TSANGAYAR MALAM 1-2
_*👳♂️👳♂️👳♂️TSANGAYAR👳♂️👳♂️👳♂️*_
1️⃣-2️⃣
"""Gauro gauro ......
gauro!!!
"Tashi gari ya waye.………
gauro!!!
"Mai azumin gema ge………
gauro!!!
"Mai sahur da ƙaragu………
gauro!!!
"Katashi gari ya waye…………Yara ne danƙam sun cika gari sai buge bugen kwanuka da jarkoki suke suna yawo ko ina suna waƙar gwauro musamman majalisar da samari ke zama da shagunan samari da yawancin su a buɗe suke sun taru suna fira,Ɗan malam ne da ke zaune cikin su baƙiru da nafi'u ya dubi samma da farin gajimare ya gauraye sararin samaniya ya ce"
"Wai ni ko Baƙiru anga watan azumin nan ne a garin nan ko ko ba a ganshi ba?
ɗan malam ya karkata wuyansa yana duban baƙiru da ya mai da hankalinsa ga ɗan malam ɗin ya amsa da.
"Ai ɗan malam ba a iya garin nan ka ɗai aka ga wata ba an ganshi a garuruwa har guda bakwai kuma sarkin musilmi ma ya shaida hakan insha Allahu gobe war haka mun kai azumin Ramadana ɗaya.
"Haba dai baƙiru,"kai yaushe kaji an faɗi haka ance an ga watan azumi?
a radio naji da inna ta kunna kasan mayyar jin labarai ce safe da dare kuma naji baƙo ma yanzu da zan fito ya shigo gidan yana faɗawa inna a tsakar gida ga kuma yara na murna kaga magana ta ta gasgata yau dole katashi kayi sahur ka dauki niyar yin *AZUMI* ɗan malam.
samma ɗan malam ya hanga ya kuma ware idanunsa duka biyun ya ce"
"Hmmm ni dai har iyau banga watan azumin nan ba sai ware ido nake ko zan ganshi.
",Taɓ ai wallahi ba zaka ma ganshi ba duk wani gwale gwalan idanun da zakayi Azumi dole kayi shi haka zalika idon Allah bai nufeka da ganin wata yanzu ba to wasu bayan Allah sun gane maka malam ka ɗaura niyya tun daga yanzu Dan yasin bazaka ga komai ba na harbo jirgin naka inda ya nufa.
amma ko Allah wadaran munafiki ɗan munafuka kuma ɗan sa ido kai kaji NAFI'UN nan daga ji nayi magana sai ka kwaɓe baki kace wani ƴan ƴan ƴan,kaga nafi'u ban kasa da kai ba balantana ka ɗauka ko na kirayi sunan ka tunda nazo nan wajan na zauna, Dan haka bana son mutum ya shiga shirgina wallahi zan maka abinda nayiwa alabaka shekaran jiya.
"kai kaji wawa baho to ai sai kayi mun kaga in zaka ci riba wallahi sai na rama in da ƙarfina ya ƙare ni ba alabaka bane da zanji tsoron ka na kasa taɓuka komai nafi'u nake duk iya shegen ka kasan na dameka na shanye yaro.
"ni ne yaron naka?
babba ma kuwa idan kana cin ƙasa to ka kiyayi ta shurun ta.
to shikenan ka zuba ido kaga yanda zata kwashe dani da kai Allah sai na manna maka hauka tuburan ba dai dani kake musu ina faɗa kana faɗa ba hmmm.
''''kaga malamai duk ba abin tada jijiyar wuya bane kun cika mana kunnuwa da surutu duk abar maganar ma ta wuce azumi kuma gobe in Allah ya nufe mu da rai da lafiya warhaka mun idah ɗaya.
idan na haƙura shege nake baƙiru sai na mannawa wannan sokon hauka tuburan akan sa bari ma kaga ina zuwa.
haba ɗan malam daga maganar azumi sai ta zama faɗa ka tashi dan Allah ka dawo mu yi maganar da zamiyi ta gonar baba Hashimu mana.
sai dai ku je kuyi abar ku indai da wannan abun za'ayi yasin na fasa ,ɗan malam ya nuna Nafi'u da yatsa ya ɗora""tun daka ɓatan rai kaf gidan ku sai ransu ya ɓaci ni na faɗa maka.
