Breaking News

YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 24-25

 *NUSAIBA*

   *'YAR AMANA*☘️☘️

*Page 24-25*

........ "Ai kuwa k'aryane ya zama dole wanan yarinyar tabar gudinan tinda bana ubanta bane" Nan Mum tayi kukan kura ta jawo 'YAR AMANA ta hau dukkanta kamar an aikota sai masifa takeyi tana cewa " wato da ubanki ke aka aiko domin aringa lashemin jinin jikoki ko? To wlh ahird'inku nafi qarfinku daga

ke har wanda suka aikoki" itako 'YAR AMANA sai ihu takeyi tana neman d'auki, IKIRAM kuka takeyi tana cewa " dan Allah Mum ki rabu da ita wlh Anti FINAH qarya takeyi NUSAIBA ba maiya bace 'yar uwarmu ce fa Mum tinda 'Yar qanin daddy ce"

Afusace Mum ta juyo ta wanke IKIRAM da mari, abun da bata ta'ba yiba arayuwarta wato dukkan  IKIRAM amma sai gashi yau tayi, wani gigicecen ihu IKIRAM tasa da dukka gidan sai da ya amsa domin ba ata'ba dukkanta ba arayuwarta koda kuwa amakaranta ne sai de cin zali irin na yarinta da tin tana yarinya a makaranta in wasu yaran sunyi mata shima bamai zafi ba, dan haka taji shigar marin da Mum taimata sosai ga hanun Mum da zafi kamar na qato.


Shi ko ABUDULJABBAR yana sa kayansa ya ringa jiyowa kamar ihu kuma da muryar NUSAIBA can kuma sai yaji ihun IKIRAM da ya amsa dukka gidan ai a sukwane ya sauqo daga sama zuwa parlour dake qasa,  da gudu ya qaraso ya kar'bi 'YAR AMANA ahanun Mum wanda lokacin 'YAR AMANA ko motsi bata iyawa sbd da dukkan da tasha, da sauri ya qwace 'YAR AMANA ahanun Mum ya nufi sama da ita, Mum ko sai masifa takeyi tana cewa " ina zaka kai min Mayya ABUDULJABBAR maza zo kafita da ita a gidan nan ka yasar atiti sauran shegun suzo su d'auka" shiko ABUDULJABBAR ko takanta baibiba kai tsaye d'akinsa ya shige ya kulle ya nufi bayi da NUSAIBA ruwan zafi ya had'a ya jefata ciki, bugun qofar Mum yajiyo tamkar zata 'balle d'akin tana masifa, dolensa yaje ya bud'e qofar yaja ya tsaya ajikin qofar Mum kuwa cikin masifa tace " ka matsamin inshiga infito da maiyarcan dan wlh basu isa sukuma cimin jikoki ba"


"Haba Mum waye kuma maiyya?"

"Waccar yarinyar ma na da daka d'auka maza fito da ita tabar gidan nan yanzu nan"

"Wa yace miki maiyya ce? Daddy ne fa ya kawota daga qauye 'yar d'an uwansa ne"

"To ina ruwa na nide na fad'a maka kafito da ita ko kabani hanya in wuce infito da ita da kaina"

"Haba Mum wa yace miki haka ne?

"Gatanan" tafad'a tana nuna FINAH da take bayanta. "Dan kuwa Malamin Mum d'inta ne yace duk cikin da FINAH take samu su suke cinya su dangin daddyn ka dake qauye shine yanzuma suka turo wanan aljanar yarinyar sund'auka kwanciyar da FINAH tayi a asibiti ciki ne"

IKIRAM ce tahayo saman da gudu tana cewa" wlh Yaya karka yarda qarya ne Anti FINAH tayiwa Mum NUSAIBA ba maiya bace.


Shiko ABUDULJABBAR wani mugun kallo ya wullawa FINAH sanan yace "ke Nafisa lalle kincika munafuka ni nasan baqin kishinki koma miye zaki iya kuma wlh NUSAIBA baza tabar gidan nan ba saide ke kibarshi" ai kafin ya ankara Mum ta wankeshi da mari cikin masifa tace " ashe baka da hankali da har kake fifita maiya akan 'yata FINAH 'yar asali 'yar gata"

Shima ABUDULJABBAR hanunsa ya d'aga ya wankawa FINAH mari cikin 'bacin rai yace munafuka burinki ya biya kullum baki da aiki sai de kiringa had'ani da uwata, ai kafin ya kuma ankara Mum ta sake yarfamar wani marin sanan cikin masifa tace " naramawa FINAH marin da kayi mata domin akai na ya kamata karama qaramin marar kunya"

