SAI A LAHIRA 14
*🎀SAI A LAHIRA🎀*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
*🅿️age 14*
*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*
*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*
_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE 1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_
_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_
*_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
WAYE BILYA BARDA❓
.........Alh bilya barda haifaffen garin katsina ne family din su masu kudi ne da kirki da mutunci sai dai bilya barda yafita zakka acikin wancan family din nasu domin kuwa mutum ne marar mutunci baya Jin wahalar girba Rashin mutunci musamman da yasan Yana da kudi shiyasa yake ganin tunda Yana da kudi to Yana da damar yin abinda yake so Kuma yaga dama.
Mutum ne dake fadin shi bai dauki mace abakin komai ba face Riga wadda zai sauyata aduk sadda yaso hakan don yanaga Yana da kudi sai ya soma sauya Mata kamar yadda ake sauya Riga laifi kadan matar zatayi zaice jeki gidan ku na sake ki saki uku
Mata Daya bayan Daya sai da auro Tara Kuma yasake su a yanzu haka babu mace agidan shi sai fa yanzu da idon shi ya hasko mishi nafisatu da yake son kawota amatsayin mace ta goma dake Shirin shigowa duk da Bata boye mishi ba Amma yace sai yaga abinda ya turewa buzu nadinshi
Babbar matsalar Alh bilya barda itace duk yadda yake son nace to da tayi ciki zaiji ya gama da ita inda aka kasa gano shi shin haihuwarce baya so Koko kyamar Mata masu ciki? Duk da da yawan Matan da yasaki wasu ma Basu Kai ga yin ciki ba yake sallamar su da saki kwarara har uku rigis don anuna Miki ke din ba wata tsiya bace duk da fadin bai dauki mace abakin komai ba face Riga wadda zai sauya aduk lokacin da yaso hakan
Sai dai magana ta zahiri Abu biyu ya hada baya son haihuwar gaba daya don Yana ganin haihuwa ita ke kashe Mata aganin shi kenan shiyasa da ya lura kina da ciki zai yi maza ya rubuta Miki Jan katin gama Zama gidan shi.
Sai dai wasu Matan Basu Kai ga takao wancan bakin matsayin ba suke rabuwa
Ance matar shi ta farko saboda ta kawo mishi abinci ta manta Bata sako cokali ba ya hau sababi batare da ya saurari uzurinta ba ya ce taje ya saketa saki uku
Ita kuwa matar shi ta biyu yau da gobe ce wadda take Kan kowa ko Kuma ace Ranar kuskure ba daidai wata Rana gishiri ya kwace Mata amiya kasancewar tana Azumi Bata lasa ba ta Kai mishi abincin yaji gishiri yayi yawa Nan ma ya hau sababi karshe itama ya Bata Jan katin
Mata ta hudu kuwa itace ta fara haduwa da laulayin ciki tunda ya kula da cikin nata ya soma nuna Mata bakin hali
Ya fara da cewa kyankyaminta yake saboda yawan amai karshe sai ya nuna Mata ko Asibiti ba zai kaita ba daga karshe dai itama yabata saki uku haka dai sabani kadan ke saka shi sakin Mata inda matar shi ta karshe wato ta Tara ita Kuma Rashin mutuncin da ya shuka mata ya zarce na sauran Matan
Dalili kawai da an Aiko mata mahaifiyarta Babu lafiya har ta Kai sai an kwantar sai an tayar har dai suka dire a Asibiti inda ta nemi izinin zuwa dubo mahaifiyarta ya ce bai yarda taje ba
Duk yadda taso zuwa ganin mahaifiyar tata Amma ta hakura sabods mijin nata bai yarda ba
Sai dai yadda mamar tata ke ta ambato sunanta da son tazo su gana yasa aka hadasu ta waya inda mamar ke ce Mata ta daure tazo suyi sallamar bankwana don ciwon ta ba na tashi bane haka ta Kira mijinta bilya barda ta sake rokon arziki tana kuka Amma yace bai amince ba inda Kuma Yan uwanta suka soma ganin wautarta na Rashin zuwa amsa Kiran mamarsu dake ta kulafucin son ganinta don haka sai kawai ta zari hijabinta ta fice zuwa Asibiti inda ta samu mahaifiyar ta na Shirin ban kwana da duniya akan idonta akuma kan cinyarta mahaifiyar tata ta cika inda barda ya shigo cikin Asibitin ya samesu suna kuka saboda yaje gida ya iske Bata Nan wannan shine laifin da ya rattaba Mata saki uku sai fa yanzu da ya hango nafisatu yake son maye gurbi da ita
Don haka Yana gama shiryawa ya fito Kai tsaye ya nufi gidan su nafisatu don ya siyo kaunarta da soyayyar ta da duk kudin da yake Jin ya mallaka.......

No comments