Breaking News

FURUCI 21-22

  21 to 22

Tsayawa tayi tana nazarin lamarin amma cikin matu'kar tsoro take tsayin lokaci tana tsaye tana karanto addu'a sannan tashiga ciki darajar addu'a yasa Iftahal taji zuciyar ta tadake sosai Kai tsaye tanufi toilet tayo alwala tafito salla tatada kafin Kiran sallar asuba sosai Iftahal takeyin addu'a akan wannan lamarin Allah yayi mata jagora 


Egypt 


Bayan dawowar Sarki Zaid da Sarauniya Batol mama takira Sarki Zaid Babu jira ya amsa kiran Mahaifiyar tashi yana shiga parlour ya taradda hjy Himla da d'anta Abdul  bayan yazauna yagaida mama sukuma suka gaidashi ygara zama mama tayi tace " Zaid abinda yasa nakiraka bawani abu bane maganace akan Abdul yana son auran  Bahijjat kuma ni nayarda da wannan auran sosai Sarki Zaid yaji babu dad'i sabida dan Kam yasan halin Abdul bayaji tako Ina gaskiya bayason wannan auran to amma yaya zaiyi bazai iya yima Mahaifiyar shi musuba babu yadda zaiyi dole yadubi mama yace " to Mama tunda kinason hakan Allah yasa hakan shine mafi alkairi " murmushi mama tayi tace Allah yayi maka albarka  Amin yace yami'ke yafita murmushi hjy Himla tayi shiko Abdul mi'kewa yayi yafita fuskar shi d'auke da murmushi part d'in Ammin yanufa sabida yasan Bahijjat tanacan yana shiga yasameta zaune akan cushion tana latsa wayar ta Zama yayi kusada ita afurgice tadube shi cikin fad'a tace 


" Maiye haka Yaya Abdul Babu ko sallama wallahi ni Kam kabani tsoro " tamke fuska yayi yace " to banyi niyyar yin sallamar ba jawota yayi tafad'o jikin shi babu zato rungumai ta yayi sosai  yakawo bakinshi dede kunnanta yace " zuwa nayi nasanar dake cewa Maimartaba Zaid yabani auran ki kinga kenan daga yau zakifara yimin biyayya " cikin zafin rai tatura shi tadube shi tace Allah yatsari gatari dasaran shuka wallahi dana aure ka gara namutu babu aure kasani Ni Bahijjat ba irin matar kabace " 


Murmushi yayi yasake matsowa kusada ita babu zato taji ya wanketa da mari mai matu'kar zafi 'kara tasaki hakan yasa Ammin fitowa ganin Abdul agaban Bahijjat itakuma tadafe kuncinta yasa Ammin tafahimci abinda Abdul yayi ma Bahijjat cikin fad'a tace " haba Abdul maiye haka da girmanka  kake cin zalin 'kanwar ka idan wani abu tayimaka ay seka sanar dani nayi mata fad'a ko " murmushi  Abdul yayi yace " Babu ruwan ki Ammi tsakanin mata da miji ne Kinga babu buqatar sanar dake " daga haka yajuya yafita yana sakin shi'umin murmushi bin shi Ammin tayi da kallo tana jinjina rashin kunyar Abdul juyawa Bahijjat tayi cikin kuka tarungume Ammi tace " Ammi dan Allah karku bari a auramin wannan azzalumin kingani tun yanzu yafara nuna muguwar d'abi'arshi  Ammi dan Allah " dede lokacin Zaffar yashigo shi d'ah ne ga yayan Ammin tsayin 5 yrs kenan da yin auran shi amma kas lokacin haihuwar matar shi tafari Allan yayi mata rasuwa bayan tahaifi kyakkyawar yarinya Mai Kama da ita  tun daga  wannan lokacin Zaffar yarufe shafin wata mace bashida abin dubawa se 'yarshi wato baby wadda taci sunan Mahaifiyar ta yad'auki dukkan lokacin shi da kulawar shi yabama yarinyar shine yakeyi mata komi yaqi bakowa ita duk da cikin yan'uwan shi dayawa sun nuna sunaso ciki hadda Ammi kimanin shekarun baby 4 kenan akwai wayo gurin baby sosai wannan kenan 


