YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 26-27
*NUSAIBA*
*'YAR AMANA☘️☘️*
*TUNATARWA*
*ALLAH MA'DAUKAKIN SARKI YACE:*
*YAKU WA'DANDA KUKAYI IMANI! IDAN ANYI KIRA ZUWA GA SALLAH ARANAR JUMA'A SAI KUYI AIKI ZUWA GA AMBATON ALLAH, KUMA KUBAR CINIKI DOMIN SHINE MAFI ALHERI AGEREKU IDAN KUNKASANCE MASU SANI. SA'ANAN IDAN ANKARE SALLAH TO SAI KU WATSU A CIKIN K'ASA KUMA KU NEMA DAGA FALALAR
ALLAH,KUMA KU AMBACI SUNAN ALLAH DA YAWA KO ZAKU ZAMO MASU BABBAN RABO.*Wato anan Allah( S.W T.) Yana cewa ne yaku wad'anda kukayi imani idan kunji anyi qiran sallar juma'a, sai kubar kasuwancinku, ku tafi zuwa gayin sallah, idan anqidar da sallar sai ku watsu acikin qasa ku nema daga falalar Allah sanan ku kasance masu yawan ambaton Allah wato tasbihi, ko zaku kasance masu samun babban rabo. SURATUL JUMA'ATI (10) Ya Allah kasance mudace ya Allah kasa mubika Ya Allah ka qaramana son manzo( S. A.W) Amin
Barkanmu da ranar juma'a 'yan uwana musulmai Allah ya sadamu da Alkairin dake cikin ta.
*PAGE 26-27*
____ Sosai daddy ya kalli d'anasa sanan yace " A'a ABUDULJABBAR bazan ta'ba bari ka saki NUSAIBA ba! Domin karka zo kana da nasani marar AMFANI. Bazan ta kura makaba akan sai katafi da ita ba. Saide ina so aduk inda kake kazamo mai gaskiya da ruqon AMANA da kuma kare mutuncin addininka da al'adarka amma abunda nakeso da kai kabar maganar NUSAIBA ahanuna tabbas ni nasan abunyi"
"Cikin ladabi ABUDULJABBAR yace Shikenan daddy nabar komai ahanunka domin gobe da Asuba nakeson barin qasar nan"
"To ABUDULJABBAR wata qasa zaka tafine haka?"
"Daddy Italy zankoma"
"Shikenan ABUDULJABBAR amma karka dad'e karka wuce shekara daya iya wuya ko dad'i"
"To daddy na kayimin addu'a domin ina buqatar addu'arka"
"Ba komai d'ana addu'akam kullum cikin yinta mukeyi"
Haka de ABUDULJABBAR da Daddy suka gama tautauna warsu ABUDULJABBAR ya tashi ya fita harabar gidan inda yasallami Escort d'insa da maqudan kud'ad'e ya sheda musu tafiya zaiyi kuma zai dad'e sbd haka ko wanne yaje ya sallameshi inkuma yadawo inyana da buqatarsu zai nemesu, sosai Escorts d'in sukaji ba dad'i domin susan megidansu mutum ne adali haka de ya sallamesu dukka ma'aikatan gidan megadi kawai ya bari da mebawa filawowi ruwa, amma hatta mai wanki da guga ABUDULJABBAR ya sallamesu haka ma mai yiwa FINAH girki shima yaqara gaba, daga nan kuwa ma'aikatarsu ya wuce ya sallemesu akan zai qaro ilimi suma basu ji dadin hakanba amma ya suka iya tinda neman ilimi zaije dan haka suka masa fatan Alheri da kuma albishirin duk lokacin da inyadawo in yana son aiki tare dasu to qofa abud'e take yadawo bakin aikinsa kawai.
Daga nan office d'in dr Musa ya wuce
Inda ya sallami dr Musa akan zai tafi Italy ne qaro karatu, dr Musa baide so tafiyar abokinasa ba kuma Amininsa amma ba yanda ya iya tinda duk harkar qaruwa ce, dan haka sukayi sallama cikin kewar juna.
