Breaking News

DUDUWA 14

 _          _14_

A wannan rana kusan gaba ɗaya jama'ar dake garin kanwa a zaune suka kwana in kaga mutum na bacci to yaro ƙarami ne ko kuma bacci ɓarowo yai awon gaba da mutum,masu sana'a,kuwa sai haƙura sukayi kowa ka kalli idon sa yai jajir tsabar rashin baccin da ba'asamu ba.


       "Tsaye Dije da yara suke a chan bakin rumfar ɗakin yara an rasa wanda zai ƙarasa ɗakin malam liman ya dubo da rai ko ta Allah ta kasan ce,sunyi jigum jigum a bakin ƙofar Dije na dafe da kuncin ta na haggu daya sha mari har kumbura yayi dan azaba ta kalli Ya'u ta ce.


"Ya'u ka leƙa man ka dubo mana malam kaga ko lafiya har hantsi ya doso bai fito ba shiru ga cikin mu na kiran ciroma da alama yau dai garin ba walwala ,"Yasin Inna ban zuwa chan da nan ga Adamu shi yaje ya dubo mana sai ni zaki aika,,harara Adamu ya jifawa Ya'u ya ce masa.

"Kaji ɗan rainin wayo kai meya hanaka zuwa dubo liman ɗin ko dan kaga bana magana,Adamu ya juyo ga inda Dije ke tsaye.


"Inna ke kiji ki dubo shi tunda har kin ɗanɗana asabar mutanan ɓoye ai idan kin koma yanzu babu abinda zasu yi miki kin riga kin zama ta gida,""gidan ubanka na zama kai kaje ka dubo kana ganin yanda kunci na gaba ɗaya ya tashi ya kumbura kamar fanke zaka buɗi baki kace naje tunda uban ku ne banawa ba kowa ya zauna ai bani yunwa da ƙishi zasu illata ba nakanyi mako guda ban saka ƙwayar dawa a baka ba bare na kwana ɗaya sai mu taru mu tsaya muga inda tsaiwar zata kai mu matsoratan banza matsoratan wofi,uban naku kun gagara ƙwatoshi tun jiya bare yanzu da gari ya waye.

    Wani abu suka hango ya turo kai daga ɗakin liman,da kokawa da ture reniya sukayi cikin ɗakin suna ihu da kururuwa, da rarrafe malam liman ya fito daga ɗakinsa kamaninsa gaba ɗaya sun chan ja,idan baka ƙura ido sosai ka dubeshi ba bazaka taɓa gane malam liman ba ya rarrafo ƙofar ɗakin da su Dije suka shiga suka rifo da yara,dukan ƙofar malam liman ya shiga yi da muryar sa data dishashee kumatun gaba ɗaya sun kumbura tsabar mari ga leɓan sama da naƙasa da sunyi lahu lahu magana idan liman zaiyi sai ya daƙile murya yanda leɓunan bazasu gogi junna ba,hakan kuma muryar bata fita,idan zai ce"""


 Nine,sai dai malam liman kaji yace.


""Shune.


Haka ya ringa buga ƙofar yana"""


      "" Shune, shune Diniiii.


Wannan magana ta liman ita ta ƙara razana Dije da Ya'u da Adamu suka haɗa baki suna ihu suna.


    "Wallahi Basu ba ne.


Malam liman yaga sun ƙi buɗe ƙofa ya tara ƙarfinsa waje ɗaya yazo dai dai windon ɗakin ya miƙe,yana miƙewa Ya'u na duban windon,nan da nan Ya'u ya kwarma ihu yana.


""Ga sunan inna ga Sabuwar halita, yayi bakin ƙofa da gudu ya buɗe ƙofar zai fito kenan liman ya baje a ƙasa ya ɗafo ƙafar Ya'u daya saki kashi a wando yana.


"La'illaha illallahu inna kashina aradu ya bushe,,,daga cikin ɗakin Dije tayi ƙarfin hali ta rarimo katakon karaga ta makawa liman ya baje atake a gun ko motsi baya yi,sai da Dije ta janyo Ya'u daga jikin fuskar liman,ta kwarma uban ihu haɗe da rugowa da gudu wajan da liman ke kwance tana"


"Malam wayyo Allah malam karka mutu ban san kai bane malam,jama'a ku taimaka mini malam katashi dan Allah,kuka Dije keyi sosai Adamu nayi,shi ko Y'u tunda yaga Dije na jansa ya sume bai san inda kansa yake ba har yanzu da Dije ke kwarma ihu da kuka.

      A hankali liman ya buɗe idon sa bakin ma ya wangale yana.


"luwa,luwa Dine luwa dan cha.