Yana shiga yadubi Ammi yadubi Bahijjat dake kuka   sama yayi sannan ya gaida Ammin gaidashi Bahijjat tayi sannan tabar gurin takoma qaramin parlour bayan fitar Bahijjat Ammi tadubi Zaffar tace " lalle ashe yau zamusha ruwan sama cikin garinnan Zaffar yau cikin gidan nan ? anya kuwa shine bagizo idanuna sukeyiba ?" d'an murmushi Zaffar yayi yace " nine Ammin bagizo bane " hmmm " Ammin tace sabida mamaki sannan tace " lalle de kam amma Ina baby yau naganka babu ita murmushi yayi yace " ay baby angirma tana Skul  nima yau Ina hutu banje Hospital ba shiyasa 'kila se zuwa yamma " dede lokacin Bahijjat takawo ma Zaffar abun motsa baki da lemon bayan ta aje tajuya hira Ammin da Zaffar suka shigayi zuwa can Ammin tace 


" Wai nikam Zaffar yaya batun aure ne ? kasani zamanka hakafa bazai yiyu ba Zaffar idan kaqi yin wani auran tofa kamar baka yadda da qaddarar da Allah yad'aura maka bane Zaffar kad'aure kayi aure kodan baby dole tana buqatar samun kulawa daga mace sannan kullum tanayimaka kukan Ina Momy kaga idan kayi aure baby zatabar kukan rashin Momyn tata Dan Allah Zaffar " ajiyar zuciya yayi sannan yace 


" Ammin bawai na'kiyin aure bane sabida kasa yarda da qaddara a a Ammin sedan bazan iya sake son wata 'ya mace ba Ammin banaso nayi aure amma yazama nakasa sauke haqqin matar sabida gaskiya tunda Nuratu tarasu narufe zuciya ta na kulle idanuna daga kowace irin mace ayanzu babu abinda nike kallo naji dad'i kamar baby kuyi ha'kuri Ammin bazan iya sake saka wata mace cikin zuciya ta ba zanjira har namutu naje natadda matata Nuratu ina roqon Allah yahad'a mu cikin gidan aljanna tare " 


Ajiyar zuciya Ammin tasauke tace " amin ya Allah amma Zaffar amatsayina na qanwar Mahaifiyar ka ina roqon wata alfarma kuma banaso kayi musu idan har na'isa Zaffar inaso ka auri 'yata Bahijjat " saurin dubanta yayi sannan yadubi hanyar da Bahijjat tabi bayan takawo mishi abun motsa baki bud'e baki yayi zaiyi magana Ammin tace " karkace komi ni zanji da komi Zaffar dan Allah karkace a a tabbas zakasamu tsananin kulawa agun Bahijjat Kuma daga lokacin da Bahijjat tashiga gidan ka baby tabar kukan rashin Mahaifiya idan har dagaskene bakason damuwar baby balle kukanta to kasamar mata da wata Mahaifiyar wacce zata maye mata gurbin tata Mahaifiyar "


Iska Zaffar yafesar yace " shi kenan Ammin amma fa banajin zanso Bahijjat zanyine dan ke Kuma dan baby amma badan ra'ayin kainaba " sosai Ammin taji dad'in hakan tashi yayi yayimata sallama yafita Kiran Bahijjat tayi cikin sanyin jiki   Bahijjat tafito tariga duk taji komi zama tayi kusada Ammin cikin wani irin yanayi murya a raunane tace " Ammin Abbee yariga ya amsa cewa Abdul zan aura Kuma Ammin Zaffar basona yakeyiba inajin tsoron auran Wanda bana gabanshi " jawota Ammin tayi jikinta tace 


" Kwantar da hankalin ki Bahijjat nasan Zaffar zesoki Kuma zakiji dad'in zama dashi  sannan maganar auran ki da Abdul abune mai sau'ki wajan warware shi amma idan Kika sanar da Saraki cewa bakison Abdul ke Zaffar kike so tonasan zeyima mama magana Kuma kinsan  yadda mama takeson Saraki duk abinda yakeso  zatayimai Babu musu bari zankirashi dakaina muyi magana dalilin dayasa nace ki auri Zaffar idan babu maganar auran wani tofa babu mafita   kuma badan Zaffar yana matsayin d'ah agareniba nake  son ki aure shi a a kyawun halin shi da kamalar shi tasa nike miki shi'awar auran shi dakuma gujema auran Abdul "  murmushin farinciki Bahijjat tasaki sosai taji dad'in abinda Ammin tace amma tana tunanin yadda zatayi zaman aure da Zaffar dan tasan halin Zaffar danuna halin ko in kula damutun 


Bayan Bahijjat tatashi Ammin takira Saraki take sanar da shi suna gama waya Saraki yakira mama magana yayi mata a takaice  " _mama  barka da yau fatan kina lfy naji kince maganar auran aunty Bahijjat  to amma mama ni yanzu bankai matsayin asanar daniba ? kema kinyarda ni marar hankalin ne mama ? komade Yaya kuka d'auka ni amatsayina na shaqiqin Aunty Bahijjat tuni nariga nayima akeey Zaffar al'kawarin auran Aunty Bahijjat Kuma itama nasanar da ita kuma ta amince dama jira nikeyi Abbee yazo nasanar dashi to amma ni bazance kucanza ra'ayin kuba amma idan kuka qi to tabbas kund'aukeni marar hankalin nabarku lafiya_ " 


