Breaking News

SHINE SILAH 36-40

 *PAGE* 36-40

.........................📖"Baka san hanya bane da zaka ce na raka ka to in kamanta hanya ka kirata ai ba kunya gare ta ba da kanta zata fito kutafi tare"  fuska ya had'e yace "kowa ma mara kunya ne kar ki 'kara kiran matata mara kunya nafada miki"  daga haka ya mike ya fuce daga d'akin ai Najma kasa kuka tayi in banda rawa da jikin ta yakeyi kamar mazari 




Najma yadda taga rana haka taga dare bawai kishi ne ya dame taba sauya war Najib ne ya 'daga mata hankali 

Allah ya gani tasan yanzu auren ta da Najib yakusa zuwa 'karshe tunda dama danginsa ba sonta sukeyi ba uwa uba Mahaifiyar sa yanzu gashi lokaci guda shima ya sauya mata gaba 'daya tasan shike nan watan mutuwar auren ta yazo 

Tana zaune har aka kira salar Asuba ta mike taje ta 'dauro alwala tayi raka'atul fijir sannan tayi salar Asuba tajima tana karatun Alkur'ani me girma sannan 'daga hannu tana mik'a kukanta gurin rabil izati ta jima tana addu'a kafin ta shafa ta mike ta cire hijab 'din nutsuwa na saukar mata ta koma kan bad ta kwanta bata jima da kwanciya ba bacci me nauyi yayi awan gaba da ita.




10:00am Najib ya shigo part 'din ta kitchen yashiga yaga ba abuda tayi tsaki yaja ya koma 'dakinta yana kiran sunanta "Najma Najma" ido ta bud'e wadda yake cike da bacci tayi mik'a ta mik'e zaune tana murza ido "sabada wula 'kanci kinsa kinada Amarya a gidan nan kika kwata kina baccin asara har 10 kina kwance"  Najma kalonsa kawai takeyi lamarin Najib har ya daina bata mamaki  cikin nutsuwa tace "kayi hakuri na 'dauka Ammi zata kawo muku amma zanyi yanzu amma fa iya naka dan bazan yiwa katuwar banza ba wallahi"    cikin fushi yace "wallahi sai kinyi kuma har part din ta sai kije kin gyara mata tunda tana kwance ba lafiya"  "balla gazar matar taka da ta saida mutun cinta a titi da namata girki gara nayiwa karnik.......!"  Marin da taji ne yasa ta kasa 'kara maganar da take ta kafeshi da ido cike da mamaki wannan shine karo na farko da suka ta'ba sa'insa da Najib harya 'daga hannu ya mareta  



Nuna ta yayi da yatsa yace "kar ki k'a zagin matata kuma ko ta zubar da mutunci a titi ita nake so kuma nake da tabba cin zata haifa mun yara dana ke so ke kuma saidai kici ki kashi amma badai haihu wa ba kuma nabaki nan da 30m kiyi mana bearkfast inkuma baki jiba kiyi zamanki" daga haka ya fice da kalo Najma tabisa hawaye na bin kuncin ta




Dole haka ta mike tashiga kitchen ta hada musu bearkfast ta ajiye masa a parlour tashige 'daki ta 'datso kofa ta murd'a key ta koma ta kwanta

Amma ta kasa komawa baccin da takeyi abun duniya yai mata zafi tabbas tayi babban kuskure akan biyewa son zuciyar Najib tayi Family plan tun tana budurwa bata da tabacin zata haihu ko ma bazata haihu ba gashi yanzu ya kaita ya barota shi kuma yaje yayi auran sa kamar ba SHINE SILAH komai ba 




Wasu hawaye masu zafi ta share a ranta tana jerowa Najib Allah ya isa dan ita yanzu gaba 'daya ya fita a ranta gani take kamar ba sonta yake ba akwai manufar da yasa tun farko ya aure ta ma

Tana kwance a gurin har akayi azahar sannan Allah ya bata ikon 'dagawa daga gurin ta tashi danyin salah.



Haka abu buwa marasa da'di suka cigaba da faruwa a gidan Najma tana ganin taskon rayuwa Naji duk ya juya mata baya ko kalon inda take bayayi ya hanata fita koda da kofar gidane bare taje gida ko School hanka linta ya 'dan kwanta in taga kawayen ta ko taje gida ko su Annur sa 'debe mata kewa amma Najib yaja ya hana abu kamar asiri ya tsane ta da duk dan ginta





Yau abokin Najib Ahmad wadda sukaje gidan sa da Najma yazo ganin Amarya har parlour Amarya aka kaishi Najib sai washe baki yakeyi Ahmad ya dubeshi yace "nayi mamakin 'kara auren ka Najib kana da mata kamar Najma amma har kake sha'awar 'kara aure"  murmushi yayi yace "in banda abunka Ahmad yanzu ai an daina 'bata lokaci akan mace 'daya kuma ni dama Najma can auran sha'awa nayi da ita shiyasa na hata haihu ita kuma Khairat zan iya zama da ita tunda haka Mami take so"   wani irin rad'ad'i Ahmad yarin ga jin zuciyar sa na mai "amma dai Najib baka da imani kason bazama zakayi da itaba zaka auro ka ajiyeta a cikin gidan ka sabuda son zuciya irin naka"  "Ahmad nifa inada kudi bazan zauna naki jin dad'in rayuwa ba dan dani ne da arzikinka ina auro 4 suka tashi daga aiki saina sake su na 'kara auro wasu 4" Ahmad lamarin Najib ya fara bashi tsoro 