Da gudu Dije taje ta kamfato ruwa a roba tazo kan malam liman tana zuba masa tana zubda hawayen daɗi da Allah yasa bai mutu ba,nan da nan malam liman ya cika cikinsa dam da ruwa ya kauda kansa gefe,da sauri yace.


"Ta gani na jamna.


Adamu ya kamashi da taimakon Dije suka jingine shi jikin garu ya zauna,duban su yayi ya fashe da matsanan cin kuka yana.


"wayyayi naca wahaya,naca mugun wahaya Dinee....


Malam me yasamu bakin ka maganar ka gaba ɗaya bata fitowa na shaga uku ni Dije.


Wahaya naca Dine,ki gaca mun jicina duk ciwo yana muni..........,da gudu Dije ta miƙe taje ta hura itace ta ɗora ruwa akai tana hura wuta tana zubda hawaye tana duban liman da gaba ɗaya halitun fuskar sa suka chan ja..



.........



"Innar Talatu ce da baffa sai yaya jauro zaune a ɗaki suna kokawa junna akan rashin talatu da akayi ga kuma abida ya faru jiya da babu wanda yasan me ya wakana sai wanda abin ya shafa,,suna cikin hira sukaji ihu a ƙofar gidan su,kan su kai ga motsawa har an yaye labulan ɗakin an turo kai ana''


"Baffa na nan,da Inna,lah yah jauro ashe duk kuna ɗaka.........


     


zumbur innar tallatu ta miƙe tsaye tana.


""Baffa wajanka aka zo bara na wuce nabaku waje,"Ni ma kam inna jira ni mu tai tare,jauro ya mike zasu fita subar baffa,baffa ya miƙe da saurin sa ya na.


"Wa nake tsimayi kamar talatu,,"ni ce baffa yasin ni ce,talatu ta amshe zanchan cikin hanzari.


   Fitar da Inna da jauro da basiya ba kenan suka juyo suna ƙarewa me rantal ɗin kan ido,da mamaki Inna tace.


Tallatu!!.........



Na'am inna.


Da sauri inna ta rungume talatu sai kukan daɗi,ita tama talatu ta kwaɓe baki tanayi sai baffa ma ya matse ƴar kwallar data taro a gefan idon sa, shi ko jauro matsawa daga chan baya yayi yana kallon talatu ya dubi fuskar ya dubi salsal ɗin kanta dake wani sheƙi kamar an narka basilin ya dubi baffa,shi har yanzu bai gamsu talatu ce ba .




------------



""Inna lafiya kika tuma uban kaya haka a kanki.


Wake magana a nan wajan.......


Duduwan ki ce inna, ina karin kumallo na yake,inna ta buɗe bargon data rufe kan ta,ta dubi duduwa data tsaya shirm da ita a gaban gadon ta tace""shin wai ina kika tafi a daran jiya na farka ban ganki ba,anya duduwa anya kuwa.


Kai kaji inna da wata magana to anya ɗin me ki fito da abinda yake ranki ko nasaka a fito dashi ta dolle..


Ni yasin ban barin komai a cika na ki faɗa musu ni kakar ki ce jiya haka suka dinga safa da marwa a kai na da Allah yayi da ƙarar kwana da yanzu sai dai labari bazaki dawo ki iske ni ba.


Dariya duduwa tayi tace""


"Wai inna ihun su lawwali har gidan nan yazo,amma ɗan dunƙule ya aje abun faɗe a garin nan dama ina wajan aradu da anyi shegiyar,ido a waje inna ta sake cewa..



shi kuma waye ɗan dunƙulan duduwa.



Tab wani aboki na ne amma yau ki shirya tunda kina son sanin waye zaki ganshi ido da ido,tsulum sai ga inna a ƙasa ta diro daga gadon ba shiri tayi waje tabar duduwa na dariyar mugunta.




..........""Hasken ranar daya ɓulo ta saman kwanan ɗakin,shiya yayi sanadin buɗe idon kulu daya daki fuskar ta,,,nan da nan kulu tamiƙe zaune da sauri ta waiga gefan data san mai gari yana wajan,ai ko ƙarasa waigowa kulu batayi ba ta miƙe a sitin ta haye kan gadon ƙarfen dake daf da ita ta saki wata iri yar ƙara data tashi mai gari dake kwance bakinsa cike da gashin baki,duk an rantale gashin kan da ƙasumbar da gemun da girar an tara masa a baki daya fusgoshi da hannu zai watsa sai dai kaga gashin ya koma bakin ya zauna kamar yanda yake har yafi nada yawa,mai gari ya fara kwabe baki zai koka ya dubi kulu da ita ma kukan take tana..


""Bun suru,yallaɓai bunsuru a ɗaki..........







_*By*_

_*Maman Dr*_

No comments