Kallon Mum ABUDULJABBAR yayi yace " bawanda yake cinye miki jikoki ita Nafisa ita take amfani da maganin hana d'aukar ciki dan kar ta haihu domin kuwa dr Musa yasanar dani komi"

Cikin masifa Mum tace " au sharri zakayi mata sbd baka sonta ka tsaneta to bara kaji daga kai har dr Musa sai naci mutuncinku"

Cikin takaici ABUDULJABBAR ya shige dakinsa ya banko musu qofa, cikin masifa Mum tace " wlh kafito da yarinyar nan ko ranka ya 'baci". FINAH kuwa wani irin ihu tasa tace " Mum kina gani ko Mum ya shige d'aki daya da maiya qila ma aljanace Shikenan Mum" shi ko ABUDULJABBAR tsayawa yayi abakin qofar yace "Nafisa ki tafi gidan ku na sakeki saki daya"

Cikin masifa Mum tabuga qofar tace " wlh bata saku ba nafad'a maka ko kajanye sakinan ko namaka Allah ya isa"

Kama hanun FINAH Mum tayi fuuu sukabar wajen itako FINAH sai wawayen qofar takeyi zuciarta na ta fasa.


Shiko ABUDULJABBAR gurin 'YAR AMANA ya koma ya cirota a ruwan jikinta kuwa sai karkarwa yakeyi sbd da zaza'bi da yarufeta runtse idonsa yayi yacire mata kayan jikinta wata jallabiyarsa dama ta d'an d'igilemar ya samata sanan yabata panadol extra tasha kwanciya tayi a tsakiyar makeken gadonasa ya rufeta da blanket ai kuwa baccin wahala yayi gaba da ita.



Ita ko FINAH suna sauqa qasa cikin fishi ta nufi d'akinta sai gata janye da ajwatinta da sauri Mum tatareta tace " ina zakije FINAH?"

"Gidanmu zantafi Mum ai kina yaji ya sakeni"

"Amma ai kinji abunda nacemar kuma nasan dole ne zai mayar dake mudin yana son albarkata ke yama maidaki d'akinki domin ni nasan ABUDULJABBAR d'ane mai biyayya" 

"Shikenan Mum, amma gaskiya bazan iya jure ganin mijina da wata maiyyar yarinya ba suna cikin d'aki daya dolene intafi gidan mu in maiyar tatafi na dawo kodan tsira da lafiya" FINAH ta qarasa maganar tana kuka.

Mum kuwa cewa tayi " kiyi shiru nasan me zanyi yanzunan"

IKIRAM kuwa najin haka ta nufi d'akin Mum da gudu ta d'auki wayar Mum ta qira daddy.


ABUDULJABBAR kuwa zaune yake abakin gadon sa wanda 'YAR AMANA ke kai tallafa kansa yayi da hanayensa yana kuka tamkar qaramin yaro yana cewa " wai ni wata irin uwace wanan dani da tafison farin cikin matar da ta auramin fiye dani ta tauyemin haqqoqina da dama akan Nafisa kullum tafi so taganta cikin farin ciki sa'banin ni, amma ba damuwa nasan me zanyi tabbas, zanbar qasar nan ya zama dole inbar qasar nan nayi nisa da Mum d'ina da kuma FINAH qila idan ina da AMFANI agaresu zasu gani tinda MUM taqi yarda in rabu da FINAH in auri Za'bina"

Zuciyarsa ce tatambayeshi wacece "Za'binaka?" 

"Duk da nasan ayanzu bani da Za'bina tabbas zata zo agaba domin NUSAIBA bama sauwaqa mata zanyi inta girma ta auri wanda takeso bazan bar qasar nan da aurenta a akaina ba"

Yana cikin wanan tunanin yaji bugun qofar Mum tana cewa "kafito da Yarinyar nan ko intsine maka yanzunan" cikin fargaba da tashin hankali ya tashi ya bud'e qofar Mum yagani tsaye FINAH na bayanta da sauri Mum ta bankeshi ta shige ciki, tafara dube duben inappropriate zata hangon yarinyar, ai ita ma FINAH rufawa MUM baya tayi ai kuwa suka hango FINAH kwance tsakiyar gadon tana miqa da sauri FINAH tayi kan gadon aikuwa ta hau kan 'YAR AMANA ta jawota ta buga ta da qasa, wani ihun azaba 'YAR AMANA tasaki, nan FINAH tahau jibgarta kamar an aikota, Aikuwa ABUDULJABBAR baisan sanda zuciya ta ciyo shiba yazo ya kwarfe FINAH agurin tafad'i qasa shima ya hau jibgarta MUM kuwa sai ihu takeyi wai ABUDULJABBAR zaiyi kisa, aguje daddy da IKIRAM suka shigo d'akin, cikin qaraji daddy yace ABUDULJABBAR!!!!!!!!!!!!!

