YAR AMANA (NUSAIBA YAR AMANA) 22-23
*NUSAIBA 'YAR AMANA☘️☘️*
*Naji duk wani k'orafinku my really pans da kukeyi akan inringa post sau biyu arana.Amma dan Allah kuyi hak'uri abarshi a d'ayanma kunsan a bubuwanne sai a slow wlh ga aikin gida ga kuma na yara ga typing, ade barshi sau d'ayan hakanma kuma kunga ba kwa samun update kullum amma zanyi k'ok'ari insha Allah inringa muku post koda sau biyarne a sati😉😉*
*inkuma kunsamu kullum to! sau biyunma a rana wata rana zaku iya samu insha Allah mudin bana busy ina godiya masoya masu k'iran waya da masu turo sak'o ta pc duk ina godiya Allah yabar K'auna hak'ik'a littafin ya kar'bu agareku 100% Allah yasa ku k'aru da abun k'aruwar dake ciki ina muku fatan Alheri a duk inda kuke makaranta wanan littafin Mummyn Minal na muku SO because of God❤️🌹*
*Page 22-23*
____ Ita ko IKIRAM gurin 'YAR AMANA ta nufa ta d'agata suka fiskanki juna sanan ta tsare "NUSAIBA me yaya ABUDULJABBAR ya miki"
Shiru 'YAR AMANA tayi tana tuno irin jan kunan da ABUDULJABBAR ya mata akan inta fad'i abunda yai mata, dan haka sai tace "ba'abunda yayi min kawai de gashi na yayankemin wai yayi min yawa"
"To amma shine naganki akwance ak'irjinsa?"
"Eh kin tsayawa nayi ya yankemin gashi domin ina son abuna shine shi kuma ya kamani ya matsani ya yanka ga shina"
'YAR AMANA ta k'arasa maganar tana kuka.
IKIRAM kuwa bubuga kafad'arta tayi sanan tace "kiyi shiru NUSAIBA zan had'a shi da Daddy ina ruwansa da gashinki?"
"A'a IKIRAM karki fad'awa daddy domin bana so ayiwa Hamma fad'a"
"Sbd me?"
"Sbd karya zaneni dan ni tsoransa nakeji"
"Shikenan kidena kuka nafasa fad'awa daddyn amma to shi Ya ABUDULJABBAR ina ruwansa da gashinki ko haushi yakeji kinfi matarsa Anti FINAH gashi domin itafa har k'ari takeyi da attachment, kuma Yaya ba ya so, amma de Shikenan muje in za'bamiki kayan da zakisa"
Gaban wadrop d'in kayan IKIRAM suka nufa inda IKIRAM ta bud'e durowar ta d'aukowa 'YAR AMANA wani Swiss less, Brown colour d'inkin riga da siket fitet, 'YAR AMANA na cikin sa kayanne sukaji tsayuwar mota da gudu IKIRAM ta fita tana cewa "NUSAIBA ga su Mum sundawo inkingama ki sameni a parlour".
Da gudu IKIRAM ta fita harabar gidan lokacin Mum ta fito daga mota kenan rungume Mum IKIRAM tayi tana cewa "oyoyo Mummy na nayi kewarki sosai"
"Ayya autata ai gani na dawo antinki ta samu sauk'i" kallon gurin da FINAH take IKIRAM tayi, kawar da kai FINAH tayi tana wani yatsina sai kace mejuna biyu, itama IKIRAM hanun Mum tarike suka shiga cikin main parlour, ita ko IKIRAM sai waige takeyi taga ta ina ABUDULJABBAR zaizo tar'barta amma bata ganshiba harda daddy yazo ya wuceta ya shige ciki, itama ciki ta shige zuciyarta nayi mata zafi dukkansu a parlour Suka ya da zango inda ma'aikatan gidan maza suke ta kawo musu kayan ciye-ciye, shiko daddy sbd takaici 'bangarensa ya nufa domin ya tsani ganin ma'aikata mazanan, gashi FINAH ta hana akawo 'yan aiki mata sbd kishin tsiya da yayi mata yawa dan ko tsohuwa tak'i abari akawo afad'arta wai kar wataran tsohuwa ta shigo musu da jikarta ko 'Yarta azo ana kalle mata miji.
