WAYAR MIJI 2
*📱😱WAYAR MIJI😱📱*
Page 2
____Ko da ta nufi ajin, bayan ɗalibai sun gaisheta sun koma sun zauna, a wannan rana cikin karfin hali ta gabatar musu da darasin badon tana jin daɗi ba, da haka har lokacin ta ya cika nan tafito daga ajin, ita kaɗai tasan mai take ji. Ji take tamkar tasa hannu aka ta sa ihu. Tabbas gaskiyar Hausawa da sukan cewa wayar miji tafi Albasa zafi da raɗaɗi, wanda ke gusar da dukkan jin daɗin mutun. Bata an karaba ta ji idanunta ya cika da hawaye, saurin goge hawayen ta yi domin ƙoƙarin zubo mata su ke. Da kyar ta samu ta dawo da nitsuwarta sannan ta shiga staff room wanda tun da tazo bata shige shi ba sai yanzu.
Ƙasacewar yau jumma'a ne, tunin agogo ya juya izuwa karfe 12:30 wanda ya kasance lokacin tashi ya yi. Da kyar Malama Hafsat ta ja jiki ta fice a staff ɗin idan kawarta Malama Khadija ta ke biye da ita duk da bata faɗa mata meke faruwa ba amma sai hakuri ta ke bata har suka isa wajen da Malama Hafsat ta yi parking motar ta. "Ki yi hakuri ƙawata, insha Allah gobe zan zo na ji abunda ke faruwa".
"Shikenan, Allah ya kaimu anjiman domin ina matuƙar bukarki don ko baki zo ba ni zan zo da kaina".
"Zan ma zo insha Allah".
"To Allah ya yadda, na gode da kulawar ki". Kare maganar ta yi tana mai ɓuɗe murfin motar, sai dai kuma ta gagara shigarata. Nan ma sanda Khadija ta yi mata magana sannan ta shiga, a yau ji ta ke kamar ba zata iya tuka motar ba, cikin karfin hali da ɗauriya ta sanyawa motar key. Malama Khadija na ɗaga mata hannu har ta ja motar ta bar wajen, ko bakin get bata Isa ba sai ga mijin Malama Khadija ya zo ɗaukar a mashin, ɗaukar ta ya yi suka tafi, inda suka bar sauran malamai da ɗalubai na fitowa daga cikin makarantar.
Malama Hafsat driven motar kawai ta ke amma sam hankalin baya ga driven don tunin ya shige wata duniyar tunani wacce ita ce silar jefa kanta cikin wannan halin damuwar, mai ruguza duk wani farin ciki. Da haka dai ta karasa gidanta dake anguwar Dubai kwates, horn ɗaya ta yi maigadi ya taso da gudu ya wangame kofar get, a hankali ta kutsa kan motar cikin gidan inda ta ɗaga wa maigadi hannun sannan ta shige tun bata karasa harabar gidan ba ta hango motar Abban Khairat lokaci guda ta ji ranta ya ɓaci wani baƙin ciki da takaici ya kara riskar zuciyarta, ko da ta yi parking motar ga gara fitowa ta yi, idanunta ta lumshe ta na ji zuciyarta na mata kuna. Sosai idanunta suka ciko da kwallah masu zafi, ta jima zaune cikin motar kafin ta fito, jiki a sanyaye ta shige ciki, a babban fallo ta tarar da yaranta guda biyu Khairat da Ihsan don yau tasan jumma'a ce da wuri suke dawo wa daga school, Khairat ita ce babba wacce a ƙalla shekarunta za su kai bakwai, sai Ihsan wacce bazata wuce shekaru huɗu ba. Da jin salmar mahaifiyar su yasa suka taso da gudu suka yi wo kanta suna mata Oyoyo Mommy, duk da ta na cikin halin damuwa bai hana ta sakarwa yaranta fuska tare da rungume su tana shafa kan su ta na murmushi. Daidai lokacin da Alhaji Mus'af ya fito da ga bedroom nasa sanye da farar shadda gezna, yana ƙoƙarin gyara hular kansa zannan bukar, a ƙalla zai kai 40years duk da shi ba fari bane sannan kuma ba a ce masa baki ba, Kamar yadda ya ƙasance yana da tsawo tare da cikar jiki don baza a kira sa da siri ko lukuti ba, . Hakika shigar ta yi matuƙar amsar jikinsa inda suka fito masa da ci kar kamalar sa wanda suka ɓoyewe masa yawan shekarun shi. Kallo ɗaya Hafsat ta yi masa ta kauda kai gefe tana mai jin wani abu ya tokari kirjinta, har ya iso inda suke, Khairat ce ta juyo tana murmushi ta ce "Lahh! Mommy kinga Abba har shirya?".
Sai a lokacin Hafsat ta ɗago kai ta dube shi da wanni irin kallo daga sama har ƙasa, ba tare da ta ce mishi ƙalaba ta kauda kai gefe, domin ita a yanzu ta tsani ta haɗa ido da shi bare kuma har magana ta haɗa su.
Alhaji Mus'af murmushi ya yi wanda aka ce ya fi kuka ciwo, duk da abunda ta masa ya kona masa rai amma bai nuna mata ba domin akwai yara a wajen, nunawa ya yi tamkar bai san komai ba fuska a sake ya ce "To ni kam zan fita masallaci, sai na dawo".
Da sauri Khairat da Ihsan su ka ce "Allah ya ki ya ye hanya, Abba a kawo mana tsaraba".
"Ameen, insha Allah zan kawo muku, amma kafin na dawo kuyi wanka ku shirya zan zo muje gidan Haj....".
Tun kafin ya karasa suka sa ihun daɗi inda suka ta ɓalbala dariya ta farinciki zasu gidan Hajiya.
