min alfarma da Aure na don kawai ka ganni hotel kaddara ta kawo ni...........

"Lallai kaddara kuwa don kaddarorin ki ai Basu fara ba ma. Bari in fada Miki abinda Baki sani ba mu da Bashir Abu guda ne mukan iya fansar da rayukan mu ga juna  ko Bashir yaji abinda mukayi ba zai damu ba So kar ki damu in don wannan da yardar shi da amicewar shi hakan ta faru Kuma ba yau kadai ya bani ba har Nan da kwanaki bakwan da ake bawa ango da Amarya fili su huta su Kuma more  don haka share kawai indai kina son DUNIYA to muna da ita Kuma in kin bimu Zaki samu DUNIYA


Kadan ya rage zuciyar ta ta faso kirji ta fito saboda Jin abinda yake fada Mata wace irin musibace ta siyo da kudinta? Me kalaman mutumin Nan suke Shirin sanar da ita? Sai dai Bata ko shakka wannan mutumin baya cikin hankalin shi tunda ita da kanta taga suna Shan wani Wanda ta tabbatar giyace haka Kuma taso jiyo wani wari Atare dashi Wanda ya Ida tabbatar Mata kalaman shi kafso ne da Marisa kawai  Bashir kawai take son gani a yanzu don ya fidda ita wannan bakin duhun

Ta dubi kanta Babu komai a tare da ita sai bargon da ta rufa anikinta inda Babu arziki ta takawa kukan ta burki ta nemi mafita.


Tamike arude ta jawo wayarta ta soma laluben lambar Bashir ta doka mishi Kira sai dai duk nacin Kiran da take mishi bai daga ko guda ba. Inda take Jin tamkar Rashin daga Kiran zai kaita kiyama

Haka tayi ta Kira ba tare da ya daga ba don ya San Allon shiyasa yaki dagawa ita Kuma Taki hakura

To Yama za ayi ta hakura? Ta hakura bakin ciki ya yi Mata jagorar zuwa LAHIRA?


Tun tana Kira ta sameshi har ta Kai ko ta Kira matar Nan me zakin muryar tsiya na sanar da ita sai dai ta sake Kira lokaci na gaba don yanzu layin baya aiki  mutumin bai kuma bi ta kanta ba ya shide ban daki ya sheko wankan shi ya fito inda yayi oder abin Kari breakfast me Rai da motsi ya dire agabanta inda take ta faman Kiran layin Bashir Wanda ake ta sanar da ita baya samuwa.

Baice Mata komai ba ya fice abinshi inda yasa key ya kalleta ta ciki ta bi kofar da ido inda ta tabbatar abin fa ya wuce yadda take daukar shi Babu ko shakka akwai kamshin gaskiya amaganar shi in ba haka ba meye na kulleta adakin? 

Ta sake fashewa da kuka yau inda siyama taga abinda ke faruwa akanta ba zatayi mata dariya ba?

Me yasa bashir ya yaudareta ya boye Mata ko shi waye?


Tana cikin zancen zucin ne taji ana bude dakin inda ta zubawa kofar dakin ido da son ganin me shigowa inda taga karisha ta shigo tana murmushi. "Yi hakuri amarya ya akaji damu masu ban haushi? Kiyi fa hakuri amarya namu ba irin nasu bane kar ki damu da duk abinda Kika gani kin San kullum ilimin Kara yawa yake.


"Dama ango ne yace in kawo Miki kayan da Zaki bukata kafin lokacin da Zaki koma gida don wata Yar tafiyace ta Kama shi yace asanar dake me yuwa ta dauke shi har sati biyu ko kwana goma idan kina bukatar wani Abu sai ki sanar Dani Zan Kuma bar Miki lambata ko da Kiran gaggawa ne sai kiyi min.

Hawaye ya tararo Mata ta dubi karisha.

"Kin ko San abinda ke faruwa? Na tabbata bashir be San wani Abu zai faruba da bai yarda ya barni ahotel ba. Nayi bakin cikin abinda akayi min.....

Karisha ta tare ta "me ke faruwa ne Amarya?


Zainab ta sanar da ita abinda ta farka ta gani Wai daya daga cikin abokan Bashir ya yi Mata Wanda sai da safiya taga abinda ya faru.

Karisha ta yi murmushi

"Kar wannan ya Dame ki amarya Ina me tabbatar Miki ko Bashir yaji Babu abinda zai faru. Don ban taba ganin abotar da ake karrama wa ba da girmama ta irin ta su bashir da masu DUNIYA.

Ke dai bisu ki samu DUNIYA ko Baki lura da yadda suke kyautar dalar amurka ba? Ina me tabbatar Miki idan Kika bi masu DUNIYA Nan sati guda sai sunanki ya zaga DUNIYA saboda kinyi bankwana da talauci kin Kuma gama Zama milloniya 

Ai haduwa dasu ma rabo ne sai Wanda Allah ya zaba to meye naki na tada HANKALIN?


 "Kin ko ji abinda na fada Miki baiwar Allah? Awace duniyar nake? Da wace irin halittar na hadu? Na Dade Ina zaton mugun mafarki nake. Ubangiji kasa abinda nikeji da gani ya zamo a cikin mafarki nake Jin su. Ubangiji kasa nayi gaggawar farkawa

Me ke shirin faruwa Dani NE???????



Lallai son zuciya baiyi ba duk da bamuji son zuciyar da yakai yarinya zainab ga wannan tarkon ba



To muje zuwa don Jin yadda ake wanyewa




Ni

Dai 

Gidan

Iko

Ne 

Sunana

Ke

Cewa

Saduwar

Alkhairi

No comments