Breaking News

MATAN HAFIZ 1

 *Bismillahirrahmanirraheem.

1.

 "Menene wannan? uhmm.Nace menene wannan?

Ya fad'a cikin kufula tare da watsa mata d'aurin kud'ade a jikinta.


Da mamaki karara a fiskarta take dubanshi , ta gagara ko motsa bakinta balle tayi magana.


"Ba anan kikace bakisan na shigo da kud'i gidannan ba? Yaya akayi kuma na samesu cikin bedroom dinki har cikin handbag dinki.


Sai a lokacin ta samu damar furta "Inna lillahi wa Inna ilaihir rajiuna."


Sassauta murya kadan yayi.

"Yaushe Kika zama haka? 

Me yasa kishi ya rufe miki ido kike neman ki b'ata sunanki da rayuwarki?

 Tunda zainab ta shigo gidannan kika gagara kwantar da hankalinki a zauna lafiya, fitinar yau daban na gobe daban.

Shin akanki aka fara kishiya?

Barin fad'a miki bazan lamunta ba. Wannan shine na karshe, idan na sake kamaki da wani laifin wlh zan wulakanta ki wulakanci mafi muni kafin ki bar gidannan.


Yana gama fadin haka ya kwashe kudaden da ya zuba mata a jiki ya juya cikin zafin nama ya barta a wajen   daskare tana binshi da kallo.


Kuka take sonyi amma yaki zuwar mata sai zafin da zuciyarta ke mata.


Wannan wani irin bala'i ne? 

Bayan hakurin kara mata kishiyar da akayi har kuma sharri sai suyi ta biyo baya?


Kwanaki anyi mata sharrin ta zuba sugar a abincin kishiya, ta dandana kuma taji sugar'n.

An sake cewa ta ajiye laya a dakin kishiya.

Ance ta yanka d'ankwalin kishiya , kuma an nuna mata ta  gani a yanken.

Tana tabbaci zainab ce ke aikata hakan da kanta kuma ta ce itace.

Bata b'oye mata ba ta sha fad'a mata cewar sakacinta yasa aka aurota.

Ta sha cika mata baki cewar da ace itace matar Hafiz ta fari bazai yi mata kishiya ba har abada.

Ta sha sanar da ita cewa yanzunma kuma bazata zauna da kishiya na tsawon lokaci ba.


A yanzun ma tana da tabbacin shirin zainab ce kai mata kudin Hafiz har cikin d'akinta  a cikin handbag nan kuma bata ma san ya shigo gidan da wani kud'i ba.


Tsam ta mike ta nufi d'akinshi.

Tare da samesu ta zainab yana had'a kudaden cikin jaka.

Kud'ade ne masu yawa.

Duk yawan kudaden da ya fitar daga dakinta basu kai rabin wadannan ba.


Zainab ke tambayarshi kudin na meye ne cikin kinibibi da kisisina shi kuma yana basarwa, sai huci yakeyi yana ci gaba da jera kudaden.


A kansu ta tsaya tana binsu da wani irin kallon tsana yayin da zainab ta d'ago da jefeta da munafukin murmushi tare da kashe mata ido d'aya.


"Hafiz" ta kirashi da murya mai cike da b'acin rai.


Duk da yadda ta kira shin ya tab'a shi, dan bata kiranshi da sunanshi ko kafin suyi aure ma.

Hakan kuwa baisa ya dago ba balle ya amsa mata ba.


Bata damu da rashin amsawar ba tace.

"A shekarun da mukayi da kai a gidannan natab'a yi maka sata?


Sata fa?

ta sake maimaita kalmar satar da alamun kalmar yana kona mata zuciya.


"Kada ka manta, tun baka kai haka ba nake tare da kai.

Ta dan ja fasali snn ta kuma cewa.

"Kuma na tabbata kasan da cewar ba don kudinka na aureka ba, tunda a lokacin dai ba wani arzikin a zo a gani kake dashi ba.

Idan ka gaji da ni kana so ka rabu da ni ba sai ka jefe ni da sharrin sata ba.

Gida naka ne igiyar auren a hanunka take, duk lokacin da ka ga dama zaka iya datse ta ba sai ka bi ta haka ba.

Saboda haka na gaji , kasan yadda zakayi dani yau a gidannan dan naga abin naku ba mai karewa bane.


"Ke kuma."

tace bayan ta maida kallonta ga zainab dake jin dadin dramar da ake tafkawa a dakin.

Ta ci gaba da cewa.

"Ki sani Allah baya barci, shi masani ne akan duk abinda kike aikatawa na b'oye da na bayyane.

Zan ci gaba da kai kuka na gareshi yayi min sakayya daidai da sharrukan da kike kulla min.

Allah zai min maganinku."


Ta karashe maganarta  murya na rawa.

Sosai maganar satan yayi mata zafi.


Fuuu ta fice ta nufi falonta, kamar zata zauna anan saidai zuciyarta na azalzalarta da ta dauki  mataki.

Cikin zafin nama ta shige dakinta ta janyo madaidaiciyar jaka tana zuba kayanta.


***


Tunda ta fita Hafiz yayi tsai yana jujjuya maganganunta a cikin kwakwalwar shi.

Gaba daya jikinsa yayi sanyi.

Idan ya fahimceta duk abinda yake faruwa a gidan bata da masaniya shiri ne kawai dan a shiga tsakaninsu.


"Ikon Allah."

ya tsinkayo muryar zainab take fada cikin alamun mamaki.


