TSANGAYAR MALAM 23-24
2️⃣3️⃣-2️⃣4️⃣
A cikin soron gidan hakimi suka kwana gaba ɗayan su kowa hantar cikin sa a kaɗe dan ba ƙaramun razana sukayi ba har aka fara kiraye kirayen sallar asubahi sahun jamma'ah ya fara yawaita a hankali
suka zare sakatar ƙofar ɗaya bayan ɗaya kowa ya tsame jikin sa yayi gidan sa da muguwar fargaba a fal a ransu,ɗan malam ya tirƙi baccin sa har da munshari ya tashe yana hamma me haɗe da sallati chan ya hangi shayi da burodin sa har da madara da takardar ƙasai a gefe,murmushi yayi ya ce""Daɗi kashe ni,ashe dai su malam ba ƙara mun ƙauna ta ake ba kai ko a wannan zamanin da magaji ke wahala ai dole su malam a lallaɓani dan ko ada ban sami kulawar nan daga gareshu ba,kai idan ma ka ɗan yi nisan kiwo da tsofaffi aradu anfi ƙaunar ka ana nan nan da kai,idon sa ya dira akan buhun takalman su hakimi da ya jingine su a jikin tagar ɗakin sa ba shiri ɗan malam ya tintsire da dariya yana,"duk zaku kwashi kashin ku a hannu musamman wanchan me rawanin da babbar rigar umm bari inje in kwashi gaisuwa gun tsofaffi kai bari dai cikina ya fara ɗauka daga baya gaisuwar ta biyo baya,ɗan malam ya miƙe ya fita fitsari yaje ya wanko bakin sa ya dawo ɗakin ya janyo shayi da burodin sa da ƙosan sa ya hau sha yana ci yana dariya shi kaɗai har ya kammala ya janyo buhunsa ya fidda takalman gaba ɗaya duk yabi ya kwashe wari ɗai ɗai ya mai da a buhun sauran warin kuma ya tuttura su ƙasan katifar sa.
A zaune a tsakar gida ɗan malam ya iske uwaila na shan shayi da saure yai ƙasa haɗe da furta"
"inna barka da asubahi mun kwana lafiya.
uwaila ta juyo ɗauke da murmushi a fuskar ta da kofin shayin ta a hannu ta mai da masa da amsa"
barka Attahiru mun tashi ƙalau.
lafiya lau inna,"ina malam yake ne?
wai malam ai ya fita tun asubar fari ya je kwana tara aikin fidda waken sa.
kwana tara kuma inna naga gonar tashi na hayin kuka me ya kai malam kwana shida aikin gona.
ajiyar zuciya uwaila ta saki shi kuma ɗan malam yaja kujerar tsuguno yazo kusa da uwaila ya zauna yana kallonta kamar uwaila baza ta magantu ba chan dai ta ce.
"Tunda malam ƙasimu cinnaka ya ɗauke ka ya kaika almajiranta hakimi da ƴan tawagarsa suka sako malam a gaba da fitintinu kala kala,in ta ƙaice maka magana hakimi da kansa ya ƙwace gonar malam wai ta asalin kakan su ce ta gado.
Kutii..............,A'uzubillahi ya da zagi kuma Attahiru.
haba inna maganar taki ce gaba ɗaya taƙi ɗaukar kai na gonar malam ɗin ce ta kakan su hakimi tashin hankali wallahi bazata taɓa saɓuwa ba gaɗa a lahira sai kuma akayi me da me inna?
ai nayi shiru tunda fitina zaka je ka jajiɓo ka yaɓan ko ribar zanchan baka gama tsayawa kaji ba kake ƙoƙarin yanke hukunci ni kam nayi tsit bakina ƙanin ƙafata.
inna kenan duk wannan hargowar da kika ga ina yi fankan fayau ce ba wani abu zan iya taɓukawa ba dan nasan malam ma ba daɗi zai ji ba kuma bana son na ƙara yin nesa da ku me zai kai ni yin fitina sam lala lala inna kawai dai naji babu daɗi ne shiya sa.
haba yanzu naji batu, kasan malam baya son tashin hankali haka sidan ka je kayi wani abu kuma ace nina faɗa maka dan Allah attahiru karkayi komai akai maganar duk ta wuce kaji.
Ni na faɗa miki babu abinda zanyi sai addu'ah ai inna nafa kintsu wallahi haƙuri gare ni yanzu kamar ruwa sai ka dake ni ma ko kallonka ban yi ba saboda abubuwan da na gani na rayuwa a chan tsangaya suma kuma sun ga darasi kala kala ba kamar e malam na kan buzu.
Allah Attahiru ka ce ka hankaltu a chan tsangayar.
kaiiii inna ai ba ɗan kaɗan ba idan ana sallah ba'a magana,wai to ya aka ƙare cigaba da bani labari naji inda zanchan yaja birki.