Sosai FINAH ta k'ula na rashin ganin mijinata yazo mata tarba, dan haka tak'i cin komai, itako Mum da IKIRAM sai hirarsu sukeyi.
Shiko ABUDULJABBAR yana can ad'akinsa abun duniya yayi masa zafi zaune yake abakin gadon sa duk hankalinsa atashe domin tabbas yana buqatar mace, yadad'e be ke'be da matarsa ba yasande shi ba dutsi bane ba kuma icce bane dolene wata rana zaiji sha'awa, wanan dalilinema haryasa ya kusa afkawa NUSAIBA amma shi ya zaiyine Allah ya had'ashi da shedaniyar mata, tabbas auren FINAH qadararsa ne, domin kuwa tun a asibiti da dr Musa yayi masa bayani akan aika aikan da FINAH take masa na shan qwayar hana ciki yaji ya tsaneta kuma tabbas bazai qara had'a jiki da itaba domin kuwa bazai iya asarar jikinsa ba da lokacin taba akan ta tinda ita tace ita tinkiyace"
Kuka ABUDULJABBAR yakeyi sbd idan hawayen ya zubomasa zaifi jin dad'i, aransa kuwa cewa yakeyi " kayi haquri daddy naje namamile yarinyar dana maka alqawarin ba yanzu zanta'bata ba, amma nakasa jure hakan gashi zan jawowa kaina raini awajen qaramar yarinya tabbas ni bana son yarinyar nan kawai tausayinta ne yasani na yarda da aurenta amma nayiwa kaina alqawari mudin inta girma ta samu wanda takeso zan sauwaqa mata, dan haka kiyi haquri 'YAR AMANA ta nariga wani da yadace da zama mijinki ta'ba jikinki amma haka ya farune ta sanadin mahaifiyata da ta za'bin macen da bata dace dani ba, harna kasa ga zawa nake neman in'bata rayuwar yarinyar da take 'YAR AMANA ce ahanuna"
Kuka sosai Mai qona zuciya ABUDULJABBAR yayi domin shi kam jinsa yakeyi tamkar bai cika mutum ba sbd rashin mace tagari amma gashi awaje ana masa kallon nagartaccen maigida.
Da yaga de kukan ba zai kaishiba kawai sai ya shige bayi ya sakarwa kansa ruwa.
A parlour kuwa Mum da FINAH suna zaune da IKIRAM sai ga 'YAR AMANA ta fito sanye da kayanda ke jikinta da kuma kwaliyarta da ta kwa'ba, ga gashinta ya bazu ko ina agadon bayanta domin bata d'aure shi da tsimma ba kamar yanda takeyi ba arugarsu, d'an kwalin kayan kuwa tama kasa d'aurashi dan haka sai ta sashi akanta ta saqaloshi ta wuyanta irin yanda 'yan qauye sukeyi, parlour ta nufo gabanta na fad'uwa domin batasan wasu irin mutane bane kuma su Mummy.
Tana fitowa parlour d'in sukayi ido biyu da FINAH ihu FINAH tasa tana cewa "waiyo Allah Mum wayece wanan?" Tashige jikin Mum.
'Dagowa kai Mum tayi ai kuwa tai ido biyu da 'YAR AMANA, "wa inahu sulaimanu wa inahu Bissimillahi rahamanir rahim. Kefe mutum ce ko aljan?"
