Breaking News

DUDUWA 18

  ~18~

'Alhamdulillah,anyi taro an ƙare lafiya da daddare gida ya cika maƙil da ƴan kai amarya,abin mamaki mata kamar titilo su akeyi kowa kataɓa,amarya duduwa zai raka ɗakin ta har da ƙawar kulu Tsahare data turo ta ganin ƙwaƙwaf taje ta sanar da ita me aka zubawa duduwa a ɗaki taje ta faɗa mata,,duduwan ka ta fito daga wankan sulɓi za aje a shirya ta kawai taja dinga ta tsaya tsakiyar mutane tana duban kowa da ido,har kusan minti biyar daga chan ta tintsire da dariya ita kaɗai kowa idon sa zuru akan ta ta furta"""


"Inna......


   inna ta matso da sauri kusa da duduw ta ce"


"Ma'u me kuma kika tsaya yi anan ana shirin kai ki ɗakin ki,yi maza muje ki idda shirya wa,murmushi duduwa tayi ta kuma cewa.


inna.....


A karo na biyu inna ta kalle ta fuska a cukule ta ce""""

          Ke bana san shashanci idan zaki wuce a shirya ki a miƙaki ɗakin ki,ki wuce in kuma kallon jama'a zaki tsaya yi to gaki gasu nan wasu ma basu shigo ba suna waje chan suna jira ai sai ki bisu.


ƙafa duduwa ta buga a ƙasa da ƙarfi,yawancin matan gurin kowa sai da cikin sa ya murɗa garin gulma sun kawo kansu masifa,ko wace sai ayyane ayyane take a zuciyarta,a fusace duduwa ta ɓarke da rawa tana""""


   "Ga sarauniya janɓera,Aa,Aa...


"ɓakuci na bayanta,Aaa,Aaa...


"Munafukan sun taru,ihmmm,ihmmm....


"Sai ku kwashi rabon ku,ihmm,ihmmm...


innalillahi daga me kukan jakuna sai me kukan akuya da mage,fitsari kuwa haka yadinga bin siminti yan wucewa ko wacce ta dashe baki sai ihu take da neman agajin gaggawa kar ashilla da ita,Duduwa ta kuma kecewa da dariya ta ce"""


"""""'Ƙafafuwa ko hannu.........


"ƴar tsere aka shiga yi daga wannan ta miƙe zatayi waje sai wannan ta kamo ƙafar wannan dan kar wata ta fita ita a wuce da ita,cikin minti goma gida ya ɗaɗe babu kowa sai uban tarin silifas birijik a tsakar gidan wasu ma har mayafin su da ɗankwalaye suka bari dan firgita,inna kuwa banɗaki ta faɗa ta banko ƙofar ta danne da baya tana sumbatu ita kaɗai a ciki,duduwa ta waigo ta waiga taga babu kowa a gidan sai sambatun da inna take yi a bayi tana.



"Abashiya wa Abashe Ashiru wa duduwatun,chan kuma sai kaji ta ce""


"fidduniyatin......



Tsabar dariya sai da Duduwan ka tayi zaman dirshen a ƙasa,inna ta kuma furgicewa jin dariyar da duduwa ke ɓaɓukawa da ƙyar duduwa ta miƙe taƙarasa bakin banɗakin ta ce da Inna.


      ""Haba kakale ta lafiya ta ƙalau nake wallahi naga munafukai sunfi mutanan kirki yawa a gidan shi yasa na kora ƴan banza gidajen su,duk me son ganin ɗaki ya biyo ni daga baya ya gani,ki fito ki kai ni ɗakina inna masoyi mai gari yana chan yana tsimayi na.


"ki rantse da Allah ke ɗin ce Ma'u,nifa kakar ki ce ni ɗinma sai an haɗa dani an gabza kamar baku san da sanayyya ba wayyo Allah ni kam ina ganin hau....



Haba inna, ni ce fa duduwarki ki fito kuma ki ganewa idanun ki.


na jima da jin haka, kuyiwa Allah ku barni nasha ruwa kar ku ƙarasani.


"Da sune fa kin san da tuni sun biyo ki har makewayin.........kan duduwa ta rufe bakinta har inna ta sheƙo daga bayi da gudu duk fuskar ta zufa kamar wacce tayi wasa da ruwa,idon ta duk yayi zuru zuru ta ce.


