Breaking News

SAI A LAHIRA 12

 


*🎀SAI A LAHIRA🎀*


              *NA*


*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*



               *🅿️age 12*

  1. *_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*



*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu'ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*



_ga hanyar da za'a bi Dan siyan book dina HAWAYE  1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 08035191669 Sai najiku masoya na hakika_



_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_



 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*





........Azumi ta baje kudin da nafisatu ta kawo Mata na cinikin Koko tana ta lissafawa inda take ta kasafin abubuwan da zatayi dasu.

Nafisatu ta dubeta

"Amma gaskiya Azumi ki biya dala kudinta kar tazo kuyi Babu Dadi ", Kinga fa yau kusan sati biyar ko shida da yin alkawarin ku na San ko ba kyalewa zatayi ba in har ta waiwayi kudinta, Azumi ta wurgo Mata harara

"Yo in Bata kyale ba sai ayi Yaya zata hadiye Ni ne? Bashi ai hanji ne Yana cikin kowa Kuma ko kotu akaje sai dai lamuni babu Wanda ake daurewa saboda bashi sai dai ayi maka lamuni don haka ba Zan biya kudin ba sai na Kara juyawa ba Yan sanda ba  in tashi tahowa ta taho min da barikin sojoji uban waye Babu bashi cikin shi? Ita idan kikaji bashin dake cikin ta ba sai kinyi mamaki ba. Nafisatu tace

"Kar kice haka Azumi kowa yace tukunyar wani ba zata tafasa ba to tashi ko dumi ba zata dauka ba haka Kuma kowa da karatun bakin shi yake salla ki dai biya ta kudinta idan ma duka duniyar ake binta bashin su Kare kalau ita da me binta.....

Ta katseta ta hanyar jeho Mata takalmi...

"Tashi ki bar wurin Nan ko in mazgeki munafuka me ruwan sufaye"

"Idan kikace wannan sanyin halin Zakiyi irin na ubanki wahala Zakiyi wallahi. Nafisatu ta tashi ta barta tana sababin da ya zame Mata jiki

Shigar nafisatu daki tajiyo sallamar dala


"Ina kike Yar duniya kin yaudare Ni kin karbe min hatsi shine da yake almunafunfun ce ke sai Kika sauya sheka wurin malam kallah to gani na iso sai asan yadda Za ayi Dani ko Kuma yanzu haura sama.


Azumi tayi maza ta tura kudin da ta baje karkashin kafafunta ta Mike kafar Kan kudin  tana washe Baki

"Haba uwar dakina dala Sha ruwan sanyi abin baiyi zafi haka ba.....

"Yafi wuta zafi Azumi don na rantse Miki a yau ba Zan bar gidan Nan ba sai kin biya Ni kudina kije ku karata da malam kallah in ba a kwado da yaro sai abashi gayan shi.


Nafisatu ta fito tana raba musu kallo tsakanin Azumi da dala

Azumi ta soma sharawa dala karya Wai kasuwar ce kwana biyu ta kwanta Kuma kullum sai anyo Mata kwantan Koko shiyasa Bata samu zarafin kawo Mata kudinta ba.....


"Nafa fada Miki ba Zaki yaudare Ni ba wallahi sai kin biyani kudina ko ki bani hatsina.....


"Kai dala kedai Baki Jin rarrashi wallahi ko mutuwa taje gidan da Babu ba hakuri take ba? " To Ni dai yanzu ba bu kudi wurina ban Kuma San Ranar da Zan same su ba tunda Baki Jin rarrashi......

"Au to haka ma zakice min? 

"To ya kike so ince Miki dala ? 


Dala ta Mike afusace

"Ai tunda kikace haka kin tattagowa kanki aiki Wallahi da ba ayi Rashin mutunci ba wallahi yanzu za ayi shi.


Azumi ta kyalkyale da dariya 

"To in Banda abinki dala rigima na Hana gari ya waye ne"?, Na fada na Kara fada ba kudi ba Kuma magana me Dadi dala kin Dade Baki yi abinda Zakiyi ba.....


"To shikenan tunda ba kudi ba magana me Dadi zakije inda Zakiyi magana me Dadi Kuma ki SHIGA ki fita ki samo kudin ko don Dole

Dala ta fice afusace inda Azumi ke kyalkyala Mata dariya 

Inda nafisatu ke rokota don Allah da Annabin shi ta biya Azumi kudinta ta Ina hakkin wani ke Zama na wani? 

