Breaking News

MATAN HAFIZ 8

8.

Yanzu saboda Allah karatun littafin da nake shi ne na banza Abban Sultan? 

Hafiz ya ce "Na banza ne mana saboda ni dai ban ga abinda ya anfana miki sai lalaci da son jiki, a da ai ba Haka kike ba Heema amma yanzu duk kin zama wata iri kuma kin daina bani kulawa a matsayina na mijinki"


"Ni fa na gaji da wannan tozarcin da kake mini, kun fi so kullum ku ganni zaune bakincikin ku ya kasheni Kai da yan uwanka da matanka? karantun nan fa da nake shi ne yake rage min damuwa da sanya ni farinciki to ba zan daina ba, maganar kulawa kuma ai ba ni kadai bace matarka, idan Kana so ka kirani da ko wacce suna ba zan damu ba, tafiya ce za ka yi Kai da matarso amaryarka Allah ya kiyaye hanya ta na gama maganarta ta wuce dakinta ta barshi nan zaune sake da baki ya bi ta da kallo har ta bace ma ganinshi"


"Oh ni Hafiz yaushe Raheema za ta gane cewa ita ce farincikina da ruhina baki daya? Murmushi ne ya baiyana a fuskarsa saboda wannan fushin da ya gani a fuskarta ya nuna cewa ta na kishinsa, dama Duk wannan fadan da nake mata saboda ta gyara halinta ne amma kullum abubuwan ta kara lalacewa suke, da ya ga babu mai bashi amsar tambayoyin shi sai ya mike ya bita dakin".


Yana shirin shiga dakin, sai ya ji ana shewa da dariya, juyawar da zai yi sai ya ga Zainab tsaye ta watsa mishi wani mugun kallo ta ce,


"Tir wallahi an dai ji kunya, Allah ya isa ban yafe ba dama ta na jin haushinshi tunda ya fada musu cewa wannan tafiyar tare da Fateema zai yi ..."


 Katseta yayi ta hanyar daka mata tsawa ya ce,


"Zainab zan Saba miki, wai ke me yasa bakida tausayi da Imani? Idan haukan naki ya tashi baki ji baki gani, Kina ganin halin da take ciki fa, a hakan kike so na tafi na barta cikin damuwa alhalin ba ita kadai bace?"


"Hafiz na gaji da haukatani da kake a kan waccen kodadiyar matar taka, ita ka dai ta fara yin cikine? Ko a kanta aka fara yin laulayi, To tsaya ka ji duk wani makircinta ina sane dashi ta na kafewa da cikin ana cin zalina dan Haka ba zan yarda ba, kuma sai Allah ya saka mini wannan tafiyar da za ka yi da Fateema saboda da ni ya dace ayi tafiyar".


Bai bi ta kanta ba ya shiga dakin Raheema ya barta ta na ta zage zage da magangganun da basu da ce ba, idan ya ce ya biye mata halakata zai yi saboda Zainab irin matan nan ne masu bakin kishi ko jibgarsu za a yi bakinsu ba zai mutum ba. Raheema kuma ta na shiga dakin toilette ta wuce ta yi wanka saboda zafi take ji Sosai a Yan kwanakin nan, bayan ta gama ta fito daure da tawel da dan karami ta na goge gashin kanta da ya jike. Hango Hafiz ta yi Yana zaune bakin gado ya zuba mata idanu ba ko kiftawa baya yayi, ita kuma ta dake ta yi kamar bata ganshi ba saboda haushinsa take ji har yanzu, girgiza kansa yayi ya Mike ya isa inda take ta na neman kayan da za ta saka saboda har yanzu bata so ta ji kamshin man shafawarta, rungumeta yayi ta baya a tare suka sauke ajiyar zuciya ya juyo da ita ta na kokarin kwace kanta ya kara mannata a jikinsa Yana shafa bayanta A hankali, da kyar ta iya ce wa "Wai kun fasa tafiyar ne?" 


Ya ce mata "Ta yaya kike tunanin zan iya tafiya Alhalin kina fushi dani my Heema? Ai ko na tafi hankalina ba zai kwanta ba, ina sonki Heema ina kaunarki kice mace ta farko da na fara so, ke ce hasken da take haskaka mini gidana ina bukatarki a rayuwata dan Allah ki daina fushin ko dan lafiyar bbynmu ya karasa maganar fuskarsa tattare da damuwa". Shiru ta yi ta na maganar zuci, amma wasu mazan munafukai ne ji yadda ya tsaya a gabana Yana zubo zance sai ka rantse ni kadai ce matarsa, to su wa'ancan da ya aura baya son su ne komai? Bama wannan ba da Yana sona kamar yanda ya ce ai ba zai mini kishiya ba, kuma gashi ya ce tafiya zai yi da Fateema Allah kadai ya san irin kulawar da zai bata a can,  a gabana mahaifiyarsa ta ce mai sai ya kara aure, wani irin tsanarsa ta kara ji a zuciyarta, so ta ke ta janye jikinta daga rungumar da yayi mata amma ina ko motsi ta kasa yi dago kanta da za ta yi yayi nasarar hade bakinsu waje daya ya fara sarafa harshensa cikin bakinta, ita kanta ta san cewa ta na son mijinta so Bana Wasa ba kuma ta yi kewarsa sosai kawai dannewa take saboda kada ya fahimta bata san lokacin da ta rike kansa da hannayenta guda biyu ta na maida mishi martani Sun dauki lokaci mai tsayi suna Abu daya tsakanin miji da mata fa sai Allah da na ga Sun nufi bakin gado na ja musu kofar na wuce Zainab sai harara take zabga mini hhhhh.


