Breaking News

TSANGAYAR MALAM 11-12

 _*‍👳‍♂️👳‍♂️👳‍♂️TSANGAYAR👳‍♂️👳‍♂️👳‍♂️*_

                  _(Malam)_

                   *Na*

_Maman Dr_

             1️⃣1️⃣-1️⃣2️⃣

Bulala goma sha ɗaya aka tsulawa Basi likita ya gigice ya rikita gaba ɗaya wajan sai da ya ishi kowa da ihu ya kasa zaune ya kasa tsaye sai soshe soshen baya yake yana muskutawa gefe da gefe kamar tsutsa har aka iso da ɗan abu da Nafi'u suka nemi waje suka zauna a kan jan kafet yanda kowa ke zama,kamar yanda Hakimi ya tambayi ɗan malam a ɗazu yanzu ma haka ya sake umartar ɗan malam da ya faɗi abinda ya faɗa ɗazu,ɗan malam ya kwaɓe baki ya fara bayani tiryen tiryen daga fara jin ƙulin da ɗan malam ya ƙulawa miyar Yadiko Nafi'u ya saka kuka haɗe da tasowa a fusace ya shiƙi wuyan ɗan malam yana kai masa dukka shima ɗan malam ɗin ya shaƙi wuyan Nafi'u suka fara kokowa nan da nan waje ya haɗe ya kaure da hayaniya aka shiga kokawar raba tsakanin su.

Da ƙyar da siɗin goshi aka shiga tsakanin matasan biyu aka raba hakimi ya dubi ɗan malam rai a ɓace ya ce"


"Kai dai anyi taƙadirin yaro lalatacce mara ɗa'a,ka haddasa baƙin ciki da takaici a zuciyarsa dan ya shaƙi wuyan ka sai ka shaƙi nasa, yo ko karka zai yi a halin da yake ciki ai bazaka kalle shi ba ma bare ka tanka duk kai ka haɗa bala'in nan kuma wallahi sai na hukunta ka dai dai da abinda ka aika ta mutumin banza da wofi kawai.


'kamar ya ya na zuba ido ya nakas ta ni kake nufi ko me hakimi?


"idan ya nakas ta kan waya ya janyowa kansa?


'da kuwa bai ƙara gangancin riƙe mun wuya ba dama ai taurin kansa da shegen bakin sa yaja masa yanzu kuma gashi ya ƙara shiƙe ni,kai bazan ma haƙura ba Allah sai na rama.


"a gaban nawa kake faɗar sai ka rama ɗan marasa mutunci,hakimi ya mai da duban sa ga maɗam,,""malam kana ji ina faɗa yana faɗa ko.



"ranka shi daɗe hukunci na kawo shi ayi masa wuƙa da nama dukka suna hannun ka.


     "ma bada bulala a zannawa ɗan malam tsimagiya guda goma a bayan sa sai ka ƙara biyar a ƙafarsa huɗu su biyo baya a ƙeyarsa sai mu yanke hukuncin daya dace ayi masa.


    Zumbur ɗan malam ya miƙe a fusace ya ce"".


"Na rantse da Allah, ba ma bada bulala ba ko wayen waye ya taɓa lafiyar jiki na sai na rama idan kuma ana musu a taɓa ni aga kawai dan na yi shiru na zuba ido sai a ha'ince ni kai badan ma malam da kansa ne ya kawo ni ba akwai ɗan da ya isa duk cikin nan wajan ya kalle ni duk ba wanda ban san makwantar sa ba a dakeni a ga........kai Attahiru abun naka har ya kai ga manya na faɗa kana faɗa har da yiwa bayin Allah baraza na.



     "To ya ranka malam Ƙasimu cinnaka kake ko wa,ko kai zaka gwada idan kana musu.



Toooo lalai ka cika taƙadirin gaske to ni ba'a mun gatse dan ba tsoro gare ni ba bari na jibgeka naga iya gudun ruwan naka, kai yasin ma *TSANGAYAR MALAM* zamu naɗeka mu kai ka irinka dubu sun buga achan sun bari da ayar Allah,kai ma bada bulala da falke ku riƙe shi gam yaga ikon Allah.


