DUDUWA 23
_*📚HAƊAKA📜WRITER'S ASSO📚 Follow this link to join my WhatsApp group:
_*🧞♂️NA DUDU🧞♂️*_
_(cigaban Duduwa)_
_*Godiya da jinjina ga ɗaukacin fan's ɗina na Duduwa musamman waɗanda suke ƙoƙarin yin comments a ko da yaushe ina matuƙar yinki mara iyaka, Allah yabar so da kauna yayiwa rayuwa albarka son so fisabilillah😘❤️😘*_
_*Spicial gift 💖 to the Mum Amnash,jinjina ga namijin ƙoƙarin ki sister ina godiya mara iyaka Allah ya bar so da ƙauna tsakaninki da Hubeey ki har gidan Aljanna❤️😍*_
~23~
Tsawa mai gari ya dakawa kulu,da sai da hantar cikin ta,ta kaɗa tsabar firgita ya ce""""
"Babu wani haƙuri tsakanin mu dake,duk abinda nasan zai faranta miki rai kulu shi nake ƙoƙarin yi miki dan kar nashiga haƙƙin ki,abinci sai wanda kika ga damar dafawa kici haka abinsha kullum akan tambayar damuwarki nake nasaka ki faran ciki,kuma ke yanzu da zaki tayani riƙon ku nayi muku adalci ashe ke ce me raba hankalina ki jefani a damuwa gidan ku zaki wuce tunda mumunan nufi gareki inyaso sai ya ƙare akan ki ke kaɗai,mai gari ya dubi kulu datayi duru duru da ita duk annurin fuskar sa ya sauya ya kuma ɗorawa da"
ki tashi ki koma inda kika fito ko baki ji yaren danake miki bane kin tsareni da ido.
durƙushewa ƙasa kulu tayi ta haɗa hannayenta dukka biyun tace""""Kayi mun rai dan Allah kabarni cikin ɗakina na zauna, nafaɗa maka insha Allahu haka bazata kuma faruwa ba sharin shaiɗan ne ranka shi daɗe.
babu ruwan shaiɗan acikin mugun nufinki da son zuciyarki da kishinki ya jawomiki,kuma Allah ne mai rayya ɗan Adam bani ba da zaki ce nayi miki rai ki tashi ki wuce kar na fusata na doke ki a gunnan kulu.
ka taimake ni ka rufa min asiri na tsufa a ɗakina yallaɓai karka tona ni diniya ta zageni dan Allah, ƴar uwata kisaka baki ya barni ko warkewa daga bugun danasha banyi ba wallahi yanzu haka bani da lafiya kuma ai kince nataso natayaki soya nama ko,ki saka baki dan Allah yallaɓai ya haƙura ya barni na zauna a ɗakina bazan kuma ba,kulu ta kwaɓe baki tasaki kuka mai ban tausayi,gwagwaron numfashi duduwa ta sauke haɗe da duban inda mai gari ya ke tsaya sai cika da batsewa yake ta ce dashi"".
"Tunda ta baka haƙuri ka haƙura mana ko ni da akayiwa sharrin bagashi na haƙura na yafe mata ba,bare kuma kai yallaɓai kawai ka bar maganar mu dai mun shirya idanma bata saduda ba ta cigaba dayi jiki magayi ita zatasha wahala ba wani ba.
kina nufin kin haƙura kin yafe mata.
Haba yallaɓai yanzun nan fa nagama faɗa maka na yafe mata mana.
To ai shikenan Allah ya yafe mana baki ɗaya sai muyiwa Annabi Salati goma goma,gaba ɗaya suka ɗauka da.
(S'A',W).
Suna iddar da salatin duduwa ta miƙe tsaye ta fito kulu ma ta biyo ta a baya wajan suyar naman har duduwa ta sunkuya zata fara aiki kulu ta daka tsalle ta dire bazata bar duduwa tayi aikin ƙauri ba tana amarya a dolle duduwa ta koma ɗaki ta barwa kulu aikin nan da nan ta gamashi tas ta ɗora shinkafa da jar miya ta sauke ta zubawa kowa rabonsa har da mudi mai gari ya fita ya dawo da fura da nono jingim a ledar ya miƙawa kowa nashi ya ƙara da sanar musu zaiyi baki da anjima da yamma suka amsa masa da to ya koma faddah aka cigaba da hira,koda yamman tayi duduwanka ta faɗa bandaki wankanta ta fesa ta dawo ɗaki tasaka tishait fara da ɗankwali da zani iri ɗaya turaren ta ƴan hamsin ta dangwali kowanne a ciki ta shafa ta kashe ɗauri ta goga janbaki da jagira har da ɗogo ta fito tsakar gida ta zauna abinta tana wake waken ta.
