DUDUWA 16
~16~
Da isar su inna gidan mai gari suka tadda me unguwa da malam liman da wasu baƙi zaune a gefansa sai faman sannu suke masa,ashe me unguwa har ya garzayo ya kwarkwarawa mai gari zuwan nasu Duduwa,da shigar su gidan suka ga an baje tabarmi kusan guda goma sha an ajiye daron ruwa da moɗa sun kai talatin ga tarin shin kafa da wake da dakakken yaje a ajiye da aka daka,kamar masu shirin wani hamshaƙin taro,"inna da duduwa suka zauna daga chan gefe mai gari ya rarrafo da rarrafe inda suke yana"""
"Marhabin bika, lale lale da zuwan iyalan Amarya duduwa,muna farin ciki da zuwanku da fatan kun iso lafiya ga guri ku zazzauna.
daga inna har duduwa sororo sukayi suna kallon mai gari yana durƙushe me unguwa ya kwaɓe baki ya ce.
"Ranka shi daɗe daka zauna kar ƙafafuwanka su gaza.
Waya faɗa maka baƙi basu zauna ba mu ƴan gida zamu zauna, idan kuma akayi rashin sa'a muka zaune a kansu muyi yaya dasu me unguwa,ko so kake a zaizaye mana mazaunai mu dinga kashi ta baki babu dare babu rana ahir da wannan maganar idan sarakai suna waje ba'afiya ɓaɓatu ba,kaji ni,"me unguwa ya ƙunshe dariyar sa a ciki ya ɗora da".
'Na jika da kunnan basira yallaɓai maganar ka gaskiya ce dan bamu san iya yawan dasu ka zo ba,ga mazauni duk ku zazzauna baƙin alkhairi dana ƙasa da na saman duk muna marhabin da isowarku,me unguwa ya ƙare batun sa yana ms duban Duduwa data zubawa mai gari ido sai murmushi take aika masa ya ce""
"Allah ya taimaki Uwar ɗakina mata a wajan mai garin garin kanwa,Allah ya taya miki sha gayya sha aiki muna muku marabin da jama'arku baki ɗaya, ya nuna daron ruwan da ke ajiye a gefe"
""kunga duk wannan daga cikin kyauta tawar muce ayiwa mutanan barka da isowa......."kaga me unguwa ba surutu ya kawo mu ba,muyi abinda mukazo yi,a cewar Inna.
to ai sai a fara,malam mamuda ku matso mana ga baƙin namu sun iso,sauran ba'a ganin su sai dai su su ganmu.
"Ikon Allah yanzu yallaɓai waƴan nan ne bakin namu duk kallabi na akan su ba rawani ba,dama mata na ɗaura aure ne,in tambaya?.
malam mamuda kenan idan kaji tarihin bayin Allah nan sai ka zubda musu da ƙwallah Allahu akhubar kabiran,wato dai su ɗin nan daka ganibasu da ko ƙwayar dangi a cikin garin nan sai mu damuka zama uwa da ubansu idan bamu tausaya mun rungume su ba, to suwaye zasu zama nasu,shiyasa nace ayi abin tuwona mai na ni da Hajjaju makkkatun wato Duduwatun malam mamadu,mai gari ya ƙare maganar sa yana mai dashe haƙora,malam ma muda ya daki saman tabarmar dayake kai ya ce.
"A gaskiya bazan iya maganar aure da kallabi ba idan ba rawani nagani ba tofa sai dai suje su sami wani shaƙiƙen maƙocin su yazo ayi maganar dashi,amma sam ba dani ba gaɗa a lahira.
Aa malam mamuda ina tausayawa rayuwarmu,"dakata yallaɓai mufa ba ɗaurin aure ya kawo muba munzo ne akan ko zaka amince ka auri duduwa da sharaɗin............
"Wallahi tallahi,na rantse da Allah nama amince tun shekaran jiya da me unguwa ya tsegunta mun,nifa idan ma ban auri Duduwa ba bazan iya cigaba da rayuwa ba,nan da nan mai gari ya fara matsa ƴar kwalla yana face majina a gefe,me unguwa ya ce.
Haba ranka shi daɗe idan kana kuka mu kuma me zamu yi, wazai tsawatarwa da wani mu da kai.
hmmm bari dai me unguwa kukan na dole ne bakaji yanda nakejin gemun nan nayimun bane shi kaɗai zai tarwatsa mafarkin da na daɗe ina yi,idan Hajja duduwa tace bata son shi nayi yaya da rayuwa ta.
bama zata ce ba yallaɓai shima gemun akansa muka zo.