Shiko ABUDULJABBAR bai tashi dawowa gida ba yau sai misalin goman dare domin ya biya airport ya gama duk abunda zaiyi jirginsu qarfe ukun dare zai tashi zuwa Italy, ko da ya shigo parlour tsit ya samu parlour ba kowa yasan yau kowa ransa a 'bace yake agidan, dan haka sid'ik-sid'ik ya shige d'akin IKIRAM, ahankali ya bud'e qofar ya shiga yarufe ya murd'a key, hangosu yayi suna bacci cikin blanket d'aya domin basu ma kashe wutar d'akin ba, ahankali yaje yayaye blanket d'in 'YAR AMANA yafara gani tana bacci cikin wahala dan numfashinta ma daqar yake futa, jikinta kuwa da fuskarta duk yayi ja sbd duka da tasha rasa me zaiyi ma kawai sai ya tofesu da addu'a, ya jawo jakar makarantar IKIRAM ya yagi paper ya d'au biro ya fara rubutu kamar haka
*IKIRAM My Sister ina so ki kula da rayuwar Nusaiba kamar taki ayanzu haka jikinta da zaza'bi da asuba idan kuntashi kibata tea mai zafi tasha tare da maganin ciwon jiki sanan ki tabbatar bata zama da yunwa haka kuma karatunta ki ringa koya mata duk abunda bata ganeba ta 'bangaren addini da kuma boko domin zaki samu lada nasan kuma zaki iya qanwata IKIRAM Allah yayi wa rayuwarku Albarka ki sani Nusaiba amana ce ahanunmu inkinkula da ita tamkar dani yayanki ABUDULJABBAR kika kula!*
Yana gama rubutawa ya ajiye jakar akan bed side drawer d'in gadon, sanan ya ajiye paper d'in akan jakar ya d'aura biron akan paper d'in sanan ya kashe musu hasken d'akin ya kunna musu dumb light, ya fice d'akin kai tsaye d'akin sa ya nufa ko kallon d'akin FINAH baiyi ba, ya shige d'akinsa ya had'a duk wani abu da yake buqata sanan ya d'auki paper da biro ya fara rubutu kamar haka
*My dear Mummy dan Allah ki yafemin*
*laifukana domin zanyi nisa daku ne na d'an wani lokaci, kamar yanda kika nemi inmayar da Nafisa d'akinta na maidata saide ayanzu zanyi nisa daku idan Nafisa taga baza ta iya ci gaba da zama dani ba to asanarmin domin ashirye nake na suwaq mata, kiyi haquri Mum Allah ya huci zuciyarki Bissalam!*
Yana gama rubutawa ya tashi ya nufi d'akin Mum ya bud'e ahankali ya shiga ya sameta tana baccinta hankali kwance akan gadonta tsaya wa yayi yana kallonta azuciyarsa kuma yana cewa " ina sonki Mummy na amma dole Zanyi nesa domin inbaha kaba son da kikewa FINAH sai yasa wata rana kin tsinemin amma yanzu inayi nesa dake daga ke har FINAH tabbas zakuga amfani na"
Ajiye paper yayi a qarqashin pilon Mum sanan ya fice a d'akin yana waiwayan Mum d'intasa
Kai tsaye d'akin Shi ya koma yayi wanka tare da alwala ya sanja kaya yaita nafiloli da karatun AlQur'an, da kuma neman gafarar Allah, har biyu da rabi tayi, sanan yatashi ya d'au jakar kayansa ya kulle d'akin ya nufi d'akin daddy, bubugawa daddy qofa yayi, shima daddy lokacin yana lazimi yagama nafilolinsa tasowa daddy yayi yace " waye ne"?
"Nine ABUDULJABBAR"
Da sauri daddy ya bud'e qofar yace " Abudul Lafiya?"
"Lafiya daddy na tafiyarce tazo domin jirginmu qarfe uku zai tashi"
Take daddy yaji jikinsa yayi sanyi sanan yace "to ina bari nazo inrakaka"
Shiga cikin d'aki daddy yayi ya d'auko key d'in mota yace " muje Abdul'
Haka suka fito harabar gidan ba kowa sai megadi, ABUDULJABBAR yace " Daddy dama nasani ai da bansalami driver ba"
"A'a ABUDULJABBAR gwanda daka sallami kowa dama ai driver d'in Mumynka da Matarka kawai yakewa aiki kaga yanzu duk inda zasu sa ita Nafisar ta kaisu tinda ta iya"
"Hakane daddy" ABUDULJABBAR yace.
Sai da sukayi tafiya mai d'an nisa daddy ya ciro Atm card, guda biyu a Aljihunsa yamiqawa ABUDULJABBAR yace " gashi ABUDULJABBAR kariqe wa'yanan Atm card d'in dukkansu Akwai kud'i acikin su fin d'insu kuwa shine .......
"A'a daddy kabarshi dan wlh bazan kar'baba ni ina da kud'i kuma idan naje ba zama zanyi yiba bayan karatuma zanemi aikin yi"
"A'a ABUDULJABBAR kasani fa rayuwar waje Akwai tsada" Eh nasani daddy nauyin da nabarka da shima na matana biyu da kuma mahaifiyata da qanwata yayi yawa ta yaya zansake kar'ban abu ahanunka?"
