Breaking News

WAYAR MIJI 1

*📱😱WAYAR MIJI😱📱*

 *LABARI, RUBUTAWA* 

               *NA* 

 *Zainab Ibrahim Gombe* 

 _Marubuciyar_ 

         👇 *SANADIN STATUS* 

  (Aka yi min kishiya)

 *WAYAR MIJI...✍️* 

*بسم الله الرحمن الرحيم*          

   *Gargaɗi!* 

     Ban yadda a sauya min labari na ta ko wani siga ba.

*Sadaukarwa* 

          gare ku iyayena abun alfahari na, Allah ya albakaci rayuwar ku.

              *PAGE 1* 

_____GOVERNMET DAY SECONDARY SCHOOL PANTAMI GOMBE STATE (G.D.S.S Pantami)                                           Makaranta ce wacce ta kasance ɗaya daga cikin jerun makarantun gwannatin dake cikin jahar Gombe na zuwa da dawowa. Babbar makaranta ce wacce ta ƙunshi tun daga matakin farko na Nursery, primary, har izuwa kammala secondary school.


Makarantar ta kasance mai fanni biyu, inda aka keɓewa Nursery and primary fannin su tare da get nasu. Jenior and senior suma aka basu nasu fanni da get nasu. Fannin daya kasance na karshe wanda za a iya kiransa da karshen makaranta shine ya kasance shashin ƴan Senior secondary (S.S 1to3) Babban wajene wanda ajujuwa suka kewaye wajen tare da staff room na malamai da office na principal, da sauran abubuwa domin samun ingantaccen ilimi.


Ranar wata talata da misalin karfe sha ɗaya na safe (11:00am) harabar makarantar ta kasance shiru kansacewar ɗalibai sun koma aji bayan breakfast da suka fito. Malamai ne jifa_jifa suke fitowa daga staff room sukan nufan ajujuwa domin gabatar da darasi wa ɗalibai akan lokaci.


Wata matashiyar Malama ce fara kyakkyawa, wacce ba zata gaza shekaru talatin ba 30year. Yana yin yadda ta ke shigar ta shi zai tabbatar maka da kuɗi sun zauna. Ado da kwalliyan da sukan rage mata yawan shekarunta. Zaune take  kan plastic chair acikin runfar da ta kasance gaban staff na malamai mata. Sanye ta ke cikin riga da zani single na  tsadadden wani les marun colour mai mayan fulawi milk and gwaldin, ta lulluɓe kanta da milk colour mayafi, sosai kyawun fuskarta ya fito duk da ba wani kwalliya ce akan fuskarta ta ba. Shiru ta yi ta zuba uban tagumi wanda koda baka tambaya ba idan ka dubi yanayin fuskarta shi zai tabbatar maka da tana cikin damuwa, don hausawa kan ce wa labarin zuciya a tambayi fuska. To hakan ta kasance ga Malama Hafsat.


Malama khadija ce tazo shiga staff da alama daga class tafito domin wani ɗalibi na biye a bayanta rike da fefofin test da tayiwa dalibai. Har zata shige sai ta hangi Malama Hafsah zaune ta zuba uban tagumi tare da kura fulawin da ke gabanta ido. Sauke ajiyar zuciya Malama khadija ta yi domin tasan wannan shirun da kawarta ta yi ba na lafiya ba. Bawa dalibin umurni ta yi daya shigar mata da fefofin ya aje mata wajen zamanta, amsa mata ya yi da to cikin ladabi ya shige ciki. Ita kuma ta nufi inda Malama Hafsat take wacce ta tsunduma duniyar tunani don har ta iso gareta bata san ta iso ba. Bakinta kusan sau uku tana sallama amma ina tamkar ba ta wajen. Ganin hakan ɓata lokaci ne ya sa Malama khadija sa hannu ta dafa kafaɗarta tare da girgiza ta tamkar wacce aka razanar cikin mafarki haka Malama Hafsat ta firgita tare da sauke ajiyar zuciya a take, daga kai ta yi ta kai dubanta ga Malama khadija wacce ita ma kallonta take domin kara karantar yanayin da take ciki, idanun su na sarkafe da juna cikin nuna kulawa Malama khadija ta ce "Ƙawata lafiya? Meke damun ki?" Tambayoyin da Malama khadija ta jero mata a lokaci guda ta na mai jan kujera ta zauna kara zuba mata ido ta yi da alama tana jiran ta bata amsa.