Khairat ce ta shigo parlour tana wata kwar kwasa da iyayi Ahmad ne ya 'dago ya kaleta ya zaro ido itama tana ganin sa jikin ta duk yayi sanyi mikewa Ahmad yayi ya kali Najib yace "zab'in da kayi yayi tun yanzu Allah yafara sakawa bai warsa Najma"  yana gama fad'in haka ya fice a fusace 

Duk suka bishi da kalo Najib ya kali Khairat yace kin san shine jikin ta na rawa tace "Aa ban san shiba walahi"  badan ya yadda ba ya rabu da ita





Ahmad na fita yashiga mota yazaro pepper yayi rubutu yaja motar sada yazo saitar me gadi ya mik'a masa ta karda yace ya kaima Najma dan Allah "to insha Allah" me gadi yace Ahmad yabashi kudi ya tafi.




Tana zaune a parlour taji a na knocking izini ta bayar aka shigo me gadi ya durkusa ya gaida ita ta amsa sama-sama dan bata so masu aikin gidan maza suna shigowa b'an garenta  pepper ya mik'a mata yace "gashi inji abokin Alhaji daya zo yace a kawo miki" "nikuma yace a kawowa"  "eh gashi" amsa tayi cikin mamaki tace shikenan zaka iya tafiya "to" yace yafice daga parlour 



Komawa tayi ta kwanta akan kujerar ta bude pepper ta fara karan tawa kamar haka



ASSALAMU ALAIKUM WARAHA MATULLAH WA BARA KATUHU, BARKA DA WARHA HAJIYA NAJMA DA FATAN KINA CIKIN KOSHIN LAFIYA.

DA FARKO INA ME BAKI HAKURI NAZO GIDAN KU BANZO MUN GAISA BA SABUDA KUNYAR KI DA NAKEJI TABBAS NAJIB YAI MIKI BUTULCI KUMA YA ZALIN CEKI AMMA KI BARSHI DA FITOWAR RANA DA FADUWARTA, KOYI HAKURI NAJMA NASAN KINA BUK'ATAR TEMAKO DAN HAKA GA NUMBER TA KI NEMENI IN KINA BUK'ATAR WANI ABUN NAGODE KI HUTA LAFIYA



rife pepper tayi tana goge hawaya yen da suka zubo mata ta zame ta koma 'kasan glass carpet ta zauna tana jin zuciyarta tana zafi da kuna ido ta rintse ta ringa mai-mai ta "inalilahi wa'ina ilaihirraji'un Allah ka kawo min 'dauki" tajima a gurin kafin taji zuciyar ta tayi sanyi ta mik'e ta ciga ba da aikinta.



Bayan kwana biyu



Yanzu Najma ta dai na sa Najib a idon ta ko part din ta ya daina zuwa kuma ita hakan dadi ya mata dan ko ya shigo cin mutun cine yake kawo shi



Yauma kamar kulum ta kule a bedroom tana aikin tunani yawar ta ta zaro ta k'ara nemo number Ahmad data sa kusan kwana biyu amma ta kasa kiransa har zata danna kira tai saurin girgiza kai zata ajiye wayar taji an banko kofa an shigo a tsorace ta 'dago tana kalonsa shikuma sai huci yakeyi ya jefo mata takarda yace uban mene hadinki da Ahmad pepper ta dauko ta duba ta gani ido ta zaro ganin bata da alak'a da wace ya kawo mata a salima ta yadda wacan wannan in banda magan ganun batsa ba abunda aka rubuta,  



Abuda Najma bata sani ba lokacin da megadi ya fita daga part din ta Khairat ta fito ta tsareshi ya fada mata Alhaji Ahmad ne yabashi ta karda ya kaiwa Hajiya salamar shi tayi taje tasamu 'yar aikin ta tace taje ta nemo mata wannan pepper haka kuwa akayi ta samo Najma ta yarda ta dako suka kwafi irin rubutun suka juyata tazoma kamar Ahmad da Najma amanar Najib sukeci su yarda pepper ida zai gani akuwa yana gani yaje zai karewa Najma tanadi.




Kaita girgiza tace "wallahi ba wannan abun ya rubu taba Allah kuw........!" mari ya dauke ta dashi wadda yasa ta sakin wayarta bata sani ba ya dauka yaga Number Ahmad akan kira ai sai ya buga wayar da 'kasa ta fashe ya 'dako yace "nasake ki kije kuciga ba da iskancin a gidan dan iskan ubanki dama ai barewa bazatai gudu 'danta yai rarrafeba"..........!




COMMENTS

AND

SHARE 



by

*XAHRA*

No comments