Breaking News

JAMI'IN DAN SANDA 19

 👨🏻‍🔧  *JAMI'IN 'DAN SANDA*.  👨🏻‍🔧

🅿️_19

....................cikin tsananin tsoro duk suka zaro idonsu tareda d'ora hannunsu akai🙆🏻‍♀️🙆🏻‍♀️ganin irin shurin da Hisham yayi da Haruna wanda k'ara d'aya yayi bai koma koda motsi ba , gaba daya idonsu kamar zasu fado k'asa yayinda cikinsu yayi wata irin murd'awa , 

Hisham kam baima kula da Haruna ya daina motsiba tsabar yadda zuciyarshi da idonshi suka rufe , sai ma k'ok'arin sake dukanshi da yakeyi , aikuwa 360 Ibrahim ya k'araso kusa da Hisham ganin ya daga k'afa zai saike d'auke bawan Allah da wani zazzafan shuri wanda yanada tabbacin in yayi mashi shi sai Allah idan ,zai rayu wannan yasa ya rik'e Hisham gam cikin rawar harshe yake fad'i , 

" Pls Hisham ka dawo cikin hankalinka mana ka tsaya muyi komai a nutse karkayi mana kisan kai pls ,"

Duk maganar da yakeyi sam Hisham baijinshi sai ma k'ok'arin k'wacewa da yakeyi, 

Matar Inspector Haruna kuwa tun lokacin da Haruna  yabuga wannan uwar k'arar ta rugo aguje zuwa d'akin , ganin abunda ke faruwa ne yasa ta fita aguje tana ihu da kiran ataimakamata za'a kashe mata miji , kamun kace mi har gidan yafara cika , 

Samarin unguwar da zafinsu suka shigo amma ganin Hisham sanye da kayan yan sanda sannan kallo Daya zaka mashi kasan cewa tabbas wannan ,Zaki ne da yake ganiyar farauta duk wanda yayi gigin shiga gabanshi kuwa to tabbas sai dai uwarshi ta haifi wani bashi ba , wannan yasa suka maida wuk'ar suka shiga lalla'ba  Hisham da kyar tsoffin unguwar suka samu suka raba Hisham da Haruna wanda baimasan inda kansa yake ba, 


Ibrahim ne ya sanya shi mota sannan yaja motar aguje suka bar unguwar don ya tsorata da yanayin abokin nashi tabbas in aka barshi zai iya kashe Haruna , gashi zafin zuciya yasa baiko bari Haruna yabashi shaidun da yace zasu taimakamashi wajan kama wadan nan azaluman ba , 


Mansur kuwa da yayi mutuwar zaune sai yanzu ne yasamu damar iya motsa jikinshi tabbas ya tsorata da muguwar zuciya irin ta yayan nashi , ashe haka yayan nasu yake ashe k

Zai iya kashe mutum sukutum saboda kudi kuma mutumin ma Abokinshi wato shiyasa yake yawan faɗin Alhaki ne ke bibiyarshi ashe shi yasan mugun abunda yake aikatawa wama yasan iya adadin mutanen da yakashe saboda son zuciya gashi nan yanzu wa gari ya waya , ina wadan da yayiwa aikin suke , ? Sun gujeshi saboda yagamayi masu amfani , 

Duk da yanda yakejin zafin shi kanan ya daure yasamo mai nafef suka sanyashi suka nufi asibiti dashi don har wannan lokacin bai farfado ba,



Direc gida Ibrahim ya wuce dasu zuwa lokacin gaba daya Hisham yagama ficewa daga hayyacinshi sam baya gane komai sai wasu irin surutai yake marasa kan gado , don abun ba k'aramun dukan k'wak'walwarshi yayi ba musamman da Haruna yamashi bayanin duk irin yadda suka shirya wannan had'arin gaba daya Abbanshi kawai yake gani a idonshi kamar a gabanshi hadarin ya faru,