Kafin mama tasakecewa komi tuni  Maher yakashe Kiran sosai hankalin mama yatashi tuni tasa aka kiramata maimartaba da hjy Himla da su Ammin Babu 'bata lokaci kowa ya hallara cikin parlour bayan kowa yazauna mama tadube su tace " ke Himla akan maganar auran Bahijjat da Abdul ayanzu Kam Babu ita kafin maganar Abdul tuni Saraki ya amshi maganar Zaffar wato d'an wan Batol se yanzu yake sanar dani Sabida haka Abdul yayi haquri yanemi wata mu aura me " wani irin farinciki kowa yaji amma banda hjy Himla data miqe tace 


" Amma gaskiya mama hakan beyiba yanzu ace har Saraki yakai matsayin amsarma Bahijjat miji bacin maIdanuwan bana guri shine jagoran su dan haka yanada cikakkiyar damar za'bama Bahijjat miji dukda tana matsayin Aunty shi sannan daga yau karki sake fad'in kalmar hauka akan Saraki Shiba hauka yakeyiba lalurace Allah yasaukar mishi Kuma in sha Allah tazo 'karshe mama Ina godiya agareku dakuka babbatar ma Saraki cewa ya Isa dakoma cikin masarautar nan Ammin Saraki kisanar da Zaffar na amince yaturo magabatan shi " 


Daga haka Sarki Zaid yafita Ammin da Umma Suma sallama sukayima mama suka bar parlour itako hjy Himla afusace tabar parlour tana shiga cikin parlour ta tad'auki wayarta takira bokan ta yanad'agawa tace " boka akwai matsala fa wannan banzan Saraki yana lalata min komi dan Allah kasheshi nike buqata tuntuni amma kakasa haba boka gaskiya nagaji idan bazaka iyaba to kasanar dani nacanza guri " dariya boka yasaki sannan yace " haba hjy Himla karki bani kunya Mana komi yakusa zuwa qarshe yanzu matsalar mu wannan matar tashice bamu iya yimata komi sabida tanatare da addu'a akoda yaushe Kuma ayanzu haka tafara shayer dashi addu'ar Kuma yafara samun sau'ki amma yanzu matakin dana d'auka shine zamu gigita ta tahanyar bata tsoro zamusa adinga furgitata sosai ta yarda dole zatabar gidan ki saurara kiji Nan kusa zatabar gidan Maher " 


Ajiyar zuciya hjy Himla tayi sannan tace " to naji amma inaso kalalata auran Bahijjat da Zaffar da'ake Shirin qullawa " dariya yabushe da ita sannan yace  " angama kisaurari ayki kawai amma inajiran ganin saqon Kaya masu nauyi " tsaki hjy Himla taja tace " yaushe na ayko akakawo maka kud'i to kasani inajiran naga ayki yaci kafin nasake ayko dawasu kayan " daga haka takashe wayar "


Zama tayi kan cushion tana huci dede lokacin Abdul yashigo ganin yadda ran Mahaifiyar tashi yake a hatashe yasa Abdul dakatawa tambayar ta yashigayi cikin fushi Abdul yace " Mom wallahi tunda aka hanani auran Bahijjat sena lalata mata rayuwa wallahi senasata taje gidan mijin batare da budurci ba tuni nike kwad'ayin surar jikin Bahijjat Mom zasunan ni suka hana auran Bahijjat " murmushin mugunta hjy Himla tayi tace " kayi duk abinda kake ganin zaisaka kahuce my son " murmushi yasaki yace " zanyi kuwa Mom 


USA


Akwana atashi babu wuya ayau ne doctor yake kan hanyar zuwa USA Abbee Kuma yasaka a Nigeria abubuwa dayawa sunfaru kafin wannan lokacin sosai Iftahal tayi muguwar rama sabida ko abinci bata iyaci hatta ruwa idan zatasha inba tayi addui ba seyakoma kamar jini duk tagama furgicewa yauma kamar kullum hankalin ta cikin Matu'kar tashe yake Sabida tayi duk tunanin dayakamata amma tarasa yadda zatayi wajan hana doctor yin wannan allurar shigowar Maher yasa Iftahal saurin zaunawa isowa yayi yazauna kan cushion ciro sigari yayi yakunna yafarasha kallonshi Iftahal tashigayi sosai tanajin matu'kar tausayin shi da tsananin qaunar shi cikin zuciyar ta d'an dubanta yayi se'alokacin yaga tayi wata irin muguwar rama sosai yaji mamakin hakan a hankali yadubeta yace 