Cak ABUDULJABBAR ya d'ago ya tsaya idonsa ne ya cika da kwalla yana kuka tamkar mace yabud'e baki zaiyi magana.

Daddy ya d'aga masa hannu yace " karka ce komai domin IKIRAM tasanar dani komai tabbas ka kyauta daka ramawa 'YAR AMANA dukkanta"

Cikin masifa da wahala FINAH tace " daddy kaduba fa ad'akin mijina na sameta kuma kayansa ne ajikinta wlh sai na hallaka yarinyar nan"

Cikin fad'a daddy yace " yimin shiru mutumiyar banza keda surukarki to wlh bara kuji kunkawoni maqura tabbas zanyanke mumunan hukunci akanku ke  Murjanatu na yanke igiyar aure na daya akanki, sbd haka kaima ABUDULJABBAR kasaki wanan yarinyar domin kuwa kana da matar da tafita komai"

Cikin masifa Mum tace " wlh qaryane bansaku ba kuma wlh muddin ya saki FINAH sai na tsinemar domin ina sonta shi yasa na auramasa ita kuma da kake cewa yana da mata wata tsinaniyarce matarsa?"

Cikin masifa Daddy yace " zaki sani Murjanatu kiban lokaci zakiga abunda zanyi zanuna miki ni Ashiru ba Mijin tace bane wlh"

Jan hanun d'ansa ABUDULJABBAR yayi sukabar d'akin itako IKIRAM kafad'ar 'YAR AMANA takama Suka fice ad'akin suka nufi d'akin IKIRAM 'YAR AMANA na d'ingisawa sbd uban dukkan da taci. Itako Mum tini jikin ta yayi sanyi sbd sakin da Daddy ya mata, amma ba damuwa tasan abunyi dan haka takama hanun FINAH sukabar gurin.


Daddy kuwa d'akinsa yakai ABUDULJABBAR ya zanar dashi ya kawo masa ruwan Swan mai sanyi yasha sanan Daddy ya shiga bashi haquri, kallon ABUDULJABBAR daddy yayi yace " Daddy na inaso inyi tafiya inbar qasar nan"

"Wata qasa zakaje ABUDULJABBAR kuma sbd me?"

"Inaso inyi nisa da Mum da FINAH ne koda na shekaru uku ne inba haka ba zasu kasheni kwana bai qareba"

"To amma ABUDULJABBAR ya maganar Aikin da kafara yi akan su Alhaji Halliru?

Daddy dole zanbarwa qungiyarmu wanan sauran aikin domin za su iya in kuma sun kasa inadawo zanci gaba domin dama inaso inqaro ilimi akan binkice"

"Shikenan d'ana bazan hana kaba domin farin cikinka shine nawa amma matarka fa tare zaku tafi ko? Ina nufin 'YAR AMANAR ka" 

A'a Daddy dama ina son in sauwaqa mata"

"Sbd me ABUDULJABBAR?"

"Daddy dolene in sauwa qa mata domin Mum baza tata'ba kar'barta ba amatsayin sirikarta sbd da FINAH, ya zama dole in saketa amma dan Allah Daddy inaso ta yi hakuri ta zauna anan har tayi karatu ni zan d'au nauyin karatunta, idan ragirma ta mallaki hankalinta sai tafitar da miji tayi aure, in kuma zuwa lokacin ahalinta su waiwayeta Shikenan kaga ko bakomai munsamu ladanta.......



Hhmmm kuna ganin daddy zai yarda da shawarar d'anasa kuwa?

Shinma su FINAH za su barta ta zauna a gidan har ta girma?


Hhhmmm muje zuwa wasa farin girki



Dan Allah in kinkaranta kiyi min shere asauran groups please




*ASSTAGAFIRILLAH WA A TUBU ILAIKA*🤲

No comments