SHINE SILAH 16-20
*PAGE* 16-20
........................📖'Dakin Mamee yashiga yasameta ita kadai tana zaune sai cika take tana batsewa zama yayi ya gaida ita ta amsa tana cewa ''jiya na tura Binta tayomin Video gidanka naga 'yan kayan da aka kawowa yarinyar kwata kwata gidan beyi kyauba sun Lalatashi da wasu lalatatun kaya dan haka inaso katashi daga wannan gidan ka koma 'karami da baikashi ba ko hayace zan kamama"
tunda tafara magana yake kalonta da mamaki harta kai karshen maganarta sannan yace "haba Mamee tsanar da kikaiwa Najma tayi yawa idai akan Khairat ne nacemiki bason Khairat ne banayi ba zan iya had'asu duka na Aura amma kiyi hakuri kibar Najma nazauna a gidana plx"
Wani mugun kalo ta watsa masa tace ''idan kasake ka zauna agidan nan bada yawuna ba" cikin tsananin tashin hankali yace "dan girman Allah Mamee kiyi hakuri kibarni na zauna a gidana badan Niba" "mtsss afuwa daya zanma itace ka zauna da Najma amma da sharad'i bazata zauna ita kadai ba sai na kaimata Aysha da Amina" kanshi ya dafe kafin yace "shike nan Mamee Nagode"
Bai jira abunda zatace ba yamike ya fice daga 'dakin
10:30am Najib yagama shirinsa na 'daurin aure abokanshi sai tsokanasa sukeyi ango yasha 'kanshi
shikuma sai washe baki yakeyi
Najma tun safe jikinta yake a sanyaye ko wanka sai da aka tsaya akanta sannan tayi akamata kwaliya tayi kyau sosai duk da kwalar da takeyi kukanma dan karta bata fice dinta ne
11am duban mutane suka shaida 'daurin auren Najib da Najma
An 'daura auren amma mahaifin Najma bai dawo ba sai kanen shine da yaye sukayi hidimar bikin
Masha Allah marya tayi kyau sosai Ango Najib sai photo ake 'dauka da amarya banda Najma bata saki jikiba
anyi taro sosai gida yacika da jama'a kowa yana cikin farin ci
Najma na zaune tayi tagumi 'yan uwansu kawayenta suna 'dakin amma kowa harkar gabansa yakeyi iPhone dinta ce tafara ruri ganin wadda yake kira sada gabanta ya fadi kurawa wayar ido tayi harta tsinke bata 'dauka ba wani kiran ne ya 'kara shigowa cikin faduwar gaba ta 'dauka tace "Assalamu Alaikum" "ameen wa'alikumus salam Amaryata yau Allah ya cika mana burin mu ya malakama junan mu yau babba ranace a garemu" Najma batasan sanda wasu hawaye masu zafi suka zubu mataba harta fara shashekar kuka
da sauri Najib yace "wai kuka kikeyi me akayi miki kike kuka" da sauri tace "A'a bakomai" ajiyar zuciya ya sauke yace "gaskiya ki daina wannan kukan yau ranar farin cikice Matata" murmushi ta 'kak'alo yace "yawwa my wife" nan suka cigaba da hirarsu har sukayi salama ya kashe wayar
wadda take kusa da itace ta dafata tace ''Najma kukan da kikeyi yayi yawa nasan akwai dalili" cikin kuka "Najma tace "Walahi Nadiya tunanin makomata nake a gidan Najib dan na fahimci mahaifiyarshi ba sona take ba jiya kiri kiri taringa muzan tani" "ayyah hakuri zakiyi ki ringa addu'a sabuda duk wadda kika gani a gidan mijinta bakya rabata da wani kalubale kema hakuri zakiyi'' "to Nadeeya nagode" nan Nadiya tacigaba da bata shawarwari masu anfani
Tun 5 Najib ya kawo motoci aka 'dauki Amarya Najma wadda Tasha kukan rabuwa da Ummee
da Magrib duk 'yan kaita suka baro gidan sai ita kadai tayi tagumi kan Najib yazo 'yan gidan sune suka zo suka 'daki takula ba wadda yamata kalon banza duk sun gaisa cikin girmama juna
bayan Suntafi ne Najib ya shigo gidan ko Aboki daya baizo dashiba shi kadai zik'au yashigo gidan