Kulu na ɗaki ta hango amarya zaune tasha jan janbaki da jagira ga uban ƙamshin daya zarto har ɗakin kulu ya daki hancinta wani abu mai ɗaci ya tsaya mata tayi saurin janyo ruwa a kofin silba ta kurɓa ta sauke ajiyar zuciya a hankali dan kar duduwa ta ji tayi shiru kamar bata gidan,Sallama akayo aka shigo mai gari da me unguwa sai malam liman suka faɗo gidan kai tsaye duduwa na ganinsu ta mike a fusace ta na.
"Haba me unguwa da liman haka sukum zaku wani faɗowa matan aure gida babu sallama,liman ina amfanin rawanin naka anyi girman kwabo kai da me unguwa aradu.
"Afuwa amarya ran gida ba laifin mu bane na yallaɓai ne don kafin mu shigo mun nemi yazo yayi mana iso yace duk kun shige ɗaka,gaskiya ne me unguwa laifin na ranka shi daɗi ne,amma ayi mana afuwa hakan bazata faruba nan gaba,liman ya furta yana duban mai gari da yayi zukuɗi dashi yana raba idanu,duban mai garin duduwa tayi ta turo baki tace.
Kaji bayanin da sukayi gaba idan katashi shigowa ka fara zuwa ka tabbatar da abu kafin ka zartar da hukunci.
in Allah ya yarda zan dinga shigowa na duba ina kuluwa ta shiga naganki ke ɗaya anan.
tana ɗakin ta a kwance kasan ta gaji da aikin suya da girki duk ita tayi mana yauwa kasaka mata albarka ma kamar yanda malam ƙarami yafaɗa idan matarka tayi maka abu mai daɗi ka shi mata albarka sai taji daɗin yin wanda yafishi,mai gari yayi murmushin jin daɗi ya ce.
"bari na bita har ɗakin nasaka mata achan ga baƙin mu nan a basu wajan zama,mai gari yayi ɗakin kulu kai tsaye, da sauri kulu ta kwanta ta rufe idonta kamar me yin baccin gaske mai gari yashigo ɗakin yaganta akwance da kamar ya tasheta sai kuma ya fasa ya jajjefa mata albarka da ƙarfi kamar yanda duduwa ta faɗi yana yi yana hangen amarya gaba ɗaya ƙamshin ta da kwaliyar sun wuce da mai gari har wani bokaɗa anci yake yana kuma ɗage kansa ran kulu a ɓace data ƙyallara ido ta hangeshi,mai gari dai yayo waje yana""
"Baci take baiwar Allah da alama ta gaji dayawa.......
ganin su liman yayi sun bararraje akan tabarma ga uban nama jingim a gabansu sai kawai suke suna shiwa duduwa albarka ita kuma sai tace,"kulu zaku shiwa bani ba dan ko juya cokali banyi ba,anan liman yake shaidawa duduwa rashin dawowar matarsa yaje biko yafi a ƙirga amma ƙemadade taƙi dawowa ƙarshe ma har zaginsa tayi.
Zaginka liman da kanta.
yasin da kanta ta zageni ido cikin ido wai bazata dawo ba in auro wata ita zawarcinta take ci da tsinke...
da bakinta ta furta haka.
hmmm tafi ga hakama indai Dije ce.
Nan duduwa tace masa ya jira nan da gobe zai ganta.
murna da godiya liman yashiga yiwa duduwa tace babu komai ta miƙe ta koma ɗaki ta barsu da mai gari suna kwasar nama.
Bayan su liman sun tafi mai gari yarakasu bai shigo gida ba sai dayayi sallar isha yaje gun Ɗan Asabe ya sayo lemo da ayaba ledar biyu ya dawo gidan,sai da yafara shiga ɗakin kulu ya bata nata sukayi sallama ya nufo ɗakin duduwa ya isketa tana gyaran shinfiɗa,sannu da zuwa tayi masa ta amshi ledar hannunsa ta ajiye ta ɗauko ruwa tabashi ya karɓa da murmushi ya shanye dukka suka shiga hira suna dariya a haka har aka fara cinye amarci duduwanka taji babu sarki sai Allah ta shiga kwarma ihu da surutai wanda ya tashi kulu zaune ta kasa tsaye ta kasa zaune sai ƙwafa take da yarfa hannu da abu yayi abu kuka kulu tasaka har da kaiwa hannunta cizo ta miƙe tsaye ta janyo fulo tana kuka tana toshe kunne😳
*Aradu kulu na da kishi bata sadudan ba ina ji🤔*
_*By*_
_*Maman Dr*_
No comments