" Iftiih!!!! meye dalilin ramarki nalura bakison cin aminci sannan kinsan nace idan har kinason nayi miki abinda kike so to yazama dole ki kwantar da hankalin ki amma bakiji magana taba " cikin raunin murya Iftahal tace " bahaka bane Prince kusan 1 week kenan banajin dad'in jikina shine kawai amma Babu wata damuwa " jinjina Kai yayi sannan yamiqe yace " tashi muje Asibiti " daga haka yanufi hanyar fita cikin sanyin jiki tamiqe dan Babu yadda zatayi tabbas batajin dad'in jikinta to amma batason zuwa asibiti d'an tsayawa tayi tace " am Prince nifa banason zuwa asibiti nan naji sauqi sosai " wata irin harara yasakar mata dole tashiga bedroom ta d'akko gyalenta tana fitowa yawatsa mata wani irin kallo yace " bana buqatar  shigar banza " duban mayafin tayi ba qarami bane Kuma yarufe mata jiki sosai " dole takoma ta d'akko hijab tafito suka fita 


Nigeria 


Sarki Zaid da waziri da liman suka sauka Nigeria cikin babban birnin tarayya wato Abuja basusha wahala ba wajan Isa gidan Alhaji Ishaq wato minister kud'i sosai akayimusu tarba tamusamman bayan sunhuta suka zauna cikin ke'bantaccen parlour duban Alhaji Ishaq Sarki Zaid yayi sannan yace " Alhaji kasan daga Egypt muke tun zuwanmu amma zansake sanar dake sunana Zaid Irfan wato Sarkin qasar Egypt ayanzu nine mahaifin Maher wato mijin 'yarka Iftahal Alhaji nataso daga Egypt ne  har nan Nigeria dan baka ha'kuri akan abinda Maher yayi shine yakeda lefi ba Iftahal ba sabida  ita FURUCI!!!! tayi bada niyar yin aure ba amma FURUCIN!!!! yazama dalilin auran su to mud'auka wannan abun daga Allan ne tunda kaga hakan tafaru to Allah kad'ai yasan dalilin haka iname baka ha'kuri Kuma Ina taya Iftahal da Maher roqon ka akan kayafe musu dan Allah musamman Iftahal kasan fushin iyaye akan 'ya'yan su babbar matsalace dan Allah kayi ha'kuri sannan ayanzu inajiran duk wani bayani akan yadda kuke shirya naku auran zamubi dukkan wata al'ada taku aure de anriga anyi duk mubar wa Allah ikon shi "


Mi'kewa Alhaji Ishaq yayi sannan yace " nayi farincikin zuwanku hakan yasa na tabbatar kai Sarki ne Mai adalci cikin masarautar ka tunda har ka it's tasowa daga Egypt zuwa Nigeria akan bani ha'kuri dakuma neman yafiya nagode sosai amma sede wani abu 1 ni banayin magana nacanza bazan iya maida Iftahal matsayin 'yataba nariga nayafeta gareku nikam banida wata 'ya maisuna Iftahal kusani nayafe mata Amma bana bu'katar sake ganinta arayuwata har abada nagode sosai Maimartaba inatayaka munar samun qaruwar wata 'yar wato Iftahal " mi'kewa Saraki  Zaid yayi yace " nagode sosai daga yafe mata Kuma nayi matu'kar farinciki dabani 'yah mai hankali da tarbiyya irin Iftahal muzamu koma fatan alkairi ga sadakin Iftahal Nan " saurin juyowa Alhaji  yayi yace banida alaqa da sadakin 'yar daba tawaba dan haka bana bu'katar ganin su " sake Sarki Zaid yayi yafita waziri ne yad'akko kud'in suka fito hotel suka nufa Sarki Zaid sosai yashiga damuwa akan yadda Alhaji Ishaq yayi fushi da Iftahal


USA


Suna Isa asibiti doctor Sera tayima Iftahal tambayoyi sosai bayan haka aka d'ibi jininta akashiga gwadawa bayan wani lokaci doctor Sera tadawo zama tayi tadubi Maher da Iftahal tayi murmushi tace " Prince ina tayaka murna gimbiya tanada ciki tsawon 5 weeks " cikin matu'kar mamaki Maher yadubi Iftahal zaro ido tayi tadafe qirjinta tsayin lokaci yakasa denayimata kallon mamaki itakuma takasa cewa komi kuma takasa d'auke idon ta daga kanshi juyawa yayi yafita afusace batare dayace komiba 



Comments please

No comments