Breaking News

SAI A LAHIRA 3

 *🎀SAI A LAHIRA🎀*



              *NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*




            *🅿️age 3*




*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_


*




*T* a dubi karisha da wani matsiyacin kallo na neman ba Asin kawota hotel a maimakon gidan su da akayi da ita. Karisha ta dubeta"yi hakuri amarya Sha guda fito muje in bada sakon......."me zanyo a cikin hotel Ni ba Yar bariki ba SHIGA hotel da aure na? Babu Dalili kije ki fito idan Kuma kinyi wurin Zama sai in fita in gano gidanmu don Babu lallai Babu Dole. Karisha tayi murmushi "haba amarya Sha guda me yayi zafi ido ke wuta gira na fidda hayaki? Daure ki fito muje ciki ku gaisa da masu DUNIYA wato abokan ango don asubanci zasuyi zuwa gida kin San ba Nan garin suke ba tafiyayya sukayo saboda su Taya ku murnar bikin AUREN ku. Daure ki fito kiyi musu sallama tunda ko ba komai ai Kinga halaccin da sukayi Miki dala dubu fa sau dubu. Kamar tace Mata na rokesu ne? Sai Kuma ta fito ta biyo bayan karisha inda tayi arba da motocin su harma da ta Bashir afake a parking space.


Tana biye da karisha inda take waya da abokan ango Wanda take Kira da masu DUNIYA dukan su hade su take tayi musu jumla wurin Fadi wato masu DUNIYA.


Kyauwun hotel din da kayatuwar ta inba masu DUNIYA ba to sai Wanda ya shirya bakowa NE zai iya rabar ta ba bare ya shigo ta in ba irin su masu DUNIYA ba. Karisha ta tambayi lambar dakin da suke suka sanar da ita Kai tsaye ta tunkari dakin me dauke da lambar tamkar ta San hotel din ko ta taba zuwa. Ko dayake ta iya yuwa ta Saba da wurin itama da dalili yayi dalili ba gashi ta tako kafar ta hotel din ba. Suka SHIGA dakin Wanda ya zamo  V I P Wanda yake hade ciki da falo falon na dauke da setin kujeru biyu masu launi kala kala inda zainab ta iske abokan Bashir su duka hada shi Bashir din zaune akan kujeru suna Shan wani Abu acikin kofin Nan gilashi Wanda Bata taba daya biyu ba akan giyace suke kwankwada shigar su ya basu damar zuba Mata jajayen idanun su abinda Kan firgitata . Karisha ta zauna kusa da Bashir har jikin su gugar juna ta Kuma nuna Mata wuri Wai ta zauna

Tayi sairin Kada kanta

"Gaskiya gida  nake son zuwa don Daya har ta wuce 

Bashir ya dubeta

"Karki damu zee in ta kama mu kwana anan sai mu kwana su malam ba zasu tuhume mu ba tunda an daura Mana igiyoyin aure 

So kar ki damu tunda ga wuri idan kinajin bacci yi kwancyar ki......

Ta wurgo mishi harara

"Don dai nice marar kunyar karshen DUNIYA daga fitowa amsa Kiran wayar ka mun taho party ba tare da sanin iyaye na Kuma sai aji na biyoka har mun kwana ? Kuma kwana a hotel sai kace wata karuwa? "Indai Babu halin maida Ni gida fada min kawai ko akafa sai in koma don ba Zan yarda asakani abakin duniya ba.


Ya yaye labulen tagar dakin inda ya nuna Mata hadarin da ya gangamo Wanda ke ta haska walkiya 

"Dubi hadari fa zee Wanda har ya soma zubar ruwa Bari in Kira malam kawai don in sanar dashi don kar in sakaki abakin duniya nasan abinda kike yiwa 

Kafin ta ce wani Abu har ya Kira layin malam din ya sanar dashi Wai harari ya Hana su dawo don haka ayi mishi afuwa ya wuce da zainab din gidan shi. Malam yayi Jim Amma kunya da nauyi ya Hana ya nuna mishi Rashin dacewar hakan sai Kuma ya ga  ba Haram bane sai dai an keta Al Ada  don  sabon salo ne Wai kaza da AUREN muzuru. Dole malam din ya amsa da Babu komai ba Haram bane da haka sukayi sallama da malam din ya dubeta

"To hankali ya kwanta malam ya San inda kike my baby ya fada Yana kamo hannunta zuwa daki  Inda taji hawaye na bin idonta Wai itace da kwana hotel  amatsayin ta na amarya amaryar da akasar hausa da akeyiwa rakiya yau ita nata mijin ya dauko ta  ya kawo hotel wananna bakin tarihi Dole ayi ta yada shi akanta Kuma ba kowa yaja Mata ba sai son zuciya da hadamar zuciya inda kanwar ta siyama ta fado Mata arai Babu rabon siyama taga wannan bakin tarihin to yau kuwa wace Rana cin Amana tayi Mata? Cin amanar ma na Yar uwarta jininta me son ta da zuciya Daya. Bata Ankara ba taji Bashir na  yi Mata salon da yasa ta janye jikinta


Don yanzu ya gama fice Mata arai mafita kawai take nema akan rabuwa da AUREN shi don ta kula da matsala a Zama da Bashir

Sai dai yadda Bashir din yake Mata duk yadda taso bijirewa bai Bata dama ba Dole tabada Kai Amma tayi mamakin yadda Bashir ya zamo akan muguwar dabiar da ya nuna Mata ayau akan abokan shi.

Bata firgita ba sai da gari ya waye inda taga mutumin da ta kwana dashi amatsayin mijin aurenta

Ta Mike afirgice ganin mutumin da take manne a kirjinshi

Daya ne daga cikin abokan Bashir Wanda ya halarci bikin auren su

Ta Dora hannuwan ta duka biyun akan ta tamkar me shirn kwarma ihu tamkar donta Kan mutumin da ta kula Yana yawan zuba Mata idanu Yana ta sharar bacci abinshi wace irin SHIGA UKU CE ta sameta haka......




Wace irn kwamacala CE haka?🤔



Muje zuwa gidan iko

No comments