Da suka kira malam sai suka bashi taƙardun sheda ya karanta har da shedar zir malam tala da malam ado da muttaƙa suka yiwa hakimi bayan yasa su bincika haka dai malam ya tashi ya barsu da Allah ba yanda ya iya ba a kwana biyu ba suka kuma ƙwace limanci daga hannun sa suka baiwa malam ƙasimu cinnaka naka.
Inna!
Na'am Attahiru.
Mutanan nan sam basu da tsoron Allah har da shedar takardu to takardun suna wajan waye yanzu?
Hakimi ai shine ya riƙe ya ce gonar gadonsu ce ta kakan sa.
Taɓɗijam to Allah ya sakawa malam ya bi masa kadinsa ai ba komai sa bashi a lahira idan kowa ya je.
Wallahi kuwa Attahiru ashe dai da gasken ka hankaltu faɗar Allah da haƙuri muraran a bakin ka Allah ya daɗo hankali da nutsuwa.
Amin amin inna ni ko askar nan taki tana kusa kinga wasu gemu ne ƙwara uku suke so wai lalai sai sun fito sun tsaya ni kuma wallahi ban shirya girma ba har yanzu ki ɗan ara mun na cire su na huta sun dame ni.
Dariya uwaila tayi ta dubi gemun ɗan malam ta ce"
ban hango su ba suna ta ina ne?
gashi nan,ɗan malam ya kamo silin gashi guda uku ya na"kin gan su ko inna su ala dole wai sai na tsaida sunnah ni kuma wallahi nace tukunna sai kun aurar dani.
Allah ya shirye ka kace kawai na aramaka aska attahiru ba sai ka haɗa da wayo da dabara ba.
to ara mun kawai inna a wuce wajan.
uwaila ta,tashi ta shiga ɗaki ta fito da askar a hannu miƙawa ɗan malam tayi da sauri yasa hannu ya warce har da yiwa uwaila godiya ya tashi ya koma ɗakin sa,leƙowa yayi yaga uwaila ta bar tsakar gidan wuf yayi waje ya fita bai tsaya a ko ina ba sai a shagon Baƙiru suka chafke hannuwa nan ɗan malam ya shiga labartawa baƙiru duk abinda ya wakan baƙiru ya jinjina lamarin shima ya sanar da ɗan malam dawowar su yadikko da baban nafi'u da Addar sa gida sun warke kamar basu taɓa ciwo ba daga busani suka shiga hirar yaushe gamo,sai kusan bayan isha'i ɗan malam ya shigo gida malam tun daya dawo bai gansa ba ya fita neman duniya bai sameshi ba dole sai da ya haƙura amma ransa a ɓace da fargabar lafiya Attahiru yake shi da uwaila,ɗan malam kam yasha faɗa daga ƙarshe malam ya ɓuge da nasiha kala kala ɗan malam ya baiwa malam haƙuri ya zauna ya kwashi girki ya tafi ɗakin kwanciyar sa ya kwanta ƙarfe goma sha ɗaya na dare ya farka ya sauya kaya yanzu farare tas ya saka ya shafa hoda fara da ya siyo a waje da bula ya haɗata da toka ya sharɓane fuskarsa da wuya da hannayen sa dukka har da ƙusunbin ƙwarya a bayan sa ya saka warin takalmin muttaƙa kafce ce dayake muttakan akwai lafiyar sahu manya manyan halitu gareshi kana hango ƴan yatsun ɗan malam gudul gudul a cikin ta kalmin ya fito daga cikin gidan da sanɗa.
Duk hanyar da ɗan malam yasan zai ci karo da mutane ya gujewa kai tsaye bayan gidan malam ƙasimu cinnaka ya nufa ya kama ƴar katangar ya ɗane kamar biri ya sauka ta ciki a hankali,ƙahon rago ya fidda daga jikinsa da zare baƙi a jiki nan da nan ya ɗaura akansa dai dai goshin sa ya fara jefa ƙafar yana lanƙwashewa haɗe da banƙarewa ladiyo da ta turo yaranta su zo yin fitsari sukayi kiciɓus da abu a babbanƙare ga fararan kaya harda mayafi fuskar sa rabi fara rabi bula bitsarin da basuyi ba kenan suka faɗa ɗakin malam ƙasimu dake kwasar girki ladiyo na masa fiffita a zaune.
""Kai kai lafiya dan gidan ku zaku faɗo mana kai tsaye"jikin yaran na rawa numfashin su na hauwa ya sauka suka haɗa baki"""
"Kaka rakiya ce da ƙaho a goshinta har da fararan kayan da aka sayo aka sa mata baba muma mutuwar zamuyi mun shiga uku zuwa tayi zata wuce da kai,sukayi sutuɓar baki zasu ce su suka ce kai.
Samma ko ƙassa ladiyo ta nemi malam ƙasimu cinnaka ta rasa sai kwanukan sa da ko rabin cin abincin bai yi ba tsabar firgicewa da ladiyo tayi ta nufi suf ɗin malam ƙasimu zata shige ciki chan taji ana"""
Ƙasa ƙasa da murya…………………………………
_*Comments/Share🤗*_
No comments