SHARUZZAMAN BOOK 1 PAGE 50
*BOOK ONE* (1)
1️⃣0️⃣
Gbdy shirye shirye suke tayi na tarar baqin da zasu zo daga adamawa mgnr neman auren gimbiya bilkisu, abunku da tuwon girma dole miyarsa da nama sosai suke shiri, bayi da hadiman gidan basu da wani lkcin sukuni sbd hidima, ita kanta masarautar hk ake ta gyaranta, ranar litinin kuwa tawagar fulanin usul suka iso masarautar zazzau bisa jagoranci sarkin mubi domin shine ze kasance tamkar waliyin ango, kunsan dai zazzagawa da iya tarar baqi hk suka amshi baqin nan hannu bibbiyu babu
qaranta, dayake sha'ani ne na manyan mutane, kowanne 6angare sun nunar bajintarsu babu wai gsky anyi takun girma, babu wani 6ata lkci mai martaba sarkin zazzau ya basu diyarshi gimbiya bilkisu aka sanya ranar dauri aure nan da sati biyu masu zuwa, daga nan kuma suka sanar dasu cewa kafin ranar daurin aure yariman adamawa ze zo dakansa don ya gana da gimbiya, ranar masarautar zazzau cike take da annuri, kowa yana cike da farin ciki idan muka cire uwar amarya da ita kanta amaryar domin kuwa kulle kanta tayi a daki tana ta sheshshekar kuka tamkar wacce aka yiwa wahayi da saqon mutuwa, she was although crazy in loving someone, shiyasa take ganin tamkar akwai ranar da zata sake ganinsa har ma yace yana sonta suyi aure but unfortunately, qadddara na neman kassara mafarkinta, lkcin da tawagar mutan adamawa zasu tafi hk aka din ga sanya musu daro daron alkaki, dubulan, samosa da dai sauran abuwawa suka tafi dashi....*Bayan sati d'aya*....
Yariman adamawa sharuzzaman ya dira garin zazzau bisa ga umarnin mahaifinsa, ranar duk wanda ya kwana ya hantse cikin garin zazzau yasan zazzau ta amshi babban baqo sbd yadda wasu sheggun baqaqen jeep jeep suka din ga shigowa cikin garin zazzau a jere suke tahiya, gbdy numbobin motocin hk suke *YARIMA ONE* YARIMA 2..... hk dai har saida suka kai guda sha biyu daidai, mutane kuwa ranar sun baiwa idanunsu abinci domin kallon motocin nan kawai suke har sai sun qure, tfy suke sannu a hnkli har suka iso qatuwar farfajiyar masarautar zazzau, inda dallatun zazzau ya taresu, lkcin da yariman adamawa ya fito daga mota tuni wurin ya dauki busa da kuma kirari, ko'ina ka duba saika hango dogarawan masarautar adamawa wadanda suka rako yarima sharuzzaman, sanye yake da wata kyakykyawar alkyabba ruwan shud'i an qawata ta da ado ruwan zinariya, rawanin dake kansa ma shud'i ne, takalmin kafarsa irin na sarka half cover mai adon zinariya, sanye yake da baqin tabarau hkn shine ya 6oye kamannin fuskarsa, saidai hannunsa kawai idan ka kalla kaga cikakken d'an hutu wanda besan meye kalmar wahala take nufi ba, qasaitaccen takunsa kawai shine tambarin wadatacciyar izzarsa, dallatun zazzau ne yyi masa jagora har cikin fadar mai martaba sarkin zazzau, fuskar mai martaba a washe cike da annushuwa ya tari surukin nasa....
