DUDUWA 24
_*📚HAƊAKA📜WRITER'S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:
_*🧞♂️NA DUDU🧞♂️*_
_(cigaban Duduwa)_
~24~
A ranar a zaune kulu ta kwana ko rintsawa batayi ba,bayan kukan da tasha idanuwan ta duk sun kumbura sunyi jajir ita bata kwanta baccin ba,bata kuma tashi yin sallah ba har asubahi ta gabato kulu na zaune ta haɗa hannu da gwiwa tana tunani.
da asubar fari mai gari yatashi cikin sauri ya faɗa madafa da kansa ya haɗa itace ya hura wuta ya zaro ƙatuwar tukunya yayo waje dan zuba ruwa ya je ya ɗora kulu dake zaune a ɗaki taji motsi a tsakar gidan tamiƙe da sauri ta fito ta na""
"waye anan ya tada wuta haka.
Nine nan uwar gida ruwa zan ɗora na gasa bayana dan nasamu sallar asubahi kin san shekara da shekara bayan ke motsawa jiki da jini.
ƙwafa kulu tayi a zuciyar ta ce,"dube shi kamar mutumin ƙwarai amma sai shegiyar ƙarya wai ni zai bunne da raina to tun kan *AI ƊARAN AKAI KWANƊI*,afili kuwa sai cewa tayi....
Bani tukunyar na ɗora maka ina zaka iya ɗora ruwa kamar wata mace macan ma ta gidan aure ai ɗora sanwa sai mu mata ranka shi daɗi.
dakin barshi na ɗora da kai na tunda ba wani aiki bane na ku zo mu gani ni kaina ɗin nan dakike gani tsaf zan tuƙa tuwo na mulla miya me ɗan karan daɗi kulu,mai gari ya zubawa kulu ido yana mai haske ta da cocilan ɗin hannunsa,matsowa yayi daf da ita yanda kowa ke jin numfashin junna ya ce""
Kulu mai kuma yasameki a fuskar ki ta sauya haka?
Ni kam babu abinda ya sameni sai alkhairi ka kawo tukunyar na zuba maka ruwan kawai.
na ce miki zan iya,shin wai me ma ya tasheki da wurwuri haka kulu.
hmmm kwanan zane nayi jiya sam ban rintsa ba gashi maƙota suka samu a gaba da iface iface kai kace yaƙin duniya ake bakuji ba yallaɓai.
ina zamuji munyi nisa da bacci amarya ce ma tayi kwanan zikiri kin santa akwai bada himma tanan ɓangaran.
Allahu Akubar, najiyo ta ai sai ƙoƙartawa take kamar malam suweɗi,bari na ɗora maka ruwan kar ayi kiran farko.
to da ko kin kyauta bari na ɗauko silifas ɗina na fito da botikin.
Kulu ta dubi ƙafafun mai gari daya tako babu silifas ta taɓe baki ta ce""
Hmmm ashe haka katako ba takalmi lallai abun nayi ne mai gari,ƙasa ƙasa kulu ta furta mai gari ya dube kulu da sauri ya ce""
me kika ce kulu?
cewa nayi bakaga takalmin naka bane ka tako haka.
auwo sauri nakeyi ne in zo in aza wuta ba ta silifas nakeyi ba maza ki ɗoran ruwan kin tsare ni da surutun da bashida amfani da sanyin asubar nan bari na duba amarya ko ta farka,mai gari ya wuce kansa tsaye ɗakin Duduwa yabar kulu tsaye tana kallonsa har ya shige ɗakin,kulu naganin mai gari ya koma ɗakin duduwa taje ta kamfato ruwa tazo ta ɗora masa akan wutar daya kuna tayi ɗakin ta tana mita ita kaɗai, ko da ta dawo ɗakin kasa zama tayi sai leƙen waje take ta taga dan taga wacce wainar za asowa tana ganin mai gari yazo da gudunsa ya juye ruwan a botiki yakai banɗaki ya zuba wani ya dawo ya shiga ɗaki bai jima ba duduwa ta fito mai garin na bayanta yana take mata baya har ya rakata makewayi ya kuma tsuguna abakin banɗakin yana jiran fitowar ta duk akan idon kulu data fara matse ƙwalla da gefan zaninta tana""
"Na shiga uku ni Hauwa kulu daga wannan sai wannan adake ka a hanaka kuka,cikin sauri ta toshe bakinta da kuka ya ƙwace mata tajanyo fulo ta tura kanta tana gunjin da ita kaɗai ke jin abinta.
