Breaking News

SHARUZZAMAN 1 PAGE 4

*BOOK (1)

             _SHARUZZAMA

_BINTU S££R_

                    

6angaren nasa yana da mutuk'ar girma kuma duplex ne, k'asan akwai manyan parlours  guda biyar, saman kuma parlours biyu ne manya sai bedrooms guda uku tafka tafka tamkar irinna 5star hotels,

kowannensu yaji dubai furnitures,gsky alhaji badaru ya shirya cin duniya, wannan daula hk tamkar babu mutuwa, rumana kam duk wannan duniyar bata d'auki hnklinta ba babban damuwarta shine tana son sanin mene dalilin kawota 6angaren nan don innaro ta kasa sanar da rumana igiyar auren alhaji badaru na d'aure akanta, rumana dai idanunta sai tsiyayar hawaye yake tana son tayi mgn don tana cike da tarin tmbyoyi amma babu muryar mgn, komai binshi kawai take da idanu, bedroom d'inta itama yana saman kusa nashi, tunda aka shigar da ita d'akin dayake matsayin nata ta nemi can k'uryar gado ta la6e sai kuka take kamar ranta ze fita, alhaji badaru magal kuwa ranar baki har kunne ya samu y'ar shila saidai ta 6angare guda kuma shima yana cike da tsoro da fargaba kusatar iyalin nasa domin yasan komai ze iya faruwa, wannan zullumi shine ya rage masa annurin fuska ya bayyanar da tsantsar damuwa tattare dashi hkn yasa duk da irin d'okin kasancewa da rumana dayake amma ya kasa tunkarar d'akinta, hk ya wuce ya shige bedroom d'insa saidai duk bayan mintina sai ya fito kalli kofar dakin nata domin zuciyarsa ta kasa sukuni sai harbawa take yana mutuk'ar shakkar abunda ze iya faruwa idan har rumana itama ta mutu, yana kwance idanunsa a rufe har bacci ya soma d'aukarsa tuni ya soma wani irin  mafarki cikin mafarki nasa ne yake jin  kuwwa a kunnensa yana amsa amo cikin dodon kunnensa ba,tashi guda kuma  wata kalar murya tamkar tana rawa ta soma mgn" drrrrrr! tabbas wannan gangaci ka aikata babba, ka janye hasken uduhah! ka janye hasken uduhahhhhhhhh" a tsorace ya farka yyi zumbur ya mik'e yana kalle kallen d'akin yaga komai na d'akin  yana nan inda yake, komawa yyi ya zauna sai gumi yake tamkar yyi tseren gudu ya rik'e kansa da hannu biyu, shikansa mafi yawan lkci yana kyankyanin kalar rayuwar dayake,zina ta zama masa tamkar ruwan sha domin be isa yyi tarayya da matar sunnah ba, idan har yyi gangancin kusantar mace wacce igiyar aure ta hadasu toh ranar  matar a k'iyama zata kwana, idan har  yaji sha'awar mace toh saidai yabi na bariki, wani tunani yyi yasashi mik'ewa da hanzari ya bud'e k'ofar bedroom d'insa ya fita ya nufi d'akin rumana kai tsaye,  murd'a handle k'ofar nata yyi yaji shi a bud'e ya tura kai ciki, ganinta yyi taci kuka har ta k'oshi ta kwanta a takure a k'arshen gado tamkar wacce za'a sace, tsayawa yyi ya k'urawa kyakykyawar fuskarta idanu, less ne golden mai d'auke da adon stone  a jikinta duk da yana da nauyi amma hk ta kwanta dashi batare data sauya wani kayan ba, yanayin kwanciyar nata kawai ya nuna baccin dole kawai take, har yakai hannu da niyyar ta6ata ya gyara mata kwanciya kome ya tuna sai kuma ya janye hannun nasa da sauri, kunna mata Ac yyi sannan yaja mata kofa ya fice ya koma d'akinshi, tun wannan mafarkin da yyi be sake jin komai ba amma duk da hk bacci ya gagari idonsa...




        6angaren innaro kuwa kwana tayi tana nafilfilu da hailala da nemarwa rumana tsari kan dukkanin sharrin mai sharri da makircin mai makirci,Allah ya tsareta da sharrin mutum da aljan, burinta kawai gari ya waye taga yaya lafiyar d'iyarta domin an tabbatar mata kusan dukkanin matan alhaji badaru a daren farko suke gamuwa da ajalinsu shiyasa take cikin mutuk'ar tashin hnkli, hk take jimawa a sujjadarta tana rok'on sarki kowa da komai kan ya ku6utar da rumana kan sharri dake tattare da wannan aure, hawaye take sosai take kuka, zuciyarta na harbawa cike da tsoron abunda ze faru da d'iyarta a wannan dare.....




      Rumana kam baccinta tayi nisa cikin bacci taji kamar ana ja mata gashi, bude idanunta tayi a hnkli ta duba gefenta  bata ga kowa ba sai kawai ta maida idanunta ta rufe tana tsammanin ko mafarki tayi, tana komawa baccin ta kuma jin yadda taji dazu, wannan karon tashi tayi zaune da sauri tana waige waige cikin dakin bata ga komai ba kuma bata ji motsin kowa ba,sakkowa tayi daga saman bed d'in ta nufi bathroom tayi alwala ta fito tada sallah kamar yadda mahaifiyar ta  umarceta dashi,bata kuma jin komai ba har asuba ta kunno kai, washegari, da safe, alhaji badaru ya shiga dakin nata ya tarar da ita zaune a bakin gado,  tana ganinshi tayi wata irin zabura cike da tsoro ta rarimi mayafinta dake gefe ta rufe jikinta, action dinta ne ya bashi yasa shi murmushin karfin hali,  hannu yasa cikin aljihun rigarsa ya ciro wata farar takarda ya mik'a mata yace"ungo wannan kije wurin mahaifiyarki ki gaisheta"  kar6ar takardan tayi batare data bud'e ba ta fita da ita rik'e a hannunta, 6angaren innaro ta nufa da sauri, tana shiga ta tarar da ita ta rafka uban tagumi, aikuwa tana ganin shigowarta ta mik'e ta rumgumeta cike da farin ciki tana sake dudduba jikinta don tabbatar da lafiyarta, sai lkcin idanunta yakai kan farar takardan dake rik'e a hannunta, alama tayi mata da hannu kan wannan takardar meye a hannnunta, murmushi tayi itama tayi mata alamar kan alhaji ne ya bata batasan na meye ba,  innaro ta kar6i takardan da sauri ta soma warwarewa tamkar wacce ta iya karantawa, mayar mata tayi da takarda tace ita ta karanta , sai lkcin rumana ta maida hnklinta kan takardan aikuwa tana tozali da saqon takardan dukkanin walwalar fuskarta ta dauke dif ta dago idanunta  tana kallon innaro cike da tuhuma da zargi.........


No comments