6angaren gimbiya bilkisu kuwa tana daga cikin gida amma har yanzu gaban be dena faduwa ba, duk ta rasa nutsuwarta musamman lkcin da wata baiwarta hulatu ta kawo mata rahoton isowar yariman adamawa sai taji gabanta na tsananta bugawa, gumi sai keto mata yake, tana nan zaune fulani kilishi ita da uwar biyu suka shiga dakin nata, rumana na biye dasu riqe da wani qaton kwando cike da turarukan qamshi, tun daga kan na hayaqi har ma dana feshi, uwar biyu ce ta amshi kwandon turarukan daga hannun rumana ta fito dana wanka ta shige bathroom dashi saida ta jima ta fito ta sanar da gimbiya bilkisu kan ta shiga komai ya daidaita, ranta a 6ace jikinta a sabule ta miqe ta shige bathroom din batare da gaddama ba sbd ganin fulani kilishi na wurin ta kafa ta tsare, cikakkun mintu sha biyar batayi ba ta fito, tuni uwar biyu ta soma murje mata jiki da wani man kamshi, daga nan kuma aka mata turaren qamshi sannan ta sanya wata alkyabba mai wuta, gbdy sai tashin qamshi take tamkar ranar take amarya, rumana kam aikinta wurin shine miqa duk abun da aka nema, fulani kilishi bata bar dakin ba saida ta tabbatar da an gama shiryata sannan suka fice, rumana tabi bayansu zata fice itama cikin sauri gimbiya bilkisu ta riqo hannunta, juyowa tayi a tsorace don ta dauka ko laifi tayi,kallonta tayi ta mata alama ta dakata kar ta fita tana son mgn da ita, batare da musu ba ta dawo ciki, miqewa gimbiya bilkisu tayi tsaye ta janyo wani memo da biro ta soma rubutu a jiki sannan ta miqa mata takardan da rubutun ke jiki, hannu biyu tasa ta amshi farar takarda ta soma karanta abunda ta rubuta, tuni jikinta ya soma karkarwa sbd tsorata da tayi da ganin abunda ke rubuce, dago da fuskarta tayi cike da tsantsar rudani da firgici tana kallon gimbiya bilkisu dake tsaye ta harde hannayenta tana murmushi, tace" wannan shine buqata ta gareki matsayinki na baiwata ki wakilceni ki tafi ki gana da wannan yarima yadda babu wanda zeyi zaton kedin bani bace ba, za muyi musayar kaya" bisa tilastawa ta cire kayan dake jikinta ta bata ta sanya tace ta zauna ta jira, dayake hular alkyabbar ta rufe mata fuska amma duk da hk saida tayi qasa da kanta ta nemi gefen gado ta zauna, ita kuma gimbiya bilkisu saita sanya kayan rumana ta sulale ta fice abinta, rumana gabanta ne kawai yake sukuwar bugawa har lkcin da fulani kilishi ta shigo ta sanar da ita yarima na jiranta a falon tarar manyan baqi, miqewa tayi jikinta na rawa kanta a sunkuye fulani ta riqe hannunta suka fita, ita ta rakata har bakin shiga falon saida taga shigarta sannan tabar wurin, tana sanya kafa cikin falon wani ni'imtaccen qamshi ya doki hancinta, kasa daga idonta tayi ta kalli inda yake hakimce, bisa ga tarin mamakinsa sai kawai ganinta yyi ta nemi qasan shimfidadden carpet din dake malale a floor ta zauna tare da sunkuyar dakanta qasa batare data furta koda kalma daya ba, sun fi minti kusan talatin amma shiru kkji babu wanda yace kazil, shi yana jiran yaji ta gaishe shi ne,
muryarsa a ciki yace" ke baki iya gaisuwa bane" abunka da kurma ko dago kanta batayi ba don bataji sautin muryarshi ba lkcin yana mgn, shirun data masa ne yyi bala'in 6ata masa rai, miqe yyi a hnkli ya nufi inda take zaune yasa hannu ya dago da fuskarta, ita kuwa jikinta rawa yake ta kafeshi da wadannan bold eyes din nata da suke farare qal, yanayin kallon da take masa kawai ya tabbatar masa da tsorata tayi, wani taqaitaccen murmushi yyi ya sake mata ha6a ya koma ya dauki glass cup din dake gabansa ya tsiyaya juice a ciki ya dawo wurin da take zaune ya tsugunna ya daga juice din dake cikin cup din ya soma tsiyaya mata a jiki tamkar Allah ya aikoshi, saurin miqewa tayi tana qamqame jikinta ta kwa6e fuska tamkar zata fashe da kuka don ita gani take kamar ya gane ba itace gimbiya bilkisu ba shiyasa ya mata wannan wulaqanci shiyasa ta tsorata sosai, miqewa shima yyi yana kallon fuskarta yace" kar kiyi zaton kin chanchanci na aureki ne, zan aureki ne bisa umarni sannan zaki rayu cikin gidana ne a matsayin baiwa, wannan shine albishir din da nk miki" har ya gama mgn kallonshi take don bata fahimci me yake fadi ba, saidai yanayin yadda take ganin ya mgnr ya tabbatar mata baqar mgn yake watsa mata, saurin sunkuyawa tayi a gabansa bisa kan guiwowinta ta daga hannu alamun ban hkr don ita duk abun nan gani take ganewa yyi ita baiwa ce shiyasa ransa ya 6aci sosai, shi kuwa kafeta yyi da idanu cike da mamaki, shi kuma sai yyi tunanin abunda ya fada mata ne yasa ta durqusa tana bashi hkr........
*Littafi na biyu na kudi ne*
Alkalamin Bintu ne......
No comments