Breaking News

HAYATUL MAHAYAT 9-10

 


🌸 *HAYATUL MAHAYAT* 🌸

         🦚🦚🦚🦚

               🦚🦚

                 🦚

_Story and written_

            ```By```

*NPEEDY A AJI* 


_Dedicated to_

*My yar amana*



```My Novels 

1-NAYI RAYUWA DAKE

2-SANADIN ACCIDENT

    2019

3-SAKAYYAR CUTA 

4-RUFAFFIYAR ZUCIYA

5-FURUCI MURDADDIYAR SOYAYYA

 HAYATUL MAHAYAT

         typing......✍🏻```


 *_____________________________________*


 *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*

*🇦SSOCIATION🤝🏻*

 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*




🅿 9 & 10 



Kuka sosai Azima keyi wato 'kanwar Aliyu wata irin harara  ummi tayimata  tace 


" tashi kibani guri shasha sha kawai " dede nan Aliyu yashigo fuskar shi tamke kallon Ummi yayi yace 


" Ummi ni dakaina zankai Zarah har gida nakuma jaddadama iyayen ta banida ala'ka dacikin  jikin ta " jinjina kai Ummi tayi tace 


" ay tarezamu  dan karma surena maka hankali bari nashi gurin mahaifinka nasanar dashi abinda kefaruwa zuwa lokacin shegiyar tafarka daga suman munafurcin  datayi  "


Kai tsaye Azima 'bangaran Zahra tanufa cikin sauri tad'ibi ruwa tafara shafa mata zuwacan Zahra tasauke wata'irin ajiyar zuciya kallon Azima tayi tafashe dakuka  hannu tasa tadafe setin zuciyar ta datakejin kamar zatafasa 'kirjinta tafito lallashin ta Azima tashigayi amma takasa dena kukan shigowar Aliyu yasa Azima saurin mi'kewa juyawa tayi tafita asukwane dan tasan halin shi tsaf zai'iya maketa 


Zama yayi bakin bed d'in yajawota jikin shi da'karfi yace 


" yau zanmayar dake gidanku amatsayin mazinaciya kuma mai d'auke dacikin shege se yanzu na'kara tabbatar dahaka  ashe  gadan gidankuce munsamu labarin fayd'an da yayan ki yayima matar d'an uwanshi tur wannan wace irin lalacewace ? gaskiya mahaifinki baidace da sarautar HAYAT ba cikin mulkin shi se fasad'i aketa aykatawa ga kisan kai wamayasa koshi  ......... "


Wani irin mari Zarah tasauke mishi afusace tanunashi dayatsa tace 


" Aliyu kashiga hankalin ka duk abinda zakayimin iya nikad'ai tozan iya sanyewa amma banda cinzarafin iyayena kamar yadda bakasona  hakanima banasonka  wallahi har cikin zuciya ta nayarda da aurankane sabida bin umarnin iyayena amma bacin haka bazan ta'ba iya auran dukwanda yafito dagacikin wannan ba'kar masarutar ba  nagode ma Allah dakace wannan cikin banakabane zanfijin dad'i idan akakirashi marar uba akan ace jikan masarutar Yazeed ne Aliyu ........ "


Hannu yad'aga zekifamata mari tayi saurin ri'kewa girgiza mishi kai tayi tace 


" karka kuskura kuma karka soma daga yau hannun bazai sake zuwa jikinaba dasunan duka ko akasin haka idan kuma kayi kuskuran haka to babu shakka zansanar da yaya Muzaffar ko Muzanbil kasan bazakaji dad'i ba gara yaya Mu'azzam akansu kasan haka "


Tashi Aliyu yayi tsaye cikin borin kunya dankam tabbas yanajin shakkarsu wani irin kallon uwala'kanci yayi mata yace 


" ni Aliyu nasakeki Zahra saki 1 sannan kisani nanda 2 weeks zanyi saban aure dawacce nikeso yarinya mai aji wadda tacika mace maza ki d'auki duk wani abunda kikasan nakine kibar gidannan  "


Wani irin murmushin jindad'i Zarah tayi tace 


" Alhamdulilah yau zankasance cikin matu'kar farin ciki kaya kuma bazan d'auki koda tsinkeba dukda sunkasance mallakina amma sun haramta aguna sabida sun shigo cikin ba'kar masarauta "