Kamashi Ibrahim yayi suka shiga cikin gidan , a falo suka tarar da Momma ,

Tana ganinsu a wannan halin ta zabura a firgice tana tambayar abunda ya faru, 

"Lafiya Ibrahim mi yasameshi, tayi maganar a tsorace don ganin halin da d'an nata yake ciki yayi mugun bata tsoro don bata taɓa ganinshi a irin wannan halin ba ko lokacin mutuwar mahaifinshi kuwa ,


Zaunar dashi ibrahim sannan ya dubi Momma cikin karfin hali don shima ba k'aramun tashin hankali ya tsinci kanshi aciki ba yau yace " bakomai Momma ki kwantar da hankalinki ki tofa masa addu'a PLS ko ya dawo cikin hayyacinshi ,"


"Yazaku shigo cikin irin wannan yanayin sannan kacemin  ba komai Ibrahim , ?" Tayi tambayar jikinta na rawa,


"Kinga Momma ki kwantar da hankalinki an gaya mashi maganar da ta d'aga hankalinshi ne amma kibari ya nutsu zan maki bayanin komai ,"


Da mamaki Momma ta dubeshi har zatayi magana kuma sai ta fasa ta nufi Hisham ta zauna a kusa dashi tafara tofa mashi addu'o'i , inda daga baya tafara maimita innalillahi wa Inna ilaihin raji'un , a bayyane , a hankali shima yakama yana maimaitawa ,ganin hakan yasa Momma tayi murmushi a ranta don tasan koma minene to yanzu zai samu nutsuwa , aikuwa sai gashi a hankali yafara dawowa cikin hayyacinshi , lumshe idonshi yayi yanajin yadda kanshi ke wani irin sarawa kamar zai cire ga gawata irin k'ishi da yake ji bakinshi ya bushe sosai  amma sam yakasa bude baki yayi magana , sun jima a haka sai da suka tabbatar da yadawo cikin hankalinshi sannan suka sauke ajiye zuciya gaba daya ,yayinda Momma ke cike da tunanin  abunda  yasamu dan nata har yafitar dashi daga hayyacinshi ,


Juyowa tayi ta zubama Ibrahim ido tace "Ibrahim ka gayamun mi yake faruwa , sam karka 'boyemun komai Ni musulma ce kuma nasan ƙaddara mai kyau ko akasin haka nayi imani ba abinda zai samu mutum face da sanin Allah ta'ala , nasan Allah baya ɗorawa bawa abunda bazai iyaba don haka ka gayamun kawai ko na samu nutsuwa a raina,


Hmmmm Ibrahim yayi ajiyar zuciya kamun a hankali ya bud'e bakinshi yace " Momma dama akan Abba ne.....,

Wani irin fad'uwa gaban Momma yayi amma sai ta danne tace " ina jinka wane Abban kenan?"


"Abba dai na nan gidan Momma Abban Hisham , to daga wajan Abokinshi Inspector Haruna muke , bisa dalilin son ganinku da yakeyi keda Hisham , to sai dai Hisham yace bazaije dake ba sai dai yaje shikad'ai inyaso koma minene shi sai ya gayamaki , 

Nan dai yashiga bata labarin abunda ya faru tun zuwansu har kawo yanzu wanda tunda yafara maganar Momma ke kuka sosai har yagama bata labarin wanda zuwa lokacin shima kukan yakeyi saboda yadda yake matuk'ar jin tausayinsu a ranshi yana tunanin in shine wannan al'amarin yafaru dashi ya zaiji ,


Cikin muryar kuka tafara magana ,

"Dama nasani ,najima da sanin cewa kashemun miji akayi saboda kawai an tsani irinsu a k'asar nan duk wani wanda yace zai kawo gyara a kasar nan tamu to za'a waye gari ne babushi a doron k'asa miye laifinsu?? saboda kawai suna aiki akan gaskiya? Ko saboda basa goyon bayan zalunci da azzalumai ,? shiyasa aka za'bi kawarda ire-irensu a doron ƙasa, wannan dalilin ne yasa na tsani aikin nan nashi saboda a kullum cikin barazana yake sun jima suna shirya mashi gadar zare kamar yadda suka jima suna kawarda ire-irensu ak'asar nan" 


