Breaking News

DUK NISAN JIFA 22

                          22


A yanzu abinda take ta shige da fice shirye shiryen auren yar uwarta d'aya cilo mace domin kuwa a yanzun auren Mami bai fi kwana biyu ya rage ba.

An bata wayarta, gidansu sawu ya dauke sai su tati kawai hakan ya sa take sha'aninta.


Kasancewar komai a kure yake zuwa sai kawai saki kadai zasu yi ita da kawayenta watau kayan fulani.


Sosai take farin cikin auren nan, shirintama yau zata koma gidan mahaifinta har sai bayan auren.


Tana ninke sauran kayanta ta kalli mamanta ta ce" Mama, a daina irin haka dai ba kyau, dan ita bata zo auren danki ba shine kema sai ki ce ba inda zaki je? Ai Abana ya zo, kuma Mami kwananta uku a gidan nan ko?"


Mama ta tura baki ta ce" Ke ni banma san shirmen me matar nan take ba, Allah na tuba da tsufana me zan tsaya yin shirmen kishi? To kishinma na me bayan na rabu da tsohon mijinta mai doro?"


Bilkisu ta zarro ido tace " Lalala mamana, walahi Abana bashi da doro, mama zankadin da shi? Uhum su mama ko dai ko dai?"


Tati ta bushe da daria ta ce "Kema kya fada wannan karfin hali da fada da wannan matar take, an ce ta koma dakinta ta ce aa bata san yaren ba kuma tana cakalkalar santalin habibinta "


Mama ta mike ta ce" Ban san ina bakinku ya koyi rashin kunya ba, aman ina ga zan kaura kusa da yarona ko zan daina jin zanceceku kamar an turo ku"


Daria suke mata har ta tafiarta dakinta


Sai da Bilkisu ta gama komai sannan ta shiga da dan sauri dan yiwa mamanta salama domin wannan tafiar a motarta zata yi


Mama ta dan kura mata ido ta ce" Walahi gabana ke cika faduwa mai gado ban san dalili ba, kuma kin ga yayanki ko? Ya ki ya zo ya dauki matarsa ko? Dan Allah yaushe ya taba yin kwana biyar yana aikin tiyata? Hum, kuma na rasa inda zan matse shi na kama shi"


Bilkisu ta ce" Aya mamana zai dawo da kansa ne, kin san fushi yake, idan ya saku zaki ganshi da kanshi ya dawo gareki, mamana ba zai iya nesa da ke ba bayan kina raye a duniya"



Mama ta yi murmushi ta ce" Gashi ke kina son ki koma wajen abanki? Bilkisu sai na ga kamar yanzun kin fi son sa a kaina ko? "


Bilkisu ta dora kanta a gefen kafadar Mama ta ce" dukanku ina son ku, ku din kune duniyata, lahirata, farin cikina Mamana"


Mama ta yi murmushi a hankali ta ce" Ki je, Allah ya kiyaye, kar a yi abinda za'a ce ba kunya kin san fa mutanenmu na gida, kuma in sha Allahu zan zo nima aman ranar daurin auren ba ana gobe ba"


Bilkisu cike da murna ta mana mata kis a kuncinta tana tureta tana komai ta fita tana daria


Yauma Tati sai da ta bata kudi sannan sukai salama ta shiga motarta ta tayar ta nufi gidan mahaifinta


Gidan cike yake da dangi, ana ta shagulgula tun yau kasancewar akoy fili da kuma dakunna masha Allah


Kowa sai sam barka yake da gannin Bilkisu, da yawa sun yi mamakin girmanta, da yawa na fadin Lalle jauro ashe yan matan biyu ne da shi


Ita dai sai da ta gaida mama sannan ta nufi dakin yar uwarta


A kwonce take idanjuwanta lumshe, kanta daure da dan farin kyalen da ta daure dan ya daina sasara mata, kafafuwanta du ta saka tsuma ta kukule dan ta ji dama damar dadatsa matan da suke yi


Da sauri Bilkisu ta karasa tana fadin" Subahannalah, Mami jikin ne ya motsa ko sakatar amarci ne? "


Mami ta kakaro murmushi ta ce" kin zo Balki am? "