Alhamdulillah,inna shi kuma gemun me yayi muku?
babu abinda yayi mana,dama acikin biyu zaka zaɓi ɗaya"ko ka zauna da gemunka ko kuma auran duduwa ba gemu.
Ni kam inna ko yanzu ashafa fatihar idan har gemun nan zai bar fuskata,mai gari ya dubi su malam mamuda fuskarsa kamar zai kuka""""
""Ku taimake ni malam mamuda,malam liman bakace ko mai ba dan gyatumar ku,ku shafa mana fatiha ga kuɗi chan na sadaki ko
wa ya shaida yanzu.
Aa,mu ba sauri mukeyi ba,tunda har Allah yasa ka aminta to ai ba matsala,ku tsaida rana mu kuma muje mu samu waliyin da zasu tsaya mana.
'Yauwa to tsohuwa kin zo wajan danake ɓiɗar azo,wato tunda kun furta zaku samo waliyin da zai tsaya muku to mun bada nan da mako ɗaya,rana ita yau jumma'a kenan ana idar da sallah a shafa fatiha.
wannan magana tayi malam mamuda,inna kinji yanda wakilai na suka shaida.
Naji yallaɓai hakan yayi dai dai da namu shirin,muma har ma kintsa Allah ya taimake mu gaba ɗaya.
"Amin,kowa ya amsa inna tace da duduwa ta tashi su tafi.
Haba inna ya kuma zaku wuce ku barni da ciyawa a gemu,nafa rantse zan aure ta,malam liman kasa baki..........
"Niiiiii lalalala wannan batu yafi ƙarfina ranka shi daɗe sai ku manya,inaaaa kai sammm aradu ni zan wuce idan an hattama Allah ya kaimu juma'atu babbar rana na ɗauki nauyin goro da alewa ni zan bada kai na haɗa har da sadakin ma Allah yai mana me kyau..
gaba daya aka kuma amsawa da.
*"AMIN*,
malam liman ya suri silifatun sa ya ɗaye da sauri har da tuntuɓe a hanya.
mai gari ya sake duban inna ya ce"""
"""Gemun nawa fa....
ya furta yana riƙe da gemun sa,inna ta dubeshi ta ce"
munji da zaran mun fita zaka nemeshi ka ras.,kafin su inna da duduwa su baro idan mai gari sai da aka ƙulla yarjejeniya akan duk abinda duduwa keyi a gari ta dena idan har tana son mai gari,ta buɗe baki tace""ta dena amma idan aka sake aka taɓota tofa wannan magana babu ita a lallaɓata kowa ya zauna lafiya a taɓo ta garin kanwa ya tashi daga aiki,da jin batun na duduwa mai gari yace zai tara taro na musamman wa jama'ar gari su shaida maganar hajja duduwa amarya wa mai gari kishiya a wajan kulu.
..........Kwanci tashi har yau juma'a ta zagayo duk wani shirye- shirye,ɓangarorin biyu sun gudanar dashi biki sosai aka shirin yi da duk wani mutum dake cikin garin kanwa sai ya shaida har da maƙoftan su,magana ta shahara ta bunƙasa a gari wannan guntsawa,wannan,wanchan fesawa wanchan,har zance ya dira a kunnan Kulu,daga ji ta daka tsalle ta dire ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,zage zage da surutai ba kai ba gindi,haka akaita tausar ta ana bata baki tayi maza ta koma kar a ɗaura auren duduwa ta riga ta shiga gidan,buɗar bakin kulu ta ce.
"Ai na yafe,Allah ya haɗa kowa da rabon sa,dama shekara nawa,babu ɓari babu jego,kai ko ɓatan wata ban taɓa yiba,su je chan su ƙarata dangin junnu,Allah yasa gaba,gaba ta soye shi ta baiwa muƙarraban nata su cinye kowa ma ya huta😂😂😂😂😂😂.
_*SU KULU AN TAƁA KISHI,YANZU AKA FARA KU GYARA ZAMA TARE DA SAMBAƊA MIN COMMENTS FAN'S ƊINA INA JINKU HAR CIKIN❤️ƊINA🥰*_
_*By*_
_*Maman Dr*_
No comments