Shima yana dariyar ya fice batare da ya ƙara yiwa Hafsat magana ba. Suko yaran suka ta binsa da addu'a.
Hafsat fitar da wani irin numfashi ta ke zuciyarta na mata raɗaɗi kasa ce musu komai ta yi ta nufi bedroom nata. Ai ko bin bayanta sukai da gudu suna Mommy ni zaki fara yiwa wanka. Wani tsawa ta daka musu wanda yasa gaba ɗayansu suka nutsu, sai tsilli_tsilli da ido suke, Ihsan kam ma shirin yin ku ka take, zama ta yi baki gado tare da sauke ajiyar zauciya zaro wayarta ta yi daga cikin jaka inda ta shiga lalumi number Baba Altine, ƴar dattijuwar matar ungiwarsu dake mata aiki, bugu ɗaya ta ɗauka jiki na ɓari Baba Altine ta ce "Barka dai Hajiya".
"Yawwa barka, dama na dawo daga makaranta ne kizo kiwa yara wanka".
"To bari na zo, sannu da dawo wa". Cewar Baba Altine.
"Yawwa, sai kin zo". Tana faɗar haka ta katse wayar ta aje. Lumshe idanunta ta yi kafin daga bisani ta dubi yaranta cikin sanyi maurya ta ce "Ku je falo ku jira Baba Altine nazuwa ta muku wanka, yau banda lafiya ne". Ta faɗi haka ne domin gusarwa yaran da tunani.
Da jin kalmar rashin lafiya duk da da yarinta a gate da su, cikin tausaya wa Khairat ta ce "Mom Allah ya sauwaka".
"Ameen, maza kuje kunga har ta zo". Duk suka juya suka fice, ita mikewa ta yi ta shige bethroom wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala ta fito. Ko da ta gabatar da sallar ta jima zaune kan sallayar tana addu'oin sannan ta shafa, ba wata kwalliya ta yi ba domin a wannan yanayin da take ciki bata ji za ta iya kwalliya doguwar rigar atamfa ta sa tare da ɗaura ɗan kwalinta ta fice daga ɗakin ta nufi falo, inda ta tadda su Khairat a shirye tsaf suna zaune a falo, Baba Altine na gefen su suna ƴar hira.
Ita ma sami waje ta yi ta zauna, inda Ihsan ta taso ta kwanta kan ciryata. Duban Baba Altine ta yi ta ce "Sannu da aiki".
"Yawwa sannu Hajiya".
"Sunci abinci kuwa?".
"A'a".
Hafsat maida kallonta ta yi ga Khairat ta ce "Me yasa ba kuci abinci ba?".
"Mommy ni akoshe muke, sai munje gidan Hajiya mu ci".
Girgiza kai ta yi batare da ta ce wani abu ba, ta ɗago kan Ihsan ta ce "Mamana ke kan zaki ci abinci ko?".
Ɗaga mata kai Ihsan ta yi alamar eh zata ci.
Ɗan murmushi Hafsat ta yi sannan ta maida kallonta ga Baba Altine ta ce kawo mana abincin.
Mikewa ta yi da hanzari ta nufi kitchen bata jima ba sai gata ɗauke da plate guba biyu na jolop ɗin taliya wanda taji kayan lambu. Ko da ta aje musu a gaban su Hafsat ce wa ta yi ta ɗau plate ɗin abincin ɗaya ta bar musu ɗaya, don ita yau bata jin cin abinci.
Tusa Khairat ta yi sanda ta ci abincinan inda ta ke bawa Ihsan a baki. A lokacin ne Baba Altine ta gama aikinta ta yi musu sallama ta tafi. Fitar bai jima ba sai ga dawowar Alhaji Mus'af, ai suna jin sallamar shi suka ruga da gudu suka nufe sa. Cak ya ɗaga Ihsan ita dai Hafsat da taga ya shigo kawai sai ta koma cikin ɗaki ta barsa tare da yaransa. Zubewa ta yi kan gado daidai lokacin da wasu hawaye suka zubo mata. Ita kaɗai tasan kunan da zuciyarta ta ke, ta na jin hayaniyar su inda daga karshe Khairat ta shigo ɗakin da ta ke ta ce "Mommy za mu tafi".
"To sai kun dawo" Amsar da ta bata ta na mai maida kanta, daura hannun ta yi bisa kirjinta idanunta ta lumshe ta na fidda numfashi mai zafi, ita kaɗai tasan raɗadin da zuciyarta ta ke.
Fitan Khairat sai ga shigowan Mus'af a hankali ya maida murfin kofar ya rufe, a hankali ya fara ta kowa cikin ɗaki, tabbas yasan shine da laifi, amma kuma mai ya kaita ɗaukar wayarsa yana bacci har ta yi bincike?. Cak ya tsaya a kanta ya na mai sauke numfashi, ya ma rasa ta ina zai fara mata magana.
Ita kuma jim kamshin turarensa yasa ta tabbatar da mus'af ne ya shigo kara damke manyen idanunta ta yi wanda suke tsiyayar ruwan hawaye, ya risa gabanta zai mata magana sai ga shigowar Khairat da Ihsan. "Abba ka zo mu tafi". Da sauri Mus'af ya mike tsawonsa nan ya riƙe hannun yaran duka ya jasu suka fita.
Da jin fitar su ta sauke ajiyar zuciya, ta shi ta yi ta zauna ta jin gina da kan gado, fillo ta rungume kwalla masu zafi na kuma sakko mata, anya zata iya hakuri ta zauna cikin gidan nan kuwa? Anya? Abunda ta ke faɗi cikin zuciyarta ke nam.......✍️
*Yawan comments*
*Yawan typing✍️*
Fatan Alkairi gare ku masoya na.
Zainab Ibrahim Gombe
No comments