Buɗawa ɗan malam yayi yana," duk wanda ke jiran mutuwar sa ya tunkaro ni sai dai gyatumar ta haifi wani ba shi ba, ko yara siyi maraicin dole,cikin hikima da dabar Hakimi ya shammaci ɗan malam ya miƙe a sukwane ya kwashi ƙafafun ɗan malam ji kake,'tiƙƙƙƙƙƙƙƙ a ƙasa da sauri jama'ah suka haɗu aka danne shi aka masa ɗaurin goro katamau malam ya kauda kansa gefe dan ƙwallah ce ta taso masa,sai da Hakimi ya tabbata ɗan malam ya ɗauru sannan ya koma kujerar sa ta girma ya ya zauna kowa ya nemi wajansa ya zauna hakimi ya ce"


'Malam Ƙasimu Cinnaka mun baka wuƙa da nama katafi da wannan yaron ka kai shi *TSANGAYAR MALAM* ko nawa ake da buƙata zan bayar dan barin irin yaran nan a gari sam bashi da fa'ida ba zai lalata mana tarbiyar yara ya addabi kowa a cikin gari na ba ko ya kuka ce jamma'ah.



"Wannan batu naka dai dai ne muma ba mayi ƙasa a gwiwa ba zamu haɗa hannu da hannu wajan taimakawa a akai shi in da zai ladaftu ya koyo yarbiya da alama duk babu a tattare dashi.


   "Maganar ka gaskiya ce Ado duk mun amince da wannan shawarar amma ba wannan ba kamata yayi yanzu a ɗan jiƙa masa koda ƙeyar sa ne ya gane cewa faddah ba wajan wasan yara bane ranka shi daɗe ko dan a tauna ƙasa aya taji tsoro.


'Allah shi maka albarka Ɗan tala abinda ke raina kenan ka rigani faɗa ai idan muka bar ɗan malam ya tafi a haka sai a raina mu dolen dolen mu sai ya karɓi tsimagiyar hakimi ko yana so ko baya so wallahi,ma bada bulala akwantar da ɗan malam a bashi tsabgai ƙwara ashirin dan kiyaye wa a gaba.


"Allah ya taimaki hakimin garin lambu,bulala har ashirin dan Allah ba dan ni ba a sassautawa yaron nan ni hukunci na kawoshi ayi masa dai dai da abinda yayi ba bulala ba ranka shi daɗe.


"Malam balarabe idan na waye ka kana nufin bamu iya hukunci ba mu azalimai ne ko ince mugaye ko?......Hakimi ya furta fuskar sa ɗauke da ɓacin rai sai muzurai yake yana bokaɗa hanci kamar na botorami,malam ya ce'



"Ba haka nake nufi ba ranka shi daɗe shi duka baya daga cikin tirsasawa ko hani ga wanda akayiwa na barin ɓarakar da yake yi haka zalika duka na ƙara kangarar da yara su ƙara ƙaimi wajan aikata abinda ba aso su cigaba da yi, da duka na maganin matsala da ba asamu matsaloli da yawa a garin nan ba yallaɓai.


'Hattara dai malam balarabe a gaban hakimi kake ba a gida ba kasan irin kalaman da zaka dinga furtawa manya rawani ba hauka bane dan kawai kana limanci.



'malam ado kenan da zaran gaskiya ta fita sai ajuya ta akarkatar da ita wani bangaran daban to ina mai sanar maka da cewa,rawani na limanci ba zai hanani faɗin abinda yake dai dai da wanda ba shida dai dai ba Alƙawari na ɗauka zan bi dokar Allah da abinda Manzon Allah(S'A'W),ya ɗora mu bisa kansa ba son zuciya da ɓacin ta ba Attahiru dai ɗana ne na cikina ganin abunda ya aikata bai kamatu ba yasa na janyo hannun sa har gaban Hakimi na kawoshi inda nake da yaƙinin za'a hukunta shi dai dai da abinda Allah(S'W'A) ya shimfiɗa ayiwa duk wanda ya aikata ba dai dai ba ga ɗan uwansa ɗan adam Allah da kansa ya girmama ɗan adam ya bashi matsayi daga cikin matsayoyi masu daraja to mu suwaye da bazamu bi wannan mafita ba ko ni na aikata ba dai dai ina roƙon Allah karya bani ikon da zan ƙi kai kaina a hukunta ni bare kuma ɗan da na haifa da ciki na.