Bilkisu ta zauna gefenta ta ce" Eh na zo, tashi na ji menene? Baki sha maganinki bane ko meye? Mama ta san baki da lafia kuwa? "


Mami ta kamo hannunta ta kai kusa da kirjinta a hankali ta lumshe idannuwanta ta ce" Balki am, kin san ina son ki kuwa? Ina son ki sosai yar uwata, na yi farin cikin samun kasancewa da ke na tsayin sati uku, ban taba fara'a irin haka ba yar uwata, ban taba jina da farin ciki madaukaki kamar irin yanda muke  baci tare ba, kin san wani abu kuwa? Da na dawo na kwonta ni daya sai na kasa yim baci, sai kawai hankalina ya tashi sosai har na ji kamar zan sike, Balki Am sai na tuna kwoncin kabari, na tuna kadaicin kabari, ya Allah ka sa mu samu wadatace mu hadu da mataya zama na alkhairi, Balki Am Allah ya raba mu da duhun kabari"


Bilkisu ta tsaya da murmushin da take tana kallonta, gani ta yi idannuwanta ai a rufe suke take bayanin nan, ga kuma hawaye a gefen idannuwanta


Da sauri ta ce" Ke Mami? "


Mami ta dan daga idannuwanta


Bilkisu ta ce" Meye haka? Tashi tashi mu tafi asibiti ko na kira yaya ne ya zo ya duba ki? "


Mami ta bude idannuwanta tana sakin murmushi ta ce" Ke dan Allah kawai ke motsi kadan sai asibiti? Ni barni baci ne nake ji sosai walahi "


Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya aman duda haka sai da ta kawo mata maganinta ta sha sannan ta tashi ta shiga shirya masu suturunsu tana labarin sai ta koya mata rawar filani


Washe gari haka aka wuni nanma ana shagulgula, ango ya zo ya gaishe da iyaye cikin shigarsa ta kamala, Umar yana da daraja mutane, ga biyaya ga kunya, a nan ne Laila ta ganshi take cewa" Kai wai da Umar mai waya ne angon? Kai masha Allah aunty ta yi dace domin Umar da kika gani kin ga yanda yan mata ke kai masa hari kuwa? Ko dan abin hannunsa ne? Ko dan kyansa ne? Aman ba ruwansa da sha'annin mata da fade faden nan, ke har shari aka so yi masa wai ko baya son mata sai maza, kin ga gashi zai yi aurensa shima"


Bilkisu dai sai murmushi take jira take ya fita ta bi shi ta tsokane shi.


Yana fita har zai shiga motarsa madaidaiciya mai kya tace "Ango ango, ango Umar na Mami bada kanka a sare ka je gida ka ce ya fad'i."


Yana dariya ya d'an nuno mata yatsa yace "Allah ya shirya ki Bilkisu."


Bilkisu tace da shi "Sai goben ko ina fatan zaka zo da k'arfe shida na safe dan ka shinfid'a tabarmu."


Yar k'aramar wayarsa ya jefo mata ta cafe yace "Yarinya kyauta ce ki kaiwa amaryana mu zanta"


Ai kam ihun murna ta sa tana ta k'ilk'ila dariya ta juya wajen yayanta da yake dariya shima tana fad'a masa hakan ya sa da sauri Umar ya shige motarsa ya tsere.


Nan suka shantake da yayanta sunna ta hira tana daria abinta cike da farin ciki.


Ba su laila suka bar gidan ba sai kusan k'arfe tara na dare, a lokacin ne ta raka su sannan ta tuna Mami.


Da yanayin tsokanar ta nufi dakin da Mami take a lab'e tana fad'in "Ke wallahi fitowa zaki yi ki sha iska ina dalili sun saka baiwar Allah lab'ewa a d'aka."


Yanzun ma Mami na jingine da garun d'akin idanuwanta lumshe.


Bilkisu tace "Kin yi sallah kuwa? " Mami ta gyada mata kai daga zaunen da take.


Bilkisu ta yi alwallah ta gabatar da shafa'i da wuturi sannan ta haye saman gadon.


A hankali ta jinginar da bayanta jikin garun ta kamo hannun Mami.


