Breaking News

ZAN FASA KWAI 5


 *ZAN FASA KWAI*

          *Page 5*

........ Hajiya ta dube shi da mamakin wannan magana ta izzatu.

"Da gaske ne abdulkarim"?

Yayi murmushi Yana mamakin izzatu akan yadda take kokarin butulce mishi

"Hajiya mu rufe maganar Nan don Allah babu amfanin da tado ta zaiyi Mana mu barwa Allah ikon shi kawai sai mu zauna lafiya.....

"A a abdulkarim idan har kasan kana da matasala kar ka rufeni fada min sai anema maka magani tunda Ubangiji Bai Saukar da cuta ba sai da ya Saukar da maganin ta.


"Haka ne hajiya to anema Mana sai muyi amfani dashi Ni da izzatu........


"Adalilin me da Kare zai dauki Dame? Ai ba a taba karan ta min akan komai ba sai sai akan magani? Kuma Ni meye hadina da Shan maganin ka na matsala? Kai ne nasu Kuma Kaine da matsalar Nan meye nawa? Ni fa kasani wallahi na gaji da wannan zaman cutar don nazo karshe wallahi da zaka sauwake min zanfi farin ciki don yanzu Babu wani amfanin Zama da Kai 


Hajiya ta Mike da Shirin komawa

"Zansa mas udu ya karbo min maganin sai kuyi amfani dashi mugani Allah ya sa mu dace

Ya Mike shima suka fito don yiwa hajiya rakiya inda direban ta ya ke 


Izzatu ta rako hajiyar da harara tana Jin kadan ya rage ta make tsohuwar komai zai faru ya Dade Bai faru ba.

Hajiya ta wuce shi Kuma ya dawo inda ya isketa sai cika da batsewa takeyi

Ya soma rarrashin ta Akan tayi hakuri su barwa Allah ikon shi akan maganar haihuwa......


"Saboda ka Gane Kai ke cutata shiyasa zakace inyi hakuri Mana Amma ai ka Dade da sanin irin wulakacin da danginka harma da hajiyar ka suke min suna zaton nice da matsala har suka kasa yi min uzuri sai yanzu da Allah ya haska min na gano ka shine Nima za a cuceni? To kasani Kai namiji ne komai Daren dadewa zaka iya samun haihuwa Amma Ni da lokaci na ya wuce to yafa wuce kenan  so abinda yafi kawai mu hakurewa juna don Allah ka sahale min aurenka tun lokaci Bai kure min ba.

"Ni dai nasan duk kokarin me kokari Bai Isa ya samo abinda ba Rabon shi ko ya samo din kuwa zai sulale ya barshi  don ba Rabo bane don haka Zan Baki shawara ki roki Allah abu mafi ALHERI a Rayuwar ki sai kiga ALHERI Yana samunki a ko ina Amma son zuciya Babu abinda yake haifarwa sai bacin zuciyar don haka don Allah don Annabin sa ina so daga yau ke daga yanzu ma mu rufe babin maganar haihuwa Ubangiji yayi Mana baiwa me yawa don Bai bamu haihuwa ba sai mu butulce mishi? Ina rokon Allah yasa Rashin haihuwar da Bai bamu ba ya zamo sanadin SHIGA ALJANNAH shi kenan magana ta Kare daga yau.


Abinda ta kawowa ranta shine kawai Yana son taci gaba da Zama dashi Yana cutar ta tunda yasan shine bashi haihuwa 

Bata tanka mishi ba Amma fa tana Jin ba zata yarda da wannan cutar ba.


Tundaga wannan Ranar sai zaman lafiya ya wanzu tsakanin ta da dangin miji su shafa duk da ba SHIGA sabgar su take ba haka ma hajiya Bata Kuma zuwa gidan ta ba inda Kuma ak yayi kwangilar shi ya gama ya samu ALHERI me yawa yayiwa hajiya da danginshi hidima itama izzatu ya Bata kasonta Wanda me yawa Wanda duk in yayi kwangila ya gama dama ka Ida ne sai ya Bata sai dai awannan karon Bata amsa ba tace ta gode ba zai siyi Ra ayin ta ba idan dai har son burgeta yakeyi to ya sauwake Mata auren shi ta Kara gaba inda itama zata haihu

Yayi murmushi Nan ma rarrashin ta yayi Yana Bata hakuri shima tayi shiru ba don ta yarda ko ta aminta ba.


Ranar wata alhamis ta kwanta barci inda tayi wani mafarki Wanda shine silar zamowa karshen auren su da AK .......

No comments