"Haba ABUDULJABBAR nifa mahaifinka ne kaine d'ana dakafi soyuwa araina zanmaka koma menene sbd biyayarka ageremu sbd haka ka kar'ba nauyin iyalinka kuma zan iya koda kuwa sunfi haka yawa"
"A'a daddy nagode Abar zancen kawai Allah yaqara maka lafiya da girma"
"Amin my lovely Son"
Da haka suka iso airport d'in inda daddy yaitayiwa ABUDULJABBAR fad'a akan ya kula da mitincinsa kuma kar ya wuce shekara d'aya, har akafara kiran sunayen fasinjoji masu tafiya zuwa Italy, nan daddy da d'anasa suka rungumi juna suna kwalla danji sukeyi kamar basu ta'ba rabuwa ba.
Daddy baibat airport d'in ba harsai da jirgin su ABUDULJABBAR ya tashi zuwa Italy.
__________________________
Da Asuba kuwa IKIRAM ce tafara tashi tinda tasaba da tashin Asuba domin kullum Yayanta ABUDULJABBAR shi yake tashinta dan haka tana tashi tashige bayi tayi wanka tare da Alwala yunufon d'in school tasa ta d'aura zani akai tayi Sallah tana azakar ne tahango paper d'in da ABUDULJABBAR ya ajiyemata bayan tagama tatashi ta d'au paper d'in ta duba ko tamiye dan ita asaninta ba ta ajiye paper ba, warewa tayi takaranta tas jefar da paper d'in tayi Sanan tafara cewa " waiyo yaya ABUDULJABBAR ina kuma zakaje? Allah de yasa ba qasar nan zaka bari ba sbd abunda Mum tayimaka?Shikenan yaya na insha Allah zankula da Nusaiba tamkar kaina ko kuma kai"
Bayi tashiga ta had'a ruwan d'umi ta dawo tatashi 'YAR AMANA taraka ta bayin tayi wanka sanan tafita kitchen ta had'o mata tea mai kauri da zafi ta d'auko mata magani tazo ta bata tasha, sanan zuwa wayewar gari 'YAR AMANA tayi Sallah ta koma bacci, itako IKIRAM tasan intatafi tabar 'YAR AMANA zata iya dawowa ta samu Mum da Anti FINAH sun kasheta dan haka tahad'awa 'YAR AMANA tea da yawa acikin flask ta ajiyemata da bread, ta d'auki d'ari biyar acikin irin kud'in da ABUDULJABBAR yake bata taje tagaida daddy kotakan Mum bata biba tawuce school ita da Daddy ya ajiye ta kuma yabata kud'i takar'ba tayi godiya tashige cikin makarantar. Shima Daddy ya wuce kasuwa abunsa.
Mum da FINAH kuwa basu tashi fitowa ba sai qarfe goma, a tunansu za su sami abin kari anjere musu akan teble kamar yanda ake musu safe da rana da dare, sai de me suna fitowa suka wayam dama Mum ce tafara fitowa sanan FINAH itama tafito ko gaisar da Mum batayi ba taja kujerar dining ta zauna, kallon Mum dake tsaye tayi tace " Mum ya kike ne?"
"Lafiya my FINAH kintashi lafiya?"
"Lafiya lau sai de rashin Abdul"
"Karki damu yana fushi ne amma zai sauqo ai"
"To wai shi wanan d'an iskan kuku me yake nufine da haryanzu banga komai ba?"
Mum kuwa cewa t"ayi Allah yasa de lafiya tinda baita'ba let haka ba"
"Habu kuku! Habu kuku!!!!!!!
FINAH ta kwallawa kuku qira amma taji shiru dan haka tatashi taleqa kitchen nanma taga wayam tsakar gidan taleqa bata kowa ba sai megadi dan haka ta yafito shi da hannu da saurinsa dattijon yazo ya d'an duqa yace " gani Hajiya"
"Ina ma'aikatan gidan nan banga kowa ba?"
"Ai Hajiya jiya dukka ya la'bai ya Sallamesu ni kawai dame kula da shukane muka saura"
"What?" FINAH tace.
Mum ce tataho da sauri tace " lafiya menene?"
Nan Megadi ya maimaita mata abunda yacewa FINAH, salati Mum tashiga yi da salallami tace " oho haka ABUDULJABBAR zaiyi mana to zaizo yasaneni zesan dani yake zancen, karki damu FINAH ai dolensa yadawo dasu amma yanzu kije ko kwaine ki soyomana tare da ruwan tea"
"Haba Mum nifa gaskiya ba abunda na iya kuma kema kinsani domin kuwa a gidan mu bana wahala in bazaki shiga kiyi mana ba zan qira waya akawomin abinci daga gida"
"Haba FINAH ai wanan qaranta ne kuma to je ki zauna bara nashiga kitchen d'in"
"Aha yauwa Mum shi yasa nakejinki domin kuwa babu uwar miji i mai saiqin kai rintawa"
Har Mum tashiga tafito tace " ko intaso maiyar can tayi manane"?
