Breaking News

SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 6

 *BOOK (1)*

                          6️⃣

Masarautar zazzau_......

Gidan sarautar zazzau yana da yalwataccen girma da tsari, k'unshe yake da 6angarori 2daban ciki kuwa har da 6angaren bayi wanda yake kudu da 6angaren  fulanin yola wato uwargidan mai martaba sarki, 6angarenta yafi na sauran girma  hkma yawan bayi, ita suke kira da fulani kilishi, 6angarenta kuma suna masa lak'abi da yola, y'a y'anta uku dukkaninsu maza, yarima jarma, yarima hassan, yarima hussain, sai kuma 6angaren inno wacce take mace ta biyu ga mai martaba sarki, ita bata ta6a haihuwa ba,  daga ita kuma sai amarya jido wacce take ta uku, tana da yara hud'u, biyu maza, biyu mata,

gimbiya ramlatu itace babba, sai gimbiya bilkisu, sai yarima ayman da yarima farhan, suna kiran 6angarenta da manbilah dayake asalinta y'ar manbilah ce, kowacce tana da bayinta na musamman dake hidimtawa 6angarenta da kuma y'ay'anta, bayin kowanne 6angare suna da irin kalar kayan da suke sanyawa don hk kana ganinsu zaka iya tantace daga 6angaren da suke,  jakadiya dindin uwar bayi mai ran k'arfe,tsohuwa ce sosai wacce a k'alla zata iya cimma shekaru tamanin har da d'oriya itake kula  da 6angaren bayi dama duk wani abu daya shafesu tun zamanin sarki jafaru har kawo yanzu zamanin d'ansa sarki mahmudu......




         Tana zaune bisa wata kujerar k'arfe tana taunar goro da wani k'aton d'auri na d'ankwalin atamfa a saman kanta,hak'oran makkanta uku, suna mak'ale a ragowar hak'oran nata da sukayi saura, rumana dake zaune gefe guda sai k'are mata kallo take, kwalawa wata mace kira tayi, suna wata rumfa a zaune suna tsifan kitso ta sake ta taso da gudu taxo wurinta ta rissina tace" gani jakadiya" kallonta tayi tare da watsa goro a baki tace" tagwai samarwa da wannan d'iyar wurin kwana" ta nuna mata wurin da rumana ke zaune da baki, tagwai ta kalli inda rumana ke zaune sannan ta dawo da kallonta ga jakadiya tace" an gama jakadiya"  tashi tayi ta nufo wurin rumana tace" taso ki biyoni" tayi gaba tana zaton rumana na biye da ita saida ta sake juyowa ta hango rumana zaune a inda take, dawowa tayi ta kalleta tace" baki ji mai nace bane" shiru taga rumana tayi kuma bata ko motsa daga wurin da take ba tace" ikon Allah, ke y'ar nan baki jin ina mgn ne"  jakadiya ta fesar da taunannen goron dake bakinta tace" ke kuwa kurma ce ba jinki take ba" tagwai ta kalli jakadiya cike da mamaki tace" Allah mai iko, dubi d'iya har d'iya ashe ba kunne" hannu ta mik'a taja hannun rumana suka nufi sashin bayi, d'aki d'aki ta soma dubawa tana neman inda bayin ciki basu da yawa nan ta


 samu d'akinsu bintu, su hud'u ne kawai ciki, d'age asabarin d'akin tayi ta shiga rik'e da hannun rumana, taci sa'a dukka y'an d'akin suna nan, kallonta sukayi, d'aya daga cikinsu tace" tagwai kece hk" dariya tagwai tayi tace" bak'uwa na kawo muku bisa umarnin jakadiya" duk suka bi rumana da kallo batare da sun furta komai ba, tagwai ta kalli d'aya daga cikinsu mai suna bintu tace" gata nan na baki amana, sai kunyi hkr da ita don kurma ce" cike da mamaki suka k'ara kallon rumana don da fari har sun soma jin kishi akan kyawunta amma yanzu na suka ji kurma ce sai suka sake da ita, bintu ta janyo hannun rumana ta bata 6angaren a d'akin, tagwai ta juya ta fice, ganinta sukayi babu komai tare da ita ko kayan sawa bata dashi,  saratu ta kalli bintu ta ta6e baki tace"sai wani rawar k'afa kk daga ganin yarinya, k'ila ma irin maita ce" hasiya tace" saratu a kul d'inki wlh, kisan mgnr da zaki din ga fadi ko don kin ganta kurma, kinsan kuwa shari'ar maita bata da k'are" tsaki taja ta mik'e ta fice daga d'akin, rumana kuwa sai kallonsu take cike da miskilanci ta kasa sakewa dasu, su kuma suna son su jata da hira amma basu san ta yadda zasu fara ba don basu iya mgnr kurame ba........