Dakin Fateema na nufa naga wainar da ta ke toyawa ita kuma, da isa na na ji ta na cewa,


"Wallahi Mufeeda ba zan yarda ba, dole sai na yi maganinsu ta yi shiru ta na sauraren hudubar kawar tata zuwa can ta cigaba da cewa, sabar ya gama zubda mini mutunci har matansa ya fada ma baya sona, yanzu kuma dan ya raina mini hankali ya ce dani zai yi tafiya salon ya ci zalina a can yauwa kawata shi yasa nake sonki insha Allah Haka zan yi sai anjima kada ya iskeni ban hada kayana ba ki gaishe mini da su Mama koma meye idan mun dawo zamu san abin yi bye" ajiye wayar ta yi ta shiga hada kayanta sauri sauri saboda mugun shakar Hafiz take saboda kwarjini yake mata gashi Allah ya jarabceta da mugun kaunarshi a zuciyarta bayan ta gama ta shiga wanka ta na fitowa ta saka bakar abaya babu laifi Fateema kyakyawa ce ita ma.


Su Hafiz kuma bayan komai ya lafa suka shiga wanka suna fitowa yayi saurin maida kayanshi saboda jirgin karfe tara zasu shiga yanzu kuma takwas da minti ashirin, sai kiransa ake a waya du wannan saurin da yake hannunsa daya na cikin rigar Raheema ya na shafa bbynsa ita kuma sai shagwaba take masa hannunta ya rike ya bata kudi ya ce ta rike wannan kafin Allah ya dawo dashi ya mata kiss a goshi ya bar dakin ta Na mishi Addu'ar dawowa lfy da kuma godiya, wannan halin na Heema shi yake kara mishi kaunarta a zuciyarsa duk abinda zai bata sai ta yi godiya. Ya na shiga dakin Zainab ya ajiye mata kudi ita ma ko tsayawa bai yi ba har zai wuce dakin Fateema ya ga rashin dacewar Haka saboda ko babu komai a matsayin matarshi take dole ne ya bata kulawa ita ma kuma gashi tare za su yi tafiyar, a hankali ya tura kofar dakinta da sauri ta daga idanunwanta ta zuba mishi wani irin kwarjini yayi mata kawar da fuskarta ta yi ta na gaisheshi, amsawa yayi a dakile ba dan kada Mahaifiyasa ta yi fushi dan me zai yi tafiya da matar da baya so? Juyawa yayi ya bar dakin.


Takaici bakinciki sune suka saukar ma Fateema a lokaci guda kome ta tuna oho na ga dai ta na murmushi abubuwa da yawa ta ke ayanawa a ranta tunani take yadda za ta zabga rashin mutunci idan Hafiz ya shigo hannunta. Da sauri ta Mike ta ja akwatinta ta bi bayan shi har ya shiga motar yana jiranta sai cika yake Yana batsewa, da kanta ta saka a kwatin bayan but ta bude baya za ta shiga kallan da ya watsa mata ta yi saurin bude gidan gaba ta shiga, da mugun karfi ya ja motar Kadan ya rage yayi gaba da maigadin gidan shi ya ruga dakinshi a guje har Yana tuntube, Mussa mai gadi ya ce, "Kai wannan Amaryar dai bata shigo gidan a sa'a, tunda aka yi auren nan ya daina ganin  dariyar maigidanshi Allah dai ya kyauta".


 Ya rufe gidan ya zauna bisa dadumar shi ya na karanta littafin Hisnun musulm.


Hafiz suna isa filin jirgi ba su dauki wani lokaci ba aka fara Kiran sunayen matafiya abokansa sai tsiya suke mishi yayi banza da su, Sun gaishe da Fateema suna janta da hira irin na abokan miji, shi dai Hafiz shiru yayi musu  ya na tunanin Matansa da yadda za su tafiyar masa da gidansa kafin ya dawo kowacce da tata matsalar da ya tuna da halin da suka kasance shi da Heema yayi murmushi da Haka aka Kira sunanshi saboda ita Fateema ta shiga tuni har ta zauna mazauninta ba'a jima ba sai ga Hafiz  ya shiga ya zauna kusa da ita har yanzu fuskar tashi a hade take jirgin na su ya daga...

No comments