YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 28-29
*NUSAIBA*
*YAR AMANA☘️☘️*
Rutawa: Karimatu Abdulhamid
( *MUMMYN MINAL*)
*PAGE 28-29*
____ Wani wawan bugu Mum takai abakin matar, ai kuwa bakin matar ya 'balle da jini cikin masifa Mum tace" qarya kukeyi ni Murjanatu nafi qarfin inzauna da kishiya! Inma kishiyarce ban zauna da ita tun yarinta ba sai yanzu da girma yazomin za amin kishiya ai wlh qaryane. Lalle Alhaji kataro mach baka da filin buga qwallo sbd da haka kafin na qirga uku wlh ku fice da tsinaniyar amaryarku ko kuma yanzunan infafasa muku kawuna"
Acikin matan kuwa wata ce daka ka ganta kaga gogagiyar 'yar bariki wanda bariki ya ratsata, d'amara taci da mayafinta akunkuminta tafito gaban Mum ta doki gaban qirjin Mum tace " ke Hajiya idan kinfasa fasa mana kai kinci abutakazar 😷
Harmu zaki fad'awa bariki dan ubanki to bara kiji mu mune bariki kije kiyi tambaya a tudun wada kice ladidi bariki to za akawoki gurina ai mu mune qarshen bariki dan kuwa tamu barikinma a Lagos mukayita a Lagos d'inma a ogere, daga ogere har agage duk mune sbd haka wlh ki iya bakinki ko ki kwashi kashinki ahannu"
Ita kuwa FINAH me zatayi inba dariya ba domin taga bakin Mum ya mutu murus jikinta sai tsima yakeyi dan haka takoma gefe tana qunshe dariyarta wai Daddy yayi aure.
Cikin Masifa Mum tace " to ko a America kukayi barikanci ni gidana yafi qarfinku wlh. Domin gida nawa ne nikad'ai dagani sai 'ya'yana ba wata shegiya da zata shigo gidan nan"
Bangajeta ladidi bariki tayi tace " maza kuzo muwuce kubar wanan karyat taci gaba da haushi domin kuwa gida de yazama namu wlh dan kuwa Alhaji Maina yau d'inan sai yaje duniyar da baita'ba zuwa a gidan nan"
Haka kuwa suka ra'ba Mum suka shige da Amaryarsu suna ya 'bawa Mum surutai.
Ita kuwa Mum zama 'Yan bori tayi aqasa tana kuka mai ciwo tana cewa "Yanzu daddyn Abdul ni zakaci amana d'anmu da yake da yarinta bai qara aure ba sekai tsofe-tsofe dakai oh ni Murjanatu Shikenan qawayena zasuyimin dariya akan nakasa riqe gidana "
Matsowa kusa da MUM FINAH tayi da take ta qunshe dariyarta sanan tace " ai Mum shawarar da zanbaki kiyi shiru ki goge hawayenki mushiga ciki kawai de magana d'ayace karki yadda kiyi ta tadawa daddy hankali harsai yakori amaryar"
Tashi Mum tayi tana goge hawaye tace " Shikenan FINAH muje ciki amma nikam daddynku ya cuceni ya d'aukomin ruwan bala'i kina jifa waisu dangin bariki ne"
"Yo ai Mum nuna musu zakiyi kinfisu bariki! Toma ni Mum intabayeki mana"
"Inajinki FINAH"
"Shin sakin da Daddy yayimiki ya janye?"
"To bama dolensa yajanyeba duk da wanan abun tsakanin mune"
"To Shikenan Mum amma wlh ki tabbatar ya maida ke d'akinki kafin yaje wajan waccar 'yar barikin amaryar tasa inkuma kikayi sake saide kijiki waje road"
"Dagaske ko FINAH?"
"Eh mana Mum"
"To Shikenan ai kawai ki shiga ciki inan inajiransa yadawo insan matsayina agidan nan"
Haka kuwa Mum taqi komawa ciki Ta tsaya aharabar gidan sauro na ta cizonta ita kuwa FINAH tana can taqira mahaiyarta awaya tana bata labari suna ta kwasar dariya, inda mahaifiyar FINAH tace " kema daughter zantashi intsaya akanki kar wanan yaron yamiki kishiya domin mu bamu gadi zama da kishiya ba, nan FINAH taitayiwa MUM dinta godiya qarshe ta kashe wayar tai kwanciyarta abunta sai kuma tinanin ABUDULJABBAR yafad'o mata akan ina ya shiga kwana biyu, sai wata zuciyar ta raya mata ko shima auran yaqara ne, Dam. Qirjinta ya buga.
Ita kuwa Mum tana nan tsaye 'Yan kawo amarya suka watse can sai ga Daddy ya shigo gidan da motar sa megadi ya bud'emar get, yana gama parking din motarsa ya fito a motar cikin shigar ALFARMA sai zabga qamshi yakeyi da wata qatuwar leda ahanunsa, 'bangaren Amarya ya nufa take Mum dake la'be taji gabanta ya fad'i aguje tafito taje tasha gaban Daddy, shiko daddy cewa yayi miye haka Murjanatu meyasa ku mata manyanku da yaranku hankalinku daya?"
Cikin kuka Mum tace " yanzu dan Allah Alhaji abunda kayimin ka kyauta kenan tun muna da yarinta bakayi aure ba sai yanzu da girma ya zomana"
"Dakata Murjanatu idan kina magana kiringa sawa da minjaye ni girma baizominba ke yazowa sbd haka sai kirungumi qadara karki kiga ina da kamar Abdul ki zaci na tsufa to wlh da saurana sbd haka kije kuci gaba da tafka rashin mutunci keda surukarki nidai nafita asabgarku"
"To yanzu makeke nufine Alhaji da nawa auren ka maida ni ne ko yaya?"