"Mu ba wa'azi muka ce kayi mana ba,kai ka kawo ɗanka da kanka ba wani ne ya kawo shi ba dan haka dole me girma hakimi ya hukuntashi yanda yake so waya hanaka kula da ɗan naka da tarbiyan tar da shi akan tafarkin dai dai zaka zo da ɗan guntun gemun ka da bai wuce kamu biyu ba ka nemi ka shigarwa hakimi hanci,fet zamu fatoka ma fetar idan hukunci bai maka ba ka tashi ka bar wajan babu wanda ya riƙe ka sai a yi sallama da gwaskan ɗan naka dan chan gabas za'yi da shi ba anan garin ba.


      Malam yayi murmushin takaici haɗe da cewa"



"Bazaka gane ba malam Ado idan kwana zanyi ina faɗa maka sam ba shiga kunnuwan ka zasuyi ba,bazaka fuskanci abinda nake nufi ba amma ka sani bani nake bada tarbiya ba Allah ne mai yin duk wani ikon sa akan bawan sa,ku je ku kai shi Allah ya shirya ya tsare ya bada sa'a Attahiru ba ƙinka nake ba so nake ka zama mutum kamar yanda kowa yake na sauke haƙƙin da Allah ya ɗora min naka akai na,na barka lafiya ranka shi daɗe,malam ya miƙe ya bar wajan da sauri ya nufi gida ransa sam babu daɗi, suko sauran jama'ar wajan suka cigaba da Allah wadai da ɗan malam kowa na aibatashi da bawa hakimi shawara mara kyau akan ɗan malam da malam balarabe alhaji badamasi kam cewa yayi'ai ranka shi daɗe da ma sutale malam ɗin kawai aka yi tun da rawanin limancin ke sa kansa fusga yake ganin kowa mara mutunci har masu daraja irin ku muga ta tsiyar matsiya ci,aka kwantar da ɗan malam aka zabge ƙeyar da tsimagiya biyu a haɗe aka mai ashirin da ɗoriya wai ladan wahalar daya bayar sannan ɗan abu ya karkace da baban sa ya ƙarya ta tare suka haɗu sukayiwa Nafi'u rashin ɗa'a,hakimi ya sallami Nafi'u da ɗan abu da basi likitan dabbobi aka bawa malam Ƙamisu cinnaka ɗan malam ya kai chan gabas wa *TSANGAYAR MALAM*,a daran kuwa malam ƙamisu cinnaka ya haɗa duk abinda zai haɗa dan tashi da a suba su kama hanya kuɗin daya wanka kuwa ya kai dubu ashirin ko ma fi na tafiya wanda aka bashi ya kai ɗan malam ya saya masa duk abinda ake da buƙata har kuɗin abincin sa.

    


       Ko da malam ya koma gida gaba ɗaya walwalar sa ta ɗauke tunanin Attahiru kaɗai yake da abun da ya wakana a faddar hakimi da abun ya ishe shi ma ɗakin Attahirun ya faɗa haɗe da saka kuka me tsuma zuciyar me sauraro sai ambatar sunan ɗan malam yake yana""Attahiru,Attahiru Allah ya shirya ya tsare mun kai a duk inda kake, wanda yasa uwaila fitowa ta iske shi yana kuka wiwi a tsugune hankalin ta ya tashi ta tambayi ina ɗan malam yake?


Malam ya zayyanewa uwaila duk yanda abun ya wakana a faddar hakimi,uwaila sai kuka da dana sanin kai ɗan malam wajan hakimi dama an daɗe ana faɗar aibun sa sai yau da suka gani da idonsu uwaila ta ƙudiri niyar ko ankai ɗan malam bangon duniya indai tana raye a duniya sai ta je ta ɗauko shi ko Hakimi zai koreta daga garin sa,a ranar daga malam har uwaila babu wanda yayi sahur ɗore suka ɗora dan a daddafe malam ya fita ya ja sallah subahi saboda zazzaɓin daya rufe shi,malam ƙasimu cinnaka kuwa da asubar fari ya tasa yaransa su biyu suka raka su tasha ya hau mota shi da ɗan malam da ko ah bai tanka ba tun a wajan hakimi har suka hau mota suka nausa Niger su da aka ce Gabas za suyi ashe *TSANGAYAR MALAM* ɗin na chan niger a garin *MARAƊI*.................

_*A nan zan gimtse in da Comments/Share*_

No comments