Hijab d'inta kawai tasaka se takalmi se wayarta  data d'auka da key d'in motar da mahaifin ta yasiyamata ranar auran ta tagabanshi  tabi tawuce amma yakasacewa  komi sabida matu'kar mamaki dan baiyi tunanin Zarah zata'iya tsayuwa  agabanshi tayimai wannan munanan maganganun ba 


Zarah tana fita kai tsaye motar ta tashiga tafigeta  aguje Aliyu yana fitowa Ummi tatareshi tace 


" yaya naga tatafi  ita kad'ai ? " kauda kanshi yayi gefe d'aya yace 


" nasaketa gaskiya bazan iya shiga cikin masarutar suba nayi rashin mutunci dan wallahi nasan wa'innan mugayen yayyun nata sesun kusa 'karyani kuma kinga duk abinda sukayimin banida hujja nine naje inda suke kawai kisa maimartaba yaje yayi duk abinda yadace nide nasaketa saki 1 kuma banida ala'ka da cikin jikinta sannan Ummi maganar aurena inason yadawo nanda 2 Weeks "


yana gama fad'i haka yayi gaba kallo Ummi tabishi dashi sannan tajuya part d'in Sarki Yazeed tanufa 


Muzaffar yana sauka daga jirgi  motoci 5 ne sukazo tarbar shi dama akwai wani ayki da'aka turashi anan 'kasar Pakistan natsawon 6 months dayaso neman hanyar dazai'ki zuwa sabida damuwar dayake ciki amma wannan abin yanafaruwa hankalin shi yakarkata zuwacan bud'emai  mota akayi yashiga zama yayi cikin motar yad'aura goshin shi saman kujerar gaba yanajin wani irin rad'ad'in bulalun suna shigarshi cikin zuciyar shi yace 


" Ni Muzaffar nine mace tayima wannan mugun sharrin lalle badan d'an uwanaba da mahaifina wallahi dasena halakata nida 'kasar Bihar babu rana kuma babu lokaci


Wani 'kayatatcen gida akanufa dashi wato masaukin shi yana shiga yazauna kan cushion a parlour zuciyar shi duk babu dad'i sawa yayi aka kiramai doctor ya dubashi yabashi magani  tunda yatafi bai bud'e wayar shi ba se yau tsayin 1 weeks kenan  nan yaita ganin text d'in mahaifiyar shi da maimartaba da 'yan uwanshi  babu text d'in daya bud'e sena mahaifiyar shi  tambayar inda yashiga takeyi da halin dayake ciki amsa kawai yabata agajarce 


" ina lafiya nakoma Pakistan anan zanciga dazama bazan dawo garekuba  Momy nayi matu'kar mamaki dakuka yarda zan'iya aykata haka Momy wallahi banyima Arfat komiba kuma zmbanje daniyar aykata komiba shi Mu'azzam d'in yace inje akan naduba part d'in shi sabida Arfat tacemai tanajin motsi cikin part d'in shine ina zuwa tacemin a cikin bedroom d'in tane ina shiga tarufe 'kofar take sanar dani wai ni takeso tun farko ba Mu'azzam ba Momy kuyi bincike akan wannan abin nasanar dakene badan inajin shakka ko tsoran waniba a'a sedan kisan gaskiya tayadda zuciyar ki zatasamu  natsuwa "


Tura text d'in yayi yatsurama wayar tashi ido tashi yayi yafita yabar wayar anan 


Cikin tashin hankali Momy take karanta  text d'in Muzaffar mi'kama yaya Ahmed wayar tayi shima yakaranta bama yaya Abubakar yayi shima yakaranta cikin damuwa Momy tace Abubakar jeka kiramin Mu'azzam tashi yayi yafita babu jimawa dafitar yaya Abubakar Zarah tashigo cikin kuka tafad'a jikin Momy 


Hankali tashe Momy tashiga tambayar ta amma takasacewa komi tsa yaya Ahmad yadaka mata yace " idan bazaki sanar damu damuwar kiba tokiyi gaggawar rufe mana baki kibarmu muji da damuwar mu shiru Zahra tayi tare Abubakar yashigo shida Mu'azzam da Muzanbil basu text d'in Muzaffar akayi suka karanta bayan sun gama yaya Ahmad yace 


" kai Mu'azzam hakane ? abinda Muzaffar yace "


Jinjina kai Mu'azzam yayi yasake bayyana musu duk yadda abin yakasance sannan yad'aura dacewa 


