SHINE SILAH 31-35
*PAGE* 31-35
.........................📖Ganin yadda Mami ta hade girar sama data 'kasa yasa duk suka shiga taitayinsu Najma ce ta duk'a har 'kasa tace "Mami ina wuni" harara ta watsa ta tace "ke ba'kar muna fuka da 'dana nakeso nayi magana ba dake shasha ba kitashi ki bamu guri tunda ba uwar wani ta haifa munshiba" jikin Najma har rawa yake ta mik'e tashige 'daki Najib ya bita da kalo Mami ta watsa mata harara tace "to mijin tace kadawo daga raka Hajiya unguwa tun 1:00pm nake jiranka mijin Hajiya sai yanzu
6:35pm kadawo ko nace kadawo da hajiyar taka to bara kaji nagaji da iskancin da kuke mun Najib nazubama Ido naga iya gudin ruwanka amma naga ko ajikin ka to mu dangi mu ba dangin rashin haihuwa bane dolene ka 'kara aure dan haka na tsaida bikin ka da Khairat nan da 2weeks" da sauri ya 'dago ya kaleta ta watsa masa harara tace "ba shawarar ka nazo ne maba kuma wallahi kace zaka bijirewa umar nina to cikin uku za'ayi daya ko ka auri Khairat ko ka saki waccan juyar kona salamawa duniya kai" taja tsaki tamike a fusace tabar gidan.Sabuda tashin hankali Najib ko motsi yakasayi a gurin sai gumi da yaringa keto masa kota ina
Najma ce ta fito daga 'dakinta fuskarta wasai tazo ta zauna kusa dashi tace "naji duk yadda kukayi da Mami kayi hakuri kayi auren dan shine mafita kaga gana da riba biyu gana faran tawa iyayenka gana raya sunnar Manzon Allah S.A.W idan kuma ka bujire zaka tashi ba albarkar iyaye kuma baji dadin zama da wace kake soba" kalonta yayi cike da kauna yace "Najma ba wannan ne damuwa taba kinsan halin Khairat ba kamun kai gare taba yanzu ace ita zan aura" kaita gyada masa tace "shine babbar abun farinciki a gurinka dan Manzon Allah s.a.w yace duk namijin da yaje ya aure karuwa a bariki ya zamo silar shiryiwarta to ladansa yafi duniya da abunda ke cikinta dan haka ka daina sa wannan damuwar a ranka"
Ajiyar zuciya ya sauke yace "nagode da tuna tarwa amma yanzu idan Khairat ta haihu ke baki haihu ba fa? kinsan akwai matsala babba" murmushin yake tayi tace "nima Allah zai bani kan lokacin tunda ancire In plan din tun watan da ya huce" "Allah yasa" "ameen yanzu katashi muje kayi wanka kaci abunci" mikewa yayi suka shiga 'dakin
Bayan yashiga toilet Najma ta fito parlour tasha kukanta tana nadamar biyewa Najib ya hanata haihuwa gashi yanzu shi zaiyi aure ya haihu ya barta duk da SHINE SILAH duk abunda ya faru" saida tayi mai isarta sannan ta shiga bathroom din cikin parlour ta wanke fuskarta ta gyada kalabinta takoma 'dakin lokacin harya fito ya shiya suka fito parlour ta zubo musu abincin suka ci tare cikin nunawa juna kulawa.
Bayan kwana biyu
Kulum sai Mami tazo gidan na amshi kudi masu yawa a gurin Najib wai na lefe tunda a banza yaiwa 'yar matsiyata bare tasu 'yar dangi
Itadai Najma nata ido ne ko 'kala bata cewa
Bikin nata matso wa kusan kulum sai Khairat tazo da masari gidan idan Najib yafita suta shewa suna kuna kida wai gida yariga yazama nata ita kuwa Najma duk sanda tagansu d'aki take shiga ta kule ta rabuda su suk'aci haukarsu kuma bata tab'a budar baki ta fad'awa Najib a cewarta yagani da idonsa
Yau saura 2days bikin tun yau 'yan uwan Khairat suka zo jere sai habai ci sukewa Najma itadai ba abunda takeyi sai murmushi ta kawo musu abunci wata daga cikin yayan Khairat ta turo mata kular tace "dauke tsiyarki ance miki mu mayin watane dazaki kawo mana wannan k'azan tar" yatsine fuska takusa da ita tayi tace "waya sanima ko wani asirin ta zubo mana ajiki" "aikuwa dai"
Wata ce tafito daga cikin dakin tace "haba Sa'adatu mene haka ina ruwanku da ita sabuda zubar da girma dame kuke so taji da masifar Hajiya ko ta kishiya da ake mata ko taku da kuka zo har gidan ta zaku mata rashin mutun ci banason irin wannan kubata hakuri yanzu" Safara'u da Sa'adatu kun kuni suka bawa Najma hakuri
Murmushi tayi tace bakomai Hajiya nagode daga haka tafice daga part din Khairat
Washe gari akayi Dinner tun safe batasa Najeeb a idon taba har 1:00am ta kwanta bacci bata san sanda yadawo ba
Haka washe gari kanta tashi yafice ko shirin 'daurin auren ba'a gidan yayi ba sai ita kadai tsuro ga Mami ta hana danginta zuwa bare su 'debe mata kewa
Haka ta wuni agidan tana kuka bame rarrashinta
7:30pm motocin kawo Amarya suka ringa shigowa ba'abunda kirjin Najma keyi sai bugawa da 'karfi bata san sanda sabon kuka ya kwace mata ba jin ana ihu ana tafi tamike a sanyaye ta lek'a ta window waro ido tayi ganin Najib ya bude motarsa ya fito da Khairat wace ko rufe fuskar Amare batayi ba kayan jikinsu iri daya mutane sai tafi suke musu ya rungumeta ajikinsa ya dauketa kamar jaririya yai cikin part din da ita dayake duk yarane masu rakiyar Amaryar suka hau ihu ana tafi
Ai Najma bata san sanda ta zube a gurin tasa kuka me sauti tana karanta "Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un Hasbunallahu wani'imar wakil" tana gurin a zaune har aka fara salar isha mikewa tayi ta dauro alwala tayi salah taringa addu'a tana kaiwa Uban gijin talikai kukanta
Sai 11:30pm Najib yashigo dakin nata tanajinsa taki kulasa ya zauna kusa da ita ya ajiye mata leda a gabanta yace "kiyi hakuri banmiki kayan fadar kishiya ba amma nasa miki kudi a account dinki" ajiyar zuciya tayi tace "to nagode Allah ya Sanya alkairi" "ameen kinmun addu'a sunake a daren yau nasamu Baby" 'dagowa tayi da sauri ta kaleshi ya kashe mata ido yamiki yace "ko zaki rakani?" Cikin b'acin rai Najma tace "...............!
COMMENT
AND
SHARE
by
*XAHRA*
No comments