Cikin tsawa FINAH tace " wlh banci saide ke kici haka kawai kalan alasheni ta sauri"
"Kuma haka nefa" MUM tace.
Haka Mum tahad'o musu break fast Suka ci, Sanan Mum tatashi taleqo taga daddy baya gidan nan tazo tafad'awa FINAH akan suje su taso Maiyarcen su koreta agidan, ai kuwa suka nufi d'akin IKIRAM suka tai buga qofar cikin bacci 'YAR AMANA taji ana bugun qofa ana zaginta akan sai tabar gidan ita de tashi tayi taraku'be jikin bango tana kuka.
Har Mum da FINAH suka gama masifarsu suka haqura domin bata da niyar bud'ewa gashi kuma qofar akulle take, itako 'YAR AMANA haka taita kuka har IKIRAM tadawo lokacin qarfe daya, sanan ta sanarwa IKIRAM duk abunda yafaru, IKIRAM tace. "Ai nasan hakan zata faru shi yasa na rufeki, bayan sunyi Sallah shayi suka sha inda IKIRAM tatafi isilamiyarsu tare da 'YAR AMANA tamata rijista acewarta Daddyn ta da yayanta sunyi tafiya,
Da rana ma kuwa Mum ce taqara yi musu girki sukaci ita da FINAH, da yamma kuwa Ana tashi daga Isilamiya IKIRAM tatare mai nepap suka je restaurant d'in da wataran ABUDULJABBAR yake kaita tayi musu oder leda biyu ta biya da kud'in da Daddy ya bata suna dawowa gida suka shige d'aki suka kulle bugun duniyarnan Mum da FINAH sunyi amma IKIRAM tama sa headphone akunenta ita da 'YAR AMANA dan karma taji me suke cewa washe gari kuwa Daddy yakaisu school tare da 'YAR AMANA aka mata rijista inda aka ajiyeta a primary 4 sbd girmanta ita kuma IKIRAM a 6 take, kuma Daddy ya d'auka ma 'YAR AMANA memata lesson da ban a school d'in inda in antashi zaina koya mata turanci da kuma sanin baqaqe.
Haka yauma da suka dawo suka siyo abincinsu awaje suka kulle kansu.
Mum saida tace idan IKIRAM batasantaba bud'e qofar ba saita tsine mata sanan IKIRAM ta bud'e MUM da FINAH suka shiga sukayiwa 'YAR AMANA shegen dukka sukace saitabar gidan, ai kuwa IKIRAM tace " wlh Mum inkuka koreta nima saina bar gidan domin Amanarta yaya yabani nan fa MUM ta han'bare IKIRAM tajawo 'YAR AMANA fuuuuh, ai kuwa sukayi kici'bis da Daddy nan tasaki hanun 'YAR AMANA tashige d'akinta ta kulle itama FINAH tahaye sama abunta domin kuwa yanzu daddy bai kula Mum ko girkinta bayaci kuma kwana biyu kenan basuga ABUDULJABBAR ba ita da FINAH amma bawanda ya nemeshi
Daddy kuwa qofa yayi yabawa 'YAR AMANA da IKIRAM haquri yace " kuyi haquri yarana daga gobe juma'a Insha Allah matsalarku taqare"
Yashige 'bangaren sa abunsa.
Washe gari kuwa juma'a koda daddy yakai su 'YAR AMANA school sai ya bawa IKIRAM kud'i yace " idan antashi kuwuce gidan Aminina Alhaji Usman dala, zanbiyoina d'auke ku inma kuma banzoba karde kutaho kujirani.
Nan suka masa Sallama suka shige cikin school d'in
Da yamma kuwa Mum da FINAH suna zaune suna hira kawai sai sukaji ana gud'a ana shigowa da kaya d'ayan side d'in dake gidan a kulle, a guje Mum da FINAH suka fita harabar gidan yayinda da yayi dai dai da anshigo da Amaryar cikin shiga ta alfarma, Mum ce tashiga gabansu tace " kai ku dakata yaushe ABUDULJABBAR yayi aure bai fad'a minba?"
Acikin matan wata tayi kud'a tace " ai Hajiya Mijinkine Alhaji Ashiru Maina yayi aure ba d'ansa ba..................
To pans kunjifa wai daddy yayi aure lalle akwai gwarama🤣🤣🤣
hhmm muje de zuwa dan yanzu wasan zai fara
Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere asauran groups please
*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*🤲
No comments