"Ko meye dalili sanya ni ciki ni kuma? Wannan shi ake kira da kora kunya da hauka."


kallonta yayi kamar zaiyi magana sai ya fasa ya ture jakar hanunshi ya fita da sauri.


Kofar falonta ya sanyawa makulli ya kulle ya zare ya jefa cikin aljihunshi.


Haka kawai jikinshi ke bashi zata iya tafiya akan maganar nan.

Shi kuma abin kunya ne a wajenshi a ce daga yin sabon aure uwargida ta bar gida.


Kuma ma ko ba komai uwar 'ya 'yanshi ce.

Bai kamata ace an ji su akan kud'i ba, kudin ma da tare sukayi gwagwarmayar rayuwa kafin ya samesu.



****


Wani iri zainab taji ganin ya fita baice komai ba.

Bata san abinda ke zuciyarshi ba.

Shin maganganun Raheema sunyi tasiri a kanshi ko kuwa.


Ta jima tana tsaye a dakin nashi cikin rashin abin yi sannan ta koma can babban falonsu ta zauna ta kasa kunne tana jiran tashin hayaniya amma  gidan tsit tamkar babu kowa a ciki.



****


Ita kuwa Raheema zuciyarta bai bar tafasa ba har ta gama hada kayanta cikin jakanta ta ratayo gyale  tare da dauko jakan.


Turuss ta ja ta tsaya jin kofar falonnata a garkame.

Murda handle ta sakeyi nanma ko motsi.


Jifa tayi da jakar a kofar tana cewa.

"Yau ko kafi Umma kokari (Uwarshi kenan) sai na tafi gidanmu.

Dan ita a yanzu Umman tafi bata haushi dan ita ta assasa maganar karin auren Hafiz din.


****


Tafe yake cikin motarshi yana tunanin  rayuwarshi da Raheema.


Itace Uwargidanshi, sunyi soyayya kwarai da gaske, tun yana makaranta ta jira shi ya kare sukayi aure kafin ma ya samu aikin sojan da yake matukar so.

Da ke yana da'n tab'a sana'a dashi sukayi ta lallab'a rayuwa har Allah ya azurtashi.


Hafiz mutum ne mai zuciyan neman na kanshi, abin wani bai dameshi ba.

Ga shi da saukin kai da kyautata wa duk wadda ke tare dashi.

Shi yasa kannenshi suke ji dashi.


Duk da cewa mahaifinsu yana da rufin asirinshi daidai gwargwado amma shi yana iya kokarinshi wajen ganin ya kyautatawa iyayenshi da kannen nashi.


Suna matukar kaunar juna shi da Raheema.


Suna kuma zaman lafiya, saidai matsalar Raheema shine.

Ta fi bawa karance karance muhimmanci akan komai na rayuwarta.

Kullum zaka sameta rike da novel ko waya tana karanta litattafan hausa.


Da farko hakan bai dameshi ba, dan har yakan zauna ta bashi labaran da ta karanta.


Wani lokacin ma tana kwance jikinshi take karanta musu labaran a bayyane.


Raheema tana da tsaftar jikinta matuka, gurin gayu da kamshi bata da matsala, haka ma tana gyara kanta ciki da waje.


Saidai tsaftar muhalline dai sai a hankali.

Farkon aurensu tare suke gyara gidan shi yasa bai fahimci tana da wannan matsala ba saida tafiya tayi tafiya.

Sannan ya samu aikin soja baya zama sosai a gidan daganan rashin kulawar matar gidan ya bayyana.

Shi kuma gashi da son tsafta, yana so a kullum ya kasance muhallin da yake rayuwa cikin shi tsaftatacce ne.

Yayi fadan, yayi nasiha , yabi da lallami  duk dai babu canji hakan yasa ya kyaleta kawai kasancewar bawai kwata kwata bata yi bane, tana yi sa'i da lokaci.

Yakance mata bai ga amfanin karance karancen da takeyi ba tunda bata daukan darrusan dake cikin su.

Ita kuwa dariya kawai takeyi ta ce "Baza ka gane bane."


Bayan haka sai rashin girki, zata wuni tana shan fruits, milk, snacks da drinks .

Sam bata damu da girki saidai ya sayo ya kawo musu.

Girkin ma sa'i da lokaci take yinshi.


Sallah ne kam idan ta kuskura ya kamata tana karatu a lokacin sallah, yakan kwace littafin ya yaga, idan kuma wayane ya kwace ya b'oye.

Hakan yasa bata wasa  da lokacin sallah.


Tafiya tayi tafiya har kannenshi suka fahimci irin rayuwar da akeyi a gidanshi suka sanar da mahaifiyarsu.


Hakan ba karamin kona mata rai yayi ba dan shima kanshi saida ta nuna mishi ba'acin ranta kuma taje gidan ta gargadi Raheema da ta canza hali ko ta dauki mataki.


Da fari ta sauya halinta duk da dai abin  yana mata wahala haka ta jure.


Saida tayi haihuwar farko abubuwa suka fara yi mata yawa ta fara komawa ruwa.


Haka kuma suka ci gaba da rayuwa har ta haifi yarta ta biyu.


Duk da kaunar da take yiwa yaran bata basu kulawa yadda ya dace , hakan ke haddasa rikici tsakaninta da ubansu.


Nanma kannen nashi ne suka kai rahoto inda Ummanshi ta dage lallai sai ya  k'ara aure........

No comments