Tunda tafara magana daga Hisham har Ibrahim ido suka zubamata da mamakin kalaminta , cikin karfin hali Ibrahim yace ,

"Amma Momma kinsan da wannan kuma kikayi shiru babu wani mataki da aka dauka"?


"Hmm wane mataki za'a dauka ibrahim , ko in nayi magana zasu dawomin dashi ne ,sun riga da sun cuceni sun rabani da bangon jinginawata banida kowa sai Allah sai shi da Hisham ,nasan ba abunda za'yi ko na d'aga maganar nan mussaman ma da banida wasu kwararan hojjoji, ko inada hujjar ma bawani amfani don mai kudi shikeda hujja a yanzu akoma minene ,

sannan ina 'boye komai ne saboda Hisham nasani in ya sani komai zai iya faruwa don bazai taba yafe masuba kamar yadda suma bazasu taba kyaleshi ba zasu iya bin duk wata hanya don ganin sun cutar dashi kamar yadda suka cutar da mahaifinshi , abunda kuma bazan iya jura ba a wannan lokacin Hisham shikadai nake kallo naji dadi  wannan yasa tun farko na barsu da Allah nasan Allah ba azzalumin bawansa bane ko yaushe ne Allah zai Mana sakkaya in a duniya in a lahira, 


Izuwa yanzu kam idonshi ko kalluwa basayi tsabar jan da sukayi kamar jini zaifita daga cikinsu a hasale ya mike tsaye lokaci daya ya kaima wani table dake kusa dashi duka wanda ya kasance na glass ne aikuwa nan take ya tarwatse yayinda lokaci daya hannunshi yafara zubda jini saboda glass din da suka shigar mashi a hannu , wani irin gurnani yakeyi kamar wani zaki cikin kakkausar murya yafara magana ,

"

"Wallahi wallahi duk sai na shirya masu gadar zaren da zata rufta dasu wallahi sai naga bayansu da hannuna yadda suka kashemun mahaifi haka zan bisu d'ai bayan d'ai ina kashesu inyaso nima a kasheni amma tabbas bazan barsu ba , bazan taba barinsu ba *sai na dauki fansa* wannan alkawarine,



Dukkansu idanu suka zaro suka zuba mashi don kuwa yanayinshi ya firgita tunaninsu kallo Daya zaka mashi ka tabbatar har cikin zuciyarshi ne zai iya aikata abinda ya fad'a ga hannunshi na zubar da jini sosai amma bai kulaba kamar ma ba a jikinshi ciyon yake ba , wani irin tsoro ne ya daki zuciyar Momma lokaci daya ta fashe da wani irin kuka kamaun tafara magana ,


"Hisham indai Ni na haifeka to tabbas ban yarda ka dauki hukunci da hannunka ba ban hanaka neman hakkinka ba amma bata wannan hanyar ba idan kuwa har kace zaka dauki hukunci a hannunka to kuwa bazan taba yafe maka .........daga haka ta juya tayi shigewarta d'aki tana gunshek'ar kuka gaba daya sun tado mata da mikin mutuwar mijinta ga kuma halin da Hisham yake ciki ta tabbatar da idan har ta kyaleshi to zai iya kisan kai wanda bata fatan hakan sam...............✍🏼





*Narage yawan typing sai naga yanayin comment dinku tukun*😜😜😜😜



*Akwai zafafan kayan mata kala kala hade da ingantacce maganin nono maganin sanyi maganin hips magani kiba uwa uba kalolin kayan mata naji da fadi kedai garzayo kar abaki labari ina Sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

No comments