"  Momy nifadama inada shakka akan wannan lamarin nasan Muzaffar bazai aykata hakanba idan kuma ya aykata to babu shakka ba'a cikin hankalin shi yakeba amma kuyimin ha'kuri zuwa nanda safiya zan tabbatar da gaskiyar lamarin "


Rai 'bace yaya Abubakar yace " tayaya zaka tabbatar da gaskiya wadda baka tabbatar da'itaba tun lokacin da'abin yafaru se yanzu da abin yabaiyana cikin masarauta "


Ajiyar zuciya Mu'azzam yasauke yace " eh tahanya d'ayace zan tabbatar wadda bazan iya bintaba alokacin sabida ina cikin tashin hankali matu'ka  tunda na auri Arfat banta'ba kusantar taba sabida ina ganin kamar hankalin ta ba akaina yakeba ta wannan hanyar zan tabbatar da gaskiya  kuma inada tabbacin Arfat bata bibiyar maza "


Shiru kowa yayi sabida mamaki amma banda Muzanbil danshi baiyi mamakiba  sabida shima hakan take cikin fad'a Momy tace 


" lalle Mu'azzam har kake iya fad'in wannan maganar agabana to idanma Arfat tayi haka batadalefi kaine mai laifin sabida kakasa sauke mata ha'kkin ta tokam yanzu sede kabari mahaifin ku yatambayi malamai aji yaya makomar auranku 'yanzu  "


Cikin sanyin rai Momy tace 


" auta daure kisanar damu damuwar ki tunda akayi auran ki bakizo gidannan ba se yau amma gashi naganki cikin tashin hankali  "


Kukan da Zahra take ri'kewa yakufce mata cikin kukan tasanar dasu komi  mi'kewa Muzanbil yayi zaifita azuciye yaya Ahmad yayi saurin ri'ko hannun shi yace 


" karkayi yunkurin komi se abinda maimartaba yace banason kowa yaji wannan lamarin "


Kwantar da kanta Momy tayi kan cushion tamakasa yin tunanin komi  


Koda sarki yaji wannan lamarin na Zarah tashi yayi tsaye yafara kai komo  cikin tashin hankali yace 


" wai maiyake  faruwane ? cikin masarutata daga wannan se wannan wallahi Aliyu 'karya yakeyi Zarah bazata ta'ba aykata zinaba in sha Allah se yayi nadamar dababu amfani akula dacikin jikin  Zarah kar'abari wani abu yasamaishi shine zai zama silar saka Aliyu cikin matu'kar nadama "


Cikin mamaki wani mutun ke kallon Rayhana tana siyar da kayan lambu Cikin rumfa kallon yaran dake gabanta yayi nufar katin dake bayanta yayi sallama yayima mutumin  bayan sun gaisa  yace 


" dan Allah bawan Allah wannan yarinyar kuma daga ina ? kashi hadda yara gata 'karamar yarinya "


Cikin had'a fuska mutumin  yace 


" kaga karufamin asiri wannan dakake gani narasa gane itad'in wane jinsice yau satin ta 6 anan gurin ranar danaganta anan nayi mamaki sabida se bayan magrip nabar shago har zuwa lokacin babu alamar mutun agurin amma washe gari danazo sena ganta kaga wannan rumfar datake ciki  to sati d'aya baza'a iya gamayin taba amma naganta a kwana d'aya danaje nayi mata magana akan tatashi to ranar ko sisi banyiba hakama washegari 


Danasake fitowa banyi mata magana ba segashi  nayita ciniki kaga wancan mai kantin shi harda  yun'kurin  marinta kafin hannun yakaiga  jikinta yama'kale haka yad'inga ihu seda yayi kwana 3 yana ro'konta sannan tashafa hannun yasa'be kuma kaga wannan kayan datake sedawa tunda nike nan banta'ba ganin wani yazo siyaba sabida kaf kasuwar nan tsoran ta akeji koda maganar arziki kayi mata to ranar haka zakatashi babu cinikin ko sisi amma ahaka sekaga tasiyar dakomi tana 'kirga kud'ad'anta "


Ajiyar zuciya mutumin yasauke yace 


" nagode ma Allah dayasa banyi mata magana ba "



Kuyi ha'kuri banajin dad'i ne sosai kuma bazan samu yimuku typing ba gobe sabida ina wani uziri 


Daga Al'kalamin.........✍🏻

No comments