Mami ta zame ta d'ora kanta saman cinyar Bilkisu tana rintse idanuwanta da take jin tamkar ba nata ba dan kuwa wani irin nauyi suke mata sosai, haka kuka jikinta ya yi zafi sosai.


Bilkisu tace "Kin cin abincinki? Kin sha maganinki?"


Mami ta k'ara gyara kwonciyarta a hankali tace "Ina jin dad'in rabar jikin ki, barni na huta."


Bilkisu ta yi dan shiru hankalinta ba a kwonce ba da yanayin Mami na k'in son yin magana , ga kuma irin yanda baki d'aya jikinta ya kaure da zafi.


A hankali tace "Wai dama haka ake shiga idan za'ai yiwa mutun aure? Yana shiga haki na rashin lafia da rashin walwala? Yana zama kamar wani wanda zai haukace dan tsoro da fargaba? Kin fara bani tsoro auntyna, shin nima haka zan ji idan Allah ya nuna min ranar aurena?"


Mami ta d'ago kanta da k'yar ta iya buda idannuwanta ta sauke a fuskar Bilkisu, a hankali ta sakar mata murmushi ta dago hannunta na dama ta shafa gefen fuskarta muryarta cen ciki ta ce" Ina son ki sosai, ki yi ta yin biyaya ga iyayenmu kin ji? Sannan ki rage kukan banza, yanzun kuma ki min shiru na samu na huta."


Bilkisu ta sakar mata murmushin itama dan a yanda ta yi maganar tana dan jan hab'arta sai kuma ta maida kanta ta k'ara kifawa.


A hankali Bilkisu ke shafa gashin kanta da aka kwonce mata da niyyar sai a gobe za'ai mata kitso.


Itama wani irin nanauyan bacci ne ya fizgeta mai matuk'ar nauyin tsiya.


Bata tab'a babci irin haka a zaune a takure waje d'aya kuma bacci mai nauyin haka ba baccin cike yake da wasu irin mafarkai na abin al'ajabi, abin tsoro, ita kad'ai sai kakab'a daria take tana neman Mami dai bata ganta ba bayan tana jin maganarta a daf da ita.


Ji ta yi an shafa gefen fuskarta da wani abu mai danshi kamar ruwa hakan ya saka a hankali ta ringa buda nanauyan idanuwanta mai cike da bacci.


A fuskar mahaifiyar Mami ta sauke dubanta, lokaci daya ta ga Mahaifiyar Mami d'in ta sadda kanta, wasu mata biyu ne suka shigo a firgice suna nufo su.


Bilkisu bata gama wartsakewa da abin bacin da take ji wuyanta ya sangaye mata ta kasa motsa shi da kyau ta ga mamanta ta shigo itama a firgida sauri ta d'ora idannuwanta a kan hannun matar da aka ce ita ce mahaifiyar Umar ta saka hannayenta tana k'ok'arin d'aga Mami dake saman cinyarta.


Da sauri tace "Kai, menene? Kun ga bacci ne mukai mai nauyi jikin Mamin ne ya tashi ko kitson ne za'ai mata? Sai kuma ta kai dubanta wajen Mamanta ta ga ta yi baya ta fad'i k'asa zaune tana toshe bakinta da hannayenta bibiyu, sai kuma ta kalli Mama ta ga mama ta jingina da garu ta rintse idannuwanta kamar wace take shirin fashewa da kuka.


Da wata irin murya matar tace "INNALILAHI WA'INA ILAIHI RAJU'NE." 


Da sauri Mama ta juya sakamakon shigowar da Aba ya yi da wani irin sauri bakinsa da kalmar shahada ya nufo wajenda da suke.


Hakan ya saka Bilkisu zabura tana son mik'ewa tsaye daidai yayanta ya shigo wato HISHAM wanda ya kawo Mama 

Idanuwansa a kanta suka sauka, ya cire dubansa da sauri ya nufi wajen da Aba ke ce masa "Ka duba min ita Docter, innalilahi wa'ina ilaihi raju'ne wai da gaske bata motsi bata numfashi?"






          *Tamat.*



😔😔😔😔😔😔😔 Dan Allah ku k'ara hak'uri kun ji...haka salon labarin ya zo, kuma ba ku kuka ce a baku na kuka ba?☹️

No comments