a bedroom ya sameta yasamu guri ya zauna yana murmushin sa na 'yan Duniya yace "Amarya kinsha 'kanshi" fuska tarufe cike da kunya yayi dariya zama yayi yaringa janta da hira amma taki sakewa dashi
Nama kaza da drinks ya dako taci amma taki ci ko ruwa taki sha ha'de rai yayi amma duk da haka taki ci dole ya hakura ya rabuda ita
yamike yashiga toilet yayi wanka ya sauya kana nan kaya marasa nauyi
yasa ta sauya kaya suka kwanta
Abunda Najma batayi tsamani bane yafaru dan Najib tunda ya kwanta ko jikinta bai rab'a ba tuntana tunani takasa bacci har baccin ya dauketa
Washe gari
Tun basu tashi ba Aysha ta buga musu gida wai Mamee tace tazo tado nan da zama da suda Amina ne Daddynsu ya hana yace Ayshar ma ta isa ta tayata zama dan acewar Mamee Najma ce ta buk'aci hakan
Najib ne yaji bugun gidan yaja tsaki yatashi yafita itama Najma tanajin fitarsa ta mik'e tashige bathroom dan sun makara sallar Asuba
Bud'e kobar yayi yaganta a tsaye da bags 'dinta a hannu had'e rai yayi yace "ke haka aka koyamiki zuwa cidan mutane da sassafe kiringa tashinsu" baki ta tab'e dan Aysha batada kunya tace "nima ai tasoni Mamee tayi da wuri tace na taho" tsaki kawai yaja yakoma ciki ita kuma tabiyo bayasa
bedroom 'din Aysha ta bu'de ta shiga komai sabone har yafi na matar gidan kyau tasan wannan shirin Mamee ne fadawa tayi kan bed d'in tana ihun murna
Yanan sunyi bearkfast ne itakuma Khairat tazo gidan wai Mamee tace tazo madadin Ameenah ta taya Aysha zama itadai Najma tace cikan kuba kota kansu bata biba
Shikuwa Najib kuka ne kawai beba yasan Mamee rediyo me jini takawo mai gida yadda komai sukayi kamar a gabanta
Da dare bayan sun gama Dinner sunyi hira har gurin 10 Najib sun shiga 'daki sun kwanta
Khairat ta kali Aysha tace ''Aysha wallahi yau bazan bari suyi kwanan nutsuwa ba bari kiga" cire kalabinta tayi ta bazo gashinta ta kwanta a parlour tana burgima da ihu tana kiran cikinta Aysha da take dariya tace "bara na taimaka miki" da gudu tai hanyar 'dakin nasu
Wadda tunda suka shiga dama yau Najma takasa gane kan Najib sai bijiro mata da sababin salo yake gaba 'daya ya sauya lokaci guda tasan ida ya dosa dan haka gabanta ya ringa fadu jin bugun Aysha ma 'karamin dadi tajiba shikuma Najib yaja wani mugun tsaki yaje da fad'a yace "uban mene kuma?" cikin kukan karya tace "Khairat ce batada lafiya"sai lokacin yaji ihunta dan da idonshi yarife baimajiba
fitowa yayi parour ya tsuguna a gabanta aikuwa ta cukukuyeshi wai irin azabar ciwon nane kalon Aysha yayi yace "tasha magani" "Eh" Aysha tace ya kamo Khairat tanata kuka yasata a 'dakinsu ya kwantar da ita yace "Aysha kikula da ita zan ringa zagayoku naga yajikin" "to" Aysha tace yayi hanyar fita haryaje kofa yaji Khairat na kakari tana wani zabura juyawa yayi yaga yadda take yace "daga gani aljanune Aysha dako cup da ruwa namata addu'a nan Aysha ta dako yama addu'a yace tabata tasha daga haka yafice ya rabu dasu
Ya koma 'daki ya maida kofa yarife Najma ta tanbayeshi lafiya yace bakomai Khairat ce bata da lafiya amma yanzu taji sauki kakalo murmushi tayi tace "to masha Allah, Allah ya 'ka sauki" "ameen" yace yana kai hanu yajawo jikisa ya...............!
Naga Comments nayi typing naji shiru kuma zan kwanta na huta nima sai najiku My Fan's
COMMENT
AND
SHARE
by
*XAHRA*
No comments