Mummy tace cikin tsoro, itako 'YAR AMANA dake tsaye mamakine ya kamata wai ita ake tambaya mutumce ko Aljan ta ina to tayi kama dasu? Zuciyarta kuwa ce mata tayi aikema haka kika d'aukesu kafin ki gane su waye su😃
IKIRAM kuwa me zatayi inbanda dariya harda rik'e ciki, itako 'YAR AMANA quri tayi tana kallon Mum, cikin masifa Mum tace " dena kallona dan ubanki imma ke maiyace wlh nafi qarfinki haka ahalina ma, sbd haka ki koma ki gaya wa wanda suka turoki kuruwata kur dani da ahalina"
Cikin dariya IKIRAM tace " Mum bafa maiyabace NUSAIBA ce"
Dukka takaiwa IKIRAM tace " NUSAIBA ubanki kina ganin idonta sak irin na mayu to wlh sai de taci kanta da wa 'yanda suka turutota amma ba niba, dama fa andad'e ana cewa a unguwar nan akwai mayu amma ban tabbatarba sai yau tinda gashi anbiyoni har gida"
Itako 'YAR AMANA sam batasan akan me Mum take mita ba domin kuwa batasan me KALMAR maita take nufi ba, tinda hausarma ba wani Sosa ta iya taba, dan haka tayi quri tana kallon Mum azuciyarta kuwa cewa takeyi "ashe su Gwaggo na da yawa"
Mum kuwa cikin masifa tace " ba zaki fita ba dan ubanki sai na shemeki"
Tashi IKIRAM tayi tace A'A Mum bafa maiya bace daddy ne ya kawota daga qauye kuma bari ya ABUDULJABBAR yazo ki tambayeshi"
Cikin Masifa FINAH tace "wlh qaryane Mum Maiyace dan Allah ki koreta danni ciki nama ya farayimin ciyo.
Ai kuwa mum tana tashi, sai ga Daddy ya sauqo yace " waye maiyar da naji kuna ambato?"
Mum ce ta nunamar saitin da 'YAR AMANA take atsaye tace " gatanan fitsarariya ta tsareni da idanu"
Kallon 'YAR AMANA daddy yayi yace " NUSAIBA zo nan" matsawa kusa da Daddy 'YAR AMANA Tayi ta tsaya cikin tsoro domin ita yanzu su Mum sunfara bata tsoro dan ta lura halin Gwaggo garesu.
Shiko Daddy cewa yayi ba maiya bace 'yata ce"
?"''Yarka" MUM ta tambayi daddy
"Kwarai kuwa 'YAR d'an uwa nane aqauye shine da naje, kuna asibiti na taho da ita domin karatu zatayi kuma anan gidan zata zauna"
"Wani gida? FINAH tatambaya
Daddy yace " wani gida kika ganta aciki?"
Cikin masifa da rashin kunya FINAH tatashi tace " A'a wlh da sake bade gidana ba kam domin a gidan nan ba wata 'ya mace bayan Mum da IKIRAM sai kuma 'Ya'yanda zan haifa"
"Cikin fad'a daddy yace " ai nan ba gidan mijinki bane gida nane na gina shi da gumina sbd haka ina da ikon da zankawo wanda nakeso ya zauna idan kinga baza ki iya ba sai kifita ki koma wanda mijinki ya gina amma NUSAIBA kam anan zata zauna"
Daddy yana gama fad'an haka ya fice yabar gidan.
Kuka FINAH tasa tafad'a jikin Mum tana cewa " wlh MUM karki yadda ai dama kwanaki anfad'awa MUM d'ina wai Akwai mayu a dangin su Daddy kuma su suke cinye duk wani ciki da nasamu shi yasa kika ga haryanzu baki samu jika ba, kuma Malamin Mum d'ina yace mayun zasu iya biyomu har gida ko suyo aiken wanda za suna musu aiki"
Cikin tashin hankali MUM tace.......
Hhmm wai me ABUDULJABBAR yake nufine My pans bangane ba ? ku fahimtar dani domin magangununsa sunsani rud'u
Wai ina labarin Gwaggo ne?
Muje zuwa dan yanzu za'a soma kaftawa kude kubani had'in kai wajen yin comments dan yanzu labari zai soma zafi.
Dan Allah inkinkaranta kiyi min shere asauran groups Ngd👏
*Love you all my pans*💕💕
*ASSTAGAFIRILLAH, WA A TUBU ALAIKA*🤲
No comments