Azumi ta nunota da yatsa 

"Ke rufa min Baki kinji ko Ni zuciya ta tsaye take da kowa ma Zan buga   ba Kuma Zan tsaya araina Ni ba


"Amma Azumi duk inda akaje fa kece Baki da gaskiya har kike fada Mata Wai rigima Bata Hana gari ya waye to amma kuwa garin zai waye wa mutum a Asibiti ko caji ofis


Mtsss Azumi taja tsaki

"In kinji haushi biya min uwar gulma ai kina da kudi.....


Daga can kofar shigowa aka doka sallama inda nafisatu ta dubi Azumi 

"Dala ce ta dauko Yan sanda",

Mtsss "sai menene don ta dauko min Dan sanda ? Suna daukar Raine? 

Ta Figo mayafi tafice inda nafisatu ta bi bayanta

Ilai kuwa Dan sanda ne tare da dala


"Waye ke sallama? Cewar Azumi

Dala tace

"Wanda Zaki fadawa magana me Dadi ne Kuma ki fito da hakkin mutane tunda Ni kin Raina Ni har kina fadin ba kudi ba Kuma magana me Dadi to ayau sai kin kwana bayan kanta akan kudina

Azumi ta dubeta awatse

"Nawa ne Wai kudin naki da kike cika min gida da kwarmato? 

"Dubu biyar da dari takwas...


"To kije Nan da sati shida ko bakwai kizo ki karbi kudin ki....

Dan sandan ya katseta dacewa lallai ta fito suje station ta bada bayani in yaso sai su daidaita acan

Azumi ta dubeshi

"To in Banda abinka Kai ranka ya Dade ka taba ganin matar aure ta fita ba da izinin mijinta ba? To Ni zaman aure nake ba irin ta bace dake zaman kanta Ni Kam Ina da mijina Babu Kuma me sani fita ba da izinin shi ba ita dai da yake Bata da miji tana da damar yin galantoyin ta yadda take so ni Kam alhamdulillah Ina cikin inuwar aure  idan Kuma mutum ya shigo gidana ince yayi wani Abu.

Kuma ko can din mukaje ai maganar guda dayace Babu kudi babu magana me Dadi shi Kuma bashi hanji ne Yana cikin kowa ba a Kuma daure mutum ayau Wai don ana binshi bashi sai dai lamuni to kuje Nan da sati shida ko bakwai Kai kazo ka karbar Mata kudinta Ni Zan koma ciki don tsayuwar Nan ma danayi daku cikin haramun ne sai anjima


Haka kuwa Azumi ta juya ta barsu sake da Baki inda nafisatu ke jinjinawa mahaifiyarta akan karfin halinta lallai Bata gama sanin Azumi ba Amma sai ta cewa dala ta jira ta kawo Mata ko rabin kudin ta ne inyaso zata cika Mata sauran daga baya


Haka kuwa akayi nafisatu ce ta biya dala kudinta don ita Kam ta San gaskiya


Kwana biyu da yin hakan sai ga yayanta Khalil shida mujahid sunzo daga kaduna

Ta tare su da murna inda mujahid ke Mata kallon Ashe kin girma

Kunya ta kamata saboda kallon

Abin arziki me yawa baba shitu ya Basu su kawowa Dan uwan shi lamis kayan abinci masu yawa har da Yan suturu da kudi dubu goma itama Azumi an Bata dubu biyar


Mujahid bai boyewa nafisatu ba akan shifa yagani yanaso har ya nemi yarda da amincewar ta sai dai har ga Allah mutum daya ne aranta wato sadik shi kadai take so to Amma tana Jin kunyar mujahid don haka tace ya Bata lokaci tayi shawara don haka sai ya sanar da babansu lamis shi dai Yana son nafisatu malam lamis yayi murna sosai don su biyu iyayen su suka haifa daga shi sai Dan uwanshi shitu don haka yake ga hada nafisatu da mujahid aure tamkar Kara donkon zumunci ne don haka yacewa mujahid ya bashi nafisatu ya gama da ikon Allah bashi da Mata sai nafisatu


Da wannan farin cikin suka koma kaduna inda lamis ke sanar da Azumi hadin da yayi na auren nafisatu da mujahid

Aiko tayi tsalle ta dire tace 

"Wai wane mujahid kake magana?

"Ba dai na wurin himen shitu ba?

"Allah ya sauwake Ni Kam wallahi ba Zan taba hada iri da Hime ba mace sai son iyawa shima shitun ba ta mallake shi ba sai abinda tace akeyi ba. To nafisatu ba zata aure shi ba ya nemi wata nafisatun agaba wannan dai albarka ban siyar ba....

No comments