"Eh na maidaki sbd d'anki da yaroqa miki haka kinci darajar yaro mai biyaya"
Fuuuuuu yayi wucewarsa 'bangaren Amaryarsa.
Itako Mum cikin kuka tace " Alhaji ni Murjanatu sai na nuna muku banda mutunci wlh nima bantsufa ba da saurana sbd haka muzuba mugani"
Awanan darande Mum kwanan baqin ciki tayi, shiko daddy kwanan Soyayya sukayi shida Amaryarsa.
___________________________
A 'bangaren 'YAR AMANA da IKIRAM kuwa kamar yanda daddy yace hakan sukayi anatashinsu daga school suka wuce gidan Aminin daddy Alhaji dala, inda anan ne 'YAR AMANA taga duniya taga gida Aljanar duniya domin kuwa Alhaji dala yafi daddy kud'i, saide matar Alhaji dala Hajiya Aisha, bata d'auki duniya komai ba sam bata da rawar kai da girman kai irin na matan masu kud'i, ita mutum ce maison talaka da tausayinsa wanan dalilin yasa Mum bata fiya harka da itaba, koda su IKIRAM suka isa sosai Hajiya Aisha tayi farin cikin ganinsu, inda ita Hajiya Aisha take da 'ya'ya uku Mus'ub da Safna, da sakina, yaya Mus'ab shine babba sa'an ABUDULJABBAR wanda yake aikin bank, a counter shi, Sai Safna mai bimar, wacce take karatu a poly, amma Safna mugun girman kai gareta dan ita kaf gidan halinta daban batayo halin iyayenta ba, kuma Safna tun tana qaramarta takeson ABUDULJABBAR amma girman kai ya hanata ta nuna koda kuwa ashi ABUDULJABBAR d'inne, sai Sakina auta ita kuma sa'ar IKIRAM ce itama ba ruwanta domin tana da sauqin kai.
Haka kuwa su IKIRAM suka samu Alhaji dala da iyalansa dukkansu a parlour inda Sakina tana ganinsu tai tsalle tarungume IKIRAM, nande aka hau hirar yaushe gamo itako Safna tsaki tayi tashige ciki, domin batason hayaniya, shiko Mus'ab sai tsonar IKIRAM yakeyi My wife domin haka yake tsokanarta, nande IKIRAM taga batar musu da 'YAR AMANA akan 'yar qanin daddy ce, nan de sukaci suka sha Sakina tajasu zuwa dakinta sukayi wanka suka sanja kaya inda suka shiga wayar da kan 'YAR AMANA suna koya mata turanci.
Shi kuma Alhaji dala da Mus'ab suka wuce massalacin juma'a
Har dare Daddy baizo d'aukar su IKIRAM ba dan haka hankalin IKIRAM ya tashi tace Ya Mus'ab ya maidasu gida amma Daddyn Sakina yace "A'a ai d'azu mukarabu da daddynku yace ku kwana anan"
Haka kuwa akayi bayan sungama hirarsu a parlour harda ya Mus'ab domin shi yace yayi kamu IKIRAM yakeso inda iyayenasu ke tamasa tsiya wai IKIRAM tayi mar qarama yanemo mata, shiko yace yana jiranta, qarshede su IKIRAM suka shige d'akin Sakina suka kwanta abusu.
Arugar su 'YAR AMANA kuwa tinda 'YAR AMANA tabar rugar Baffa bai qara lafiya ba danko fita baya iyayi, dan haka yanzu abun duniya ya ishi Gwaggo dan kuwa bamai zuwa mata talla ya samo mata kud'i qarshe da rashin kud'in ya isheta sai tafara tallar furan da kanta, amma me bawanda yake siya, tinifa komai yayiwa Gwaggo zafi tarasa ya zatayi tana cikin wanan halin qawarta asabe tasake zuwa inda tabata shawarar tabar auren su shiga birni neman kud'i kawai hakance kuwa ta faru domin dukka shanukan baffa da kajinsa da zabinsa Gwaggo da qawarta suka kwashe suka seda suku gudu, bayan guduwar Gwaggo Baffa yafara samun sauqi sbd rubutun da Mallam ke kawo masa kullum yake sha, koda Baffa ya samu sauqi sai yaji shima bazai iya zaman rugarba yayi kuka sosai narashin 'YAR AMANAR sa domin kuwa komai yafaru ne shide bai cikin haiya cinsa dan haka Baffa ya tatara Sauran abunda ya ragemasa shima yataho birni ko da Allah zaisa wata rana ya had'u da 'YAR AMANA domin kuwa yasan a d'an birni suka aurarwa ita.
Gari na wayewa FINAH tafito a d'akinta a haukace kici'bis sukaci da Mum, Mum tace " lafiya FINAH ina zakije haka"?
Cikin masifa FINAH tace " neman mijina zanje zanine induba sabon gidan mu ko shima auren yaqara ba musani ba"
Fuuuu tawuce tana kad'a key d'in motar dake hanunta da gudu gudu tashige cikin motar, ta tadata da sauri megadi ya bud'emata get, aguje tafice agidan kai tsaye Sardaunah crescent FINAH ta nufa da sanyin safiyar nan tana ta tsula uban gudu akan titi, aqofar had'ad'en gidan ABUDULJABBAR tayi parking inda tafita amotarta tasamu gidan arufe da paddock sanan tayi sanyayar ajiyar zuciya ta shiga motar ta taqara gaba tana tunanin ina to ABUDULJABBAR ya shiga haka kwana biyu? Karya kan motarta tayi tanufi titin gidansu.........
To pans wai ina labarin ABUDULJABBAR ne?
Maza ku nemowa FINAH masoyinta
No comments
No Typing
Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere asauran groups👏
*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*
No comments