******
Kwanci tashi har mai gari ya cika she kwanakin sa bakwai a ɗakin duduwa ya koma ɗakin kulu,karku so kukaga rawar kai wajan kulu har dasu goge kaushe dayin sabon kitsu da lalle,zannuwanta masu kyau na zuwa suna da biki ta fidda dan yiwa mai gari kwalliya abinka da ba'asaba ba har dasu jagira da janbaki aka ɓali gora kaɗan aka jefa a baki ana tauna shi a hankali kamar me tausayin goron kulu ta hakimce a gefan gado tana jiran shigowar mai gari,ɗan muskutawa tayi bakin windo yadda zata fara hangoshi kafin ya iso gare ta,ita ko duduwa yinin ranar chir a ɗaki tayi shi saboda ciwon kan daya isheta gashi sam bata son hasken rana datayi ƙoƙarin fitowa sai kan yasara haka dole zata koma ɗaki ta kwanta ta kasa cin komai bari sha har dare ya gabato.
Shigowa gidan mai gari yayi da sallama,kulu tayi charaf ta amsa tana daga taga tana gyara ɗaurin ɗan kwalinta daya ke shirin zamowa daga kanta,mai gari ya nufi ɗakin duduwa dayasa kulu miƙewa tsaye babu shiri tayi turus tana leƙo tsakar gidan bakin ta na faɗin"""
Kan bala'i gurguwa da auran nesa,au ni za'a saƙawa zaran da zai kwance ummm lalai tsahare kinyi gaskiya,bari naga iya gudun ruwan nasu.
tayi ƙasa zata zauna a inda ta tashi sai ji kulu tayi,tayi wanwar a ƙasa ɗan kwalin kannata ya sule kitson zanan hannunta ya bayyana dara dara sai ƙyalin mai yake yana sheƙi kamar sabuwar amarya,gyaran muryar mai gari ne ya dawo da kulu daga duniyar tunani data tafi sam bataji shigowar mai garin ɗakin ta ba tayi duru duru ta mike tana washe haƙora haɗe da mikar da hannayenta dukka biyun zanin jikinta ya kwance zai faɗi da sauri ta taro shi bakin nan a wangale sai cila hannn take gaban mai gari da yayi zuru dashi yana kallon baƙon yanayi.
ƙara dashe haƙori kulu tayi ta cila ƙafarta ɗaya tayi wani sifirin ta juya idanun ta kamar maƙallaru ta ƙara cilla ɗayar gaba idan yayi far ta ce da mai gari"""
""Sannu da zuwa da fatan kasame mu lafiya ƙallemun cikin zuciyata ga waje ka zauna na tunbatsa maka cikin ka da abinc me dagargza hanji da hantar cikin ka.
mai gari yafara ƙoƙarin ja da baya yana.
"",Ƙallu inna lillahi wa inna ilaihirraju'una....ya soma karanta ƙula ƙuzai yana tofawa kulu dake wani fari da ido tana jefa hannuwa gaba tana juyasu baya zanin jikinta har ciki ta kawoshi ta fara wata murguɗa tana takawa a hankula kamar ƙwai zai fashe mata,ganin haka mai gari ya fito daga ɗakin da gudu ya shige na duduwa ya banko ƙofa yana ta sallati shi kaɗai da sallallami kulu ta fito daga ɗakin ta daga chan nesa da ɗakin duduwa ta tsaya ta shiga kwarawa mai gari kira tana girkin tane yau koya manta ne zai kaiwa wata,yace da ita gashi nan zai fito amma ta koma ɗakin nata ta zauna yana tafe.
kulu ta daka tsale ta dire bil hakki sai mai gari yafito sun tafi tare shiko ya ce sam bazai fito ba haka kawai ta dagargaza masa hanji da hanta har da wani cewa wai ƙallemunta waya sani ko maƙalƙalo min zuciya zatayi ta kaini inda ban shirya zuwa ba gashi Duduwa bata nan bare ta taimake ni,innalillah yau gani ga Allah.
Abinda kulu bata sani ba tun shigowar mai gari gidan daya shige ɗakin duduwa ya isketa a kwance zazzafan zazzaɓi ya rufeta duba da rashin kasan cewar sa a ɗakin ya gurgura da taimakon sa ya rakata gidan inna yayi mata bayani yanda ya kamata,inna da murnar ta tace,"ai babu komai sun kwana tare inyaso da safe ta mai do ta da kanta,mai gari yayi godiya yamiƙawa inna ƴan magungunan daya saya ahanya ya dawo gidan ya shiga ɗakin kulu ya isketa a wannan safgar.
…………………Banɗaki dije ta shiga kanta tsaye babu Addu'a.................
_*By*_
_*Maman Dr*_
No comments