Breaking News

MATAN HAFIZ 21

21.

...Rai bace Hafiz ya furta "dakata naji komi daga bakinki doctor blessing basai kin cemun wani abu ba, yana gama furta hakan ya zaro wayarsa yana lallatsawa, sosai Dr blessing ta qara tsurewa dan tabbas ranta ya bata mahaifin sa zai kira, bata Ankara ba ko taji hawaye na biyo mata itako ta shiga ukku da

wnn aikin take ciyarda kanta da yaranta ta fantama iyason ranta tayi qaryarta ynz idan aka rabata dashi ai karyarta ta qare mutane dariya zasuyi mata musamman wanda takewa kallon hadarin kaji.

Sukuwa su ammi suncika da mamakin abinda ke faruwa wajen, tambayoyi cikeda cikinsu fall, shin wnn sojan mike hadinsu da Dr blessing haka har take durqushin bashi haquri dudda rashin kirkin nata?

(dan kwata 2 basuyi tunanin shi d'an mai asibitin bane) 

kuma ga alamu shi ba likita bane to ya akayi ne?''

tambayar dake cigaba da kewaye kwakwalunsu knn amman babu damar yi. 

dan shi kuwa abbu a  lkcn ma yaji kamar an tsokano masa ciwon nasa, shi kadai yasan yanda yakeji don sama sama kawai yakejin mike faruwa yayinda basmah har lokacin batabar sharar kwalla ba hannunta cikin na abbun ta.


"Hello bro kana inane? OK to please ina hospital din ku shigo please kaida bro nuran, OK ina sauraranku ynx"

 

Katse wayar yai, ya medo dubansa ga Dr blessing fuska  babau annuri ya furta da yarenta

"nawane kud'in aikin nasu"


da sauri ta sadda kanta qasa tana in ina tama kasa mgn, biyoni, abinda yace knn yajuya ya har zai fita saikuma yadawo gabnsu ammi fuska a dan sake dudda har lokacin ransa babu dadi ya ce "kuyi haquri dan Allah ba aladar asibitin nan bane wulaqanta mutane mai asibitin ma bai laminci haknba, kunsan mutane akwai d'alihan akwai salihan ako inane ammn kuyi haquri kada ku tafi ina zuwa, kamin ammi tace wani yayi saurin ficewa itama Dr blessing tabi bayansa jiki babu kwari.

basma ta dauke idanunta akansa gamida ajiyesu kan na amminta bayan ta share kwallan shigewa tai jikin ammi tana sakin wani sabon kukan qasa qasa.


**

fateema kuwa koda ta shiga wajen heema Sam bata nuna mata wani mugun hali ba saima rarrashinta take da bata haquri kan rashin da sukayi na asaran beby, har take bata qarfin gwiwan kada tadamu dan mijin nasu ai gwarzo ne zasu samu wani babyn soon kada ta damu.

a zuciyarta kuwa cewa take munafuka keda haihuwa a gidan Hafiz saidai kuga anayi keda dayar munafukar zee, wlh mutuwar kasko zamuyi gaba daynmu ynda ban haihuba kuma kunyi kadan, fatana dai kidai sha tea din nan  komi zaimin dai-dai ne.

cikin kissa ta daukowa heema kakkauran tea din nan data hado mata Wanda pills din datasaka a ciki sun jima da gama narkewa, 

wani munafikin murmushi ta saki gamida gyad'a kai ta cije lips , ahaka ta juyo ta dawo ta zauna kan gefen bed din da heema ke akai tace "sannu heema amshi tea din nan kisha nasan zakiji dadi 'yan hanjinki zasu warware dan nasan baki sawa cikinki komiba, kuma abinci ki  da kikafi so ma shi nayo miki kici ko kyaji karfin jikinki dan zama da ciwo ga yunwa mu likitoci munsan ba qaramin illa yake sake haifarwa patients ba" 


jiki babu kwari heema ta amshi cup din tareda qaqaro murmushi dudda bata buqatar tea din amman ta furta 

"ngd da kulawanki gareni fateema..., katseta fateema tai a d'an murnushe ta furta " shihh,,,, kisha tea din dai ai babu gdy a tsakaninmu sbd na fahimci ke mutuniyar kirkice heema fiyeda zee kuma insha Allah zaki sameni da koyi dake a kyawawn halayenki musamman na haquri da kauda kai, bazan qara biyewa zee ba zanso mu had'a kanmu mu ukun nan a matsayinmu na *matan Hafiz,* fad'a ya qare a tsakaninmu insha Allah oga Hafiz yagama kukan rashin jin dad'in mu'amalanmu da juna a gidansa saidai san barka inda ynz tafiyarmu tazama d'aya daku" taqarashe mgnr a sigar wani rainin wayau.

 heema ko ta aminta da gaske fateema take mgnrta har zucci, sai murmushi ta keyi taji kaso cikin 100 na damuwar 6arin datai kashi 60 sun tafi, 


fateeam ganin kamar heema na jinkirin shan tea din gashi batason wani ya shigo ya rosa mata tsari ga kuma hafiz tabarosa waje tadauro ya shigo ynz musammn ma data lura kmr heema bata buqatar shayin abincin take buqata gashi kuma iya tea din ta saka maganin kuma tasan Hafiz na shigowa inya fahimci tafi buqatar abincin to tabbas shi zata ci, danshi bai lamunci takurawa wani ba a rayuwa kan ra'ayinsa da sauransu,dan haka fateeam  amsar cup din tayi daga hannun heema a yaudare ta nufi bakin heeman dashi tana furta


"please sha kinji sis...






*By 4 writers👩‍👩‍👧‍👧😍*

No comments