Nan nauyan ajiyar zuciya Malama Hafsat ta sauke tana mai gyara zamanta, kau da kanta ta yi da ga kallon da Khadija ta ke mata. Shiru ne na yan mintuna ya ratsa wajen kafin daga bisani ta dawo da kallonta cikin sanyin murya mai nuna alamar damuwa Malama Hafsat ta ce "Aminiyata ina cikin wani hali". 


"Subhanallah! mai ke faruwa Hafsat?" Cike da kulawa ta yi tambayar tana mai zuba mata ido.


"Kwarai ma kuwa Hafsat dole kowa ma ya faɗi haka idan har yasan waye mijinki dole a kirasa da miji na gari".


"Khadija ba lalle ne abinda ya kasance a zahiri ya kasance haka a ɓoyeba domin a jiya na tabbatar da zargin da nakewa mijina gaskiya ne, a jiya na tabbatar da namiji bayi da amana, tabbas namiji butulune". Cikin rawar murya ta kare maganar inda hawaye tunin suka ciko idonta.


Sosai Malama khadija ta shiga ruɗani da jin maganganun marassa daɗi da ƙawarta ta jero wanda ba ta yi tsammanin jinsu daga bakinta ba. Buɗe baki ta yi za ta yi magana sai ga sallamar wani ɗalibi daya ratsa kunne su. Da sauri Malama khadija ta kai dubanta gare sa ta ce "Lafiya?".


"Lafiya lau Malama dama kiran Malaman Biology na zo yi domin lokacinta ya yi".


Malama khadija sauke a jiyar zuciya ta yi, tare da maida kallonta ga ƙawarta ta, kafin ta yi magana ta tsinci muryar Malama Hafsat nacewa "Ka je ina zuwa".  Amsar da ta bashi a takaice tana mai gyara zamanta, lumshe rinnannun idunta ta yi tana sauke a jiyar zuciya sosai kwakwalwar ta da zuciyarta ke dawo mata da abinda ya faru a jiya.


Tabbas a jiya ta yi matukar da na sanin da na daman daukar wayar Abban Khairat, da tasan wannan abu zata tarar da bata dauka ba. "Ya Allah" Ta furta can kasan makoshinta tana mai ware idanunta ta dubi Malama Khadija ta ce "Ƙawata naso na gaya miki abinda ya faru dani jiya, domin ke ka ne zaki iya fahimta ta, har ki bani shawara, sai dai kuma kash! ba lokaci". Kare maganar ta yi tana mai dafe goshinta, wani raɗadi take ji cikin zuciyarta. Numfashi ta ke fitarwa mai zafi, "Ya Allah ka kawo min mafita". Kalmar data fito a bakinta.


Ita dai Malama khadija kallon ƙawarta ta ta ke wacce tausayinta ya kamata. Cikin kulawa ta ce "Hafsat kar ki damu, aduk halin da kike ni mai baki shawara ce. Don haka ki tashi ki shiga aji, idan don lokacine an jima da yamma zanzo gidan ki, sai ki faɗa min koma menene kin ji". Cikin Muryar nuna tausaya wa ga ƙawarta ta ta kare maganar. Tana duban fuskar Hafsat, hannunta Hafsat ta haɗa da hannun khadija ta na kallonta ta ce "Na gode Khadija".


 "Kar ki damu ki tashi kije kar time ya kure".


Gogen kwallan dake shirin sauko mata Hafsat ta yi tare ɗaukar jakarta ta mikewa, ita ma Malama khadija mikewar ta yi. "Bari naje ƙawata".


"Ok, to sai kin dawo". Cewar Malama khadija.


Nan suka rabu, Malama khadija bin bayan Hafsat ta yi da kallo tana saka zancen zuci, azuciyarta ta ce "Ikon Allah! yo inni ne da gata irin naki Hafsat har akwai wani damuwar da zata damen?" Abunda ta faɗin tana mai juya ta shige staff room....✍️





To dai kunji wannan salon labarin,

Ya sha bamban da SANADIN STATUS


Idan har kuna bukatar ci gaban sa, na ga ni daga yawan comments naku. Ni kuma sai na ji daɗin yi muku typing mai ya wa.





Ta ku har kullu


    Zainab Ibrahim Gombe

No comments