      Washagari, tana kallonsu suna sallar asuba kowacce cikinsu ta soma sanya kayan bautar ta, sarautu ita kalar kayanta irin na bayin dake hidima a 6angaren amarya jido ne, sai bintu dake hidimtawa 6angaren inno, hasiya da kulu kuma suna 6angaren fulanin yola wato kilishi, saratu ta kalli bintu tace" ita kuma k'awar taku ba bauta tazo yi bane na ganta a zaune" bintu tace" sai jakadiya tayi mgn akanta tukunna" bata sake cewa komai ba ta d'auke kanta ta cigaba da d'aura d'ankwalinta, hasiya tace" ko sunan ma bamu sani ba" cikin sauri bintu ta janyo jakar islamiyyarta dake rataye a jikin k'usa ta fito da fensir da wata farar takarda tace" bari na tmbyta sunanta a rubuce" saratu tayi tsaki tace" kaji k'aryar ilimi, sai kuma tace miki ita d'in ta iya karatu koh, son a sani tusa a lasifka" ko kallonta bintu batayi ba ta soma rubutunta, mik'awa rumana takardar tayi ta amsa, sai addu'a take kan Allah yasa rumana itama ta iya karatun hausa, rumana kuwa kallon takardar tayi ta d'ago dakanta ta mik'a hannu ta amshi fensir d'in dake hannunta ta rubuta mata sunanta kamar yadda ta tmbyta a jikin takardar, bintu na duba takarda tayi ihu tace" wallah ta iya


 karatu itama"  cigaba tayi da mata tambayoyi tana bata amsa, hasiya tace" kin ga ki kyaleta mu wuce kar mu makara" murmushi tayi ta maida fensirin nata tare da littafin cikin jaka ta maida jakar ta rataye suka juya suka fice, basu jima da fita ba tagwai ta shigo suka fita tare da rumana suka nufi 6angaren fulanin yola, cikin 6angaren nata yana da fad'i d'auke yake da gini irin na zamani an k'awata shi da ado irin na jinin sarauta, a bakin shiga babban parlourn fulani suka had'u da jakadiya, tana ganinsu ta kamo hannun rumana suka shige parlourn fulani kilishi,suna sanya k'afarsu cikin parlourn wani ni'imtaccen k'amshin turaren wuta daya gauraye da sanyin Ac ya daki hancinsu, rumana tuni ta saki wata lafiyayyar ajiyar zuciya,  wata madaidaciyar mace ta hanga sanye da wata doguwar riga mai kalar shud'i ,ta  kishingid'e bisa wani lallausan catty carpet dake shimfid'e saman wani chinese carpet tayi matashi da wani k'aramin timtim, ita ba fara ba sannan kuma ba za'a kirata da bak'a ba, tana da wadataccen dogon hanci, tana kallon wani k'atoton tvn bango amma ba manne yake a bango ba yana kafe ne bisa wani k'aton stand, suna k'arasawa ciki jakadiya ta zube a gabanta cike da girmamawa ta soma zabga mata kirari kafin daga k'arshe tace" ranki shi d'ade, wannan itace d'iyar dana miki mgn akanta, jikar iya dudu ce" rumana itama tana daga durqushe a gabanta ta sunkuyar dakanta k'asa, k'ureta fulani kilishi tayi da idanu sannan ta maida kallonta ga jakadiya tace" amma sam wannan d'iyar bata kama da iya dudu wannan ai tamkar d'iyar


 buzaye"  jakadiya tayi k'asa dakanta da sauri tace" ehh,ran fulani ya jima, bawai ina nufin kai tsaye jikar iya dudu bace,aa, suna dai da dangantaka da uwarta" shiru fulani kilishi tayi sai kuma ta jinjina kanta tace" ki samar mata abunyi a tsakar gida" cikin hanzari jakadiya tace" toh, ranki shi dad'e" tana mgn tamkar zata kifa a gabanta, rumana dai tana gefe tana kallon ikon Allah har lkcin da jakadiya ta mik'e taja hannunta suka fice, suna fita ta wuce da ita


 babban kitchen,  tana shiga kitchen ta kwalawa goggo tamari kira, ita ke kula da 6angaren kitchen, goggo tamari na jin muryar jakadiya ta fito da sauri tana dariya tace" tsohuwa mai ran k'arfe kin k'i ambato" murmushi jakadiya tayi tace" kin ga wan ga d'iya na kawo miki ki samar mata matsuguni a ma'aikatar taki" ta k'arashe zancen cike da raha, itama goggo tamari dariya tayi tace" babu matsala uwarmu"  wucewa jakadiya tayi tabar rumana a kitchen, goggo tamari ta bata tankad'en gari mai bala'in yawa ta soma tankad'ewa.............


Alkalamin Bintu Ne.....

No comments