"Asama'u ke ce?



Ni ɗin ce mana gani nan agabanki,aradu inna akwai ki da ɗanbanzan tsoro sai kace farar kura.


ƙaniyar ki,ke ɗin ce ai dole aji tsoran ki,yanzu tsakani da Allah kina sane kika firgita bayin Allah nan daga sun zo rakiya.


munafukai ne inna har da tsahare aminiyar kishiya ta kulu.


na shiga uku,har kulu ta zama kishiyar ki duduwa tun bamu kai ki gidan mai garin ba .



yo ba an riga an ɗaura auren ba ai kishiya ta ce halak malak,ni gaskiya inna kuyi sauri kar mai gari yagaji da jirana.


haka hakan ki,nace haka hakan ki,kaga mara ta ido,dariya duduwa tayi ta ɗora da"""


Inna tawa, ta kaina ni banma ce ki yafeni ba haka da za'akai Sahura ɗakin Sale naji tana cewa uwale""!



"Uwale ki gafarce ni,na tuba uwale na tafi ɗakin aure sai wata rana idan da rai da rabo.


dariya sosai inna ke yi harda ɗan dukan duduwa, gaba ɗaya kuma inna sai taji tausayin jikallan ta gashi zasu rabu yau ko da yake ma babu nisa a tsakaninsu dolle ne nayi kewa Allah sarki rayuwa,inna ta matse ƴar ƙwallar ta,tayo hanyar waje.

     Maƙota inna ta dinga bi tana janyo tsofaffi ƙawayen ta,wasu sun zo wasu ko basu zoba dan sunji abinda ya faru da ƙyar aka samu tsofai guda huɗu suka saka duduwa agaba suka raka ta gidan mai gari babu buɗa bare waƙa har suka shiga gidan da sayyadar su,duk wata al'ada da bidi'ar ƙauyen si da aka gabatar akayi siyan baki liman da me unguwa suka fadda kuɗi na dukan kuɗi har dubu biyar suka miƙawa tsofaffin,daga nan suka ajiye gasassun zakarun da aka gasa tun safe aka banƙare aka gasa da dakakken yaji me ɗan karan daɗi suka bar Duduwa da angon ta mai gari a ɗaki,,innalillahi kar kuga yanda Hajja duduwa ta duƙufa akan zakaru ko baki mai gari bai rufe dayi mata bismillah ba ta duma hannu ta fara kaiwa cikin ta kamar bata taɓa ci ba,mai gari ya koma daga baya ya zuba mata ido yana kallon ta chan kuma yasaki murmushi me nuna farin ciki.


  Ko da duduwanka ta gama buroshi da naman zakaru mai gari ya shigo da ruwan randa me sanyi ya zuba mata ta shanye ya ƙara zuba mata wani akofi ta ce"Aa ya bata babban kofin gaba ɗaya shi zai isheta hakan kuwa akayi ya miƙa mata ta kwankwaɗe shi gaba ɗaya ta ajiye,Alwala ya umarce ta da suje suyi ta tashi bokaɗai bokaɗai suka fito,,shiya zuba musu ruwan alwalar abuta ya saka mata kujerar tsuguno ta zauna tana ta dashe haƙora sukayi alwala suka koma ɗaki danyin sallah,bayan sun idar ne mai gari ya jima yana kwarara addu'a kana suka shafa gaba ɗaya ya juyo ya kama kan duduwa da zumar yi mata du'a'i ba shiri ta fusge ta miƙe tsaye tana hararar sa nan da nan ya soma Addu'a akafaice yana hura mata inda take,chan kuma ta haye ɗaya gadon ta kwanta bacci me nauyi ya kwashe ta,batayi wani nisa dayi ba ta fara wani gurnani kamar zaki tana nishi a daƙile mai gari ya zaro ido ya haye ɗaya gadon da gudu ya naɗe babbar rigarsa da hannun rigar da dogon wandon ya zauna da charbi a hannu yana kwara Addu'ar da duk ta faɗo masa baki har aka kira sallar asuba ya diro daga gadon da gudu ya fito daga ɗakin yayi masallaci ko alwala bai ɗaura ba................













_*By*_

_*Maman Dr*_

No comments