Breaking News

MATAN HAFIZ 15

15.

Wai ke Zainab yaushe zaki yi hankali ne? Ta na shirin yin magana ya Daga mata hannu ya cigaba da cewa "Ba fa tsoronku nake ji ba da nayi shiru na kyaleku kuna iskancin da kuka ga dama, har kunya nake ji abokaina su zo gidana saboda kada kuyi mini hauka a gabansu, A ido dai gaku Kamar masu

hankali Amma ko mintu biyu mutum ya zauna daku sai yayi Allah wadai daku, to ya isheku hakanan ko wacce ta gyara halinta idan ba haka ba Kuma hmmm ya sa Kai ya bar musu gidan gabaki daya."


Takaici bakinci sune suka Hana Heema ko motsin kirki, ita dai ta shiga uku a wannan gidan. kowa tashi jabarshi sai ya hada da ita, bata shiga harkar kowa Amma kullum sai anci mutuncinta. Magangannun Hafiz sun Kona mata rai sosai maimakon ya hukunta Zainab da Fateema da suke matsifar su aa Saida ya hada da dukansu. Zage zagen da su Fateema suke shi ne ya dawo da ita a duniyar tunanin da ta lula, dogon tsaki taja ta bar musu falon ta shige dakinta.



Asalin labarin


Alhaji Ahmed dane a wajen malam Ismail da Inna Lami, manomi ne Wanda yake zaune a garin Niger republic jahar Damagaran, malam Ismail mutum ne da ya dogara da kansa kasancewa su biyu ne mahaifansa suka haifa shi da kanwarsa Maryam bayan rasuwar mahaifansa da wata biyu kanwarsa ma ta zo ta rasu a lokacin yanada shekara ashirin da uku a duniya ya zama maraya gaba da baya ba uwa ba uba danginshi duk sun guje shi, ko yaje inda suke korarshi suke haka yake shiga gari yayi dako ya samu abinda zai ci saboda karatun ma ya ajiye shi gefe tun bayan rasuwar mahaifansa, Inna Lami sunyi auren soyayya shi da ita diyar maigarin garin ce ta na da kyau ba laifi uwa uba ga kunya, kasancewa maigarin ya san mahaifin malam Ismail bai wani tsaya dogon bincike ya bashi auren diyarshi lami, bayan tarewar lami abubuwa suka Kara kwabe ma malam Ismail ya rasa yadda zai yi wani lokacin haka zai fita gari ya wuni Yana neman aiki ya kasa samu, yauw ma Kamar kullum tafe yake Yana zullumi da tunani yadda rayuwarsu zai cigaba da tafiya a haka har ya karaso gida yayi sallama ya shigo gidan, da sauri lami ta amshi ledar hannunsa tana murna saboda jiya ruwa kawai suka Sha suka kwanta, bude ledar tayi taga garin kwaki ne da suga sai madarar gari leda biyu, ta juyo ta kalli maigidan nata ta ce,


"Malam Ina ka samo mana wannan?"


Murmushin karfin hali yayi ya ce,


"Na biya wajen mussa mai shagone abokina shi ne fa ya bani ledar ni banma bude ba".


Kai Alhamdulillah Allah mun gode maka ka Kara mana kwanciyar hankali da lafiyar jiki, ya amsa da "Amine" wannan halin na lami shi ne yasa take Kara shiga ranshi Yana sonta so mai sanani. Katse mishi tunanin tayi tare da mika mishi ruwa, karba yayi ya kafa kanshi yasha sosai sai ya ajiye yayi hamdallahi, yauwa malam da zu maigari ya aiko wani yaro Yana nemanka... Da sauri ya kalleta tare da cewa,

."Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, shi kenan lami rabani za'ayi dake dama na sani watarana sai an rabamu saboda na kasa Baki Kulawa yadda ta dace, duk hakinki da ya rataya a wuyana bana cikashi wani lokacin haka muke kwana Bamuci ba ya karashe maganar idanunsa Yana ciko da kwallar tausayin kansu".


Doguwar ajiyar zuciya lami ta sauke ta ce "Babu Wanda ya isa ya rabamu sai Allah, bafa abinda kake tunani bane saboda ni ban taba zuwa gida nace ga halin da muke ciki dan haka ka cire tunanin komai a ranka ka shiga bandaki kayi wanka sai ka je kaji abinda yasa ake kiranka"


Ajiyar zuciya ya sauke ya Mike ya shiga bandakin, Bai wani Jima sosai ya fito ya shirya ya kama hanya ya tafi Kiran surikin nashi tana mishi adawo lafiya ya amsa da Allah ya sa. Da isar shi fadar maigari an tarbeshi hannun bibbiyu an kawo mishi ruwa da abin motsa Baki, saida ya natsu tukunna mai gari ya fada mishi abinda ya sa ya kirashi Kamar haka, "Na kiraka ne saboda ganin irin halin da kake ciki na yanke hukuncin baka daya Daga cikin gonakina na malaka maka su har abada ko bayan raina naka ne, ga takardun ma duk na canca na saka sunanka ya karshe maganar Yana murmurshi".

