Breaking News

ZAN FASA KWAI 18

 *ZAN FASA KWAI*

           *page 18*

.........Wata zuciyar tace Mata shiga kawai ki karbo hakkin ki tunda ma gashi kin gani ya kawowa wadda ta sakashi

Har ta cire kafa zata tunkari kofar shiga gidan sai Kuma wata zuciyar ta kwabeta

Akul Kika SHIGA gidan can yadda Dan ta addar can ya nuna Miki bindiga komai zai iya faruwa gara dai ki koma gida ki sako sabon lale Amma SHIGA gidan can ayanzu akwai matsala

Sai Kuma ta karbi wannan shawarar da fuskar fahimta ta juya gida


Gambo mafiyas ya direwa izzatu kudin a gabanta inda inda ta Gane kudin ba duka bane Amma dai an rage ta Zaria rafar dubu dari ta bashi ya karba Yana godiya inda yace da wani aikin ya samu ta kirashi

Da haka ya fice Yana zukar tabar iblis din shi


Abinda izzatu bats sani ba shine shima gambo mafiyas sai da ya wari wasu kudin ya boye don harkar duka Babu Amana Amma izzatu Bata Gane ba ta dauki kudin ta mayar daki


Komawar sister mero gida ta doko wa izzatu waya inda tana ganin Kiran meron gabanta ya Sara dass ! Amma sai ta maze ta daga da salon bagararwa


"Sister mero ya kike ya aikine?

"Lafiya Amma abinda Zan fada Miki izzatu karki yarda kice irin wannan wasan zamuyi dake don na rantse Miki da Allah sai na kaiki kasa warwas..........


"Me akayi Kuma mero?....... .

"Karki yaudare Ni don Ni ba yarinyar goye bace idan kudin ki kike so ai ba sai kin turo min babbakun mabiya ba sai in maido Miki in karbi Yar mutane.........


"Nifa bangane Abinda kike nufi ba mero wani Abu ya faru ne?

"Kin fini sanin abinda ya faru saboda Babu Wanda ya San zanje banki karbar kudi sai ke to Akan me Zaki turo min Dan fashi bayan Ni da ke taimakon juna mukayi? Kuma magana Kare nazo dazu na tarar da shi Wanda Kika sa yayi min fashin ya Zo gidan ki da buhun kudina to saurareni da kyau na rantse Miki da sarkin da ya huran numfashi da tassarufin lamurana sai kin biyani kudina  Baki Nan da awa ashirin da hudu ki turo min kudina ga lambar asusuna Nan Zan turo Miki idan Kuma kina bukatar sauran kudinki Zan maido Miki in karbi Yar mutane duk shawarar da Kika yanke Ina jiran kiranki.........  

Dit ta yanke wayar tabar izzatu da kyalkyala dariya


"Uhum mero kenan na kula in ba kwanji na na motsa ba Zaki zame min kadangaren bakin tulu to duk Zan hada in kashe da tulun da kadangaren don Banga amfanin su ba


Akarshe dai ta yanke shawarar turawa sister mero kudinta don suna game wayar sakon lambar account din ta shigo wayar izzatu a take kuma tayi Mata transfer ta wsyar kudinta suka SHIGA inda sister mero tayi murmushi


"Uhum izzatu kenan tunda wannan turbar kike son mubi to Zan nuna Miki Ni har gobe takadarci Yana min Rana Baki sanni bane Amma Zan nuna Miki kece karamar Yar iskace Nasha gabanki har abada ke  gaba da abada ma na wuce da iyawar ki Zan Kuma waiwaye ki don wasan mu Bai ma fara ba karamar marar kunya dake bileja


Itama izzatu anata bangaren Tasha mugun Alwashin akan mero saboda ta kula itace zata zamo Mata matsala to su zuba shege NE zai fasa Bata santa bane nata iskancin kawai ta sani Bata San nata ba Allah yasa tsautsayi ko azal ya sa mero Kiran wayarta ko ma zuwa gidanta taga yadda ake kera Rashin mutunci



Tom Bari muga yadda Za ayi haduwa ta gaba da sister mero da izzatu waye zai FASA KWAI.............

No comments