Hannunshi na karkarwa ya amshi takardu cikin murna da farinciki ya shiga mishi godiya da addu'o'i hawaye na zubo mishi, da kyar maigarin ya shiga kwantar mishi da hankali ta hanyar nuna mishi wannan abin ba komai bane, saboda sunyi zaman mutunci da amana da mahaifansa kafin su rasu Dan haka ya daina godiyar hakanan fatanshi kawai Allah ya sanya mishi albarka aciki ya amsa da amine da haka yayi sallama da maigarin ya wuce gidanshi sai murna yake. Yana zuwa gidan ya nuna ma matarshi Lami abinda ya samesu ta tayashi murna da fatan alheri.

Haka dai rayuwa ya dinga tafiya ya dinga noma a gonar tashi inda ya saka hatsi Alhamdulillah kafin shekara hudu arziki yana ta shigo mishi saboda yana Kai buhuhuwan hatsin shi kauyuka masu yawa Yana Saidaa, yanzu ya ma daina nomar  ya dauki yaran da suke mishi, saidai kawai a kawo mishi kudinshi yayi nisafi hata yanayin gidanshi ya canza komai da komai surikin nashi ma Yana yawan mishi alheri da mutanen gari Baki daya, haihuwa ne har yanzu shiru shekarar su takwas da lami har yanzu ko batan wata bata taba yi ba, Bai taba nuna mata damuwarta saboda Yana da ilimin addini sosai ya san cewa hahuwa nufin Allah ne, shi da kanshi yake kwantar mata da hankali watarana. A wani daren juma'a suna zaune ita da lami suna hira misalin karfe Tara na dara sai ganin lami yayi ta mike da sauri tayi hanyar waje tana kwarara amai cikin tashin hankali ya bi bayanta Yana mata sannu tareda mika mata ruwa ta wanke bakinta duk ta galabaita sai ajiyar zuciya take sauke ya riketa suka koma daki jikin nata zafi radau, Daren ranar Basu runtsa ba Daga ita har shi, washegari misalin karfe takwas na safe suka tafi asibiti sun yi sa'a Babu mutane daya mutum biyu kawai suka iske ya je ya yanko kati suka shiga domin ganin Dr, ya mata tambayoyi da Kuma yadda take jin ajikinta da ta mishi bayani yace mata ta je a dauki jikinta domin Kara tabbatar da zarginshi, bata wani jimawa ba ta dawo ya ce su tafi gida karfe uku na rana su dawo domin amsar sakamako.

Bai samu damar zuwa amsar results dinba sai wajen karfe biyar saboda bakin da yayi sun zo neman taimako Saida ya sallame su ya samu damar fita, Yana zuwa a office din Dr ya tura kofar tare da yin sallam ya amsha mishi Yana wasu rubuce rubuce a wasu takardu, ya nuna mishi kojerar da hannunshi ma'ana ya zauna. Yana gamawa suka Kara gaisawa ya mika mishi sakamakon tare da tayashi murna, cike da zumundi ya amsa ya bude Yana gode ma Allah da ya azurtashi da samun karuwa, likitan har dariya yake mishi kudi ya mika ma Dr din masu yawa ya fita ya shiga motarshi yayi hanyar gidanshi ko parking Bai tsaya yayi da kyau ya shiga kwalla ma lami Kira Yana fada mata irin abin farincikin da ya same su, dadi ne taji sosai ta Kara rungumeshi da kyau suka wuce daki, haka dai suka cigaba da rainon cikinsu har ya shiga wata na Tara ta sha wahala sosai saboda tunda safe da aka kaita asibiti sai wajen karfe hudu ta haifi danta namiji kyakyyawa dashi sak tamkar mahaifinsa sai washe gari aka samesu maigari ya aiko mata da wata tsohuwa ta zauna mata har tayi arba'in, ranar sunan yawon yaci suna Ahmed sun dauki son duniyar nan sun Dora mishi kowa kaunar yaron yake saboda yanada saurin shiga rai...




*Yan uwa ku bimu a hankali domin gane inda muka da so, yanzu labarin kankanin Hafiz muke bada wajen mahaifinsa✊🏾.*

 


*By 4 writers fasaha*

No comments