Idan baka fasa ɓatawa dangin mu kaf rai ba baka cika jinin malam ba har ni zakayiwa burgar banza da kake yiwa wasu sokayen.
Ohhhhhh Allah ina ma na fito da shiri na amma bata ɓaci ba Nafi'u duk zaka amayar da zantukan nan ranar da ka kasa gane hanyar gidan ku ohhhhhh shatttt Nafi'u kazo da wasa ka dugunzuma zuciyata ka karkatar da lissafina akan kaf dangin ku gaba ɗaya kuma na rantse maka da Allah bazaku walwala a cikin garin nan ba mudin ina ciki,Dan malam ya juya afusace yayi qofar gidan su,yana zuwa dai dai qofar gidan ya banke ƙyauran gidan ya faɗa kai tsaye Baƙiru sai kwara masa kira yake yana"""
"ɗan malam!! ɗan malam!! ɗan malam, ko juyowa ɗan malam be yi ba ya nausa kansa cikin gidansu ya na kwara kira"""
""Malam!! malam!! fito ga tambaya me ma'ana tunda kune manyan malamai magada Annabawa.
tsuke bakin sa ɗan malam yayi ya chake akan wata dattijuwar mata fara sol da ita ya na.
"Kaga Uwailan malam me taro da sisi yau kuma me ake shirya mana,wai shin ma ina malam yake tun da na shigo nake ta faman kwara masa kira bai amsa ba ban kuma ga ƙeyarsa ko sayyadarsa ta leƙo ba ina malam ya nufa ne Uwaila?
"yatafi koyo sallama.
Uwaila ta bawa ɗan malam amsa ko ɗagowa batayi ba kan ta na kan tace giron da take murmushi ɗan malam ya saki ya gyara tsaiwar sa ya ce""
""Koyon sallama kuma bayan sune masu koyar da yin sallamar ko dai zakkah yatafi karɓo mana ne Uwaila kike son ɓoye mun kin ga sanar dani da da wuri mu fara kasafta namu rabon kafin malam ya dawo.
hmmm, uwalai tace ta cigaba da safgar gabanta ko ƙala bata tankawa ɗan malam ba,shima ɗan malam ɗin ganin Uwaila tayi masa shiru yasa ya tsuke fuskar sa ya ɗan sunkuyo kan Uwaila ya ce""
Uwaila!! uwaila!! kenan ki amsa mini da wuri kar ki shiga layi yanzu haka rai na aɓace yake ina malam ya nufa na ce miki?
Ban sani ba tunda nace maka yatafi gidan koyo sallama baka hankaltu ba kar ka uzira mun kazo ka dameni daga shigowarka ni nace........"Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu,wani dattijon mutum fari tas dashi ya faɗo gidan riƙe da buhu a hannunsa babba Nafi'u na bayan mutumin shima ya saɓo wani buhun akansa,da sauri Uwaila ta miƙe tana""
"""Wa'alaikumus'salam Warahmatullahi Wabarakatuh,Uwaila ta miƙa hannu da sauri ta amshi buhun dake hannun dattijon haɗa cewa""
""sannu da zuwa malam.
Yauwa Uwaila.
malam ya faɗi yana saukewa Nafi'u buhun dake kansa harara ɗan malam dake tsaye ƙiƙam ya dallawa Nafi'u,Nafi'u ko takansa bai biba yayiwa malam sai anjima malam ya zaro wazobia ya miƙawa Nafi'u yana masa godiya Nafi'u ya ƙi amsa ya fice daga cikin gidan da sauri kar malam ya ce sai ya karɓa malam da uwaila suka shiga yabawa nafi'u da zayyano kyawawan ɗabi'unsa ko inda ɗan malam yake basu kalla ba haushi da baƙin ciki yasa ɗan malam yin ƙofar gida yana tafe yana ƙunƙuni malam ya bi bayansa da kallo haɗe da faɗin""
"Allah ya shirye ka ya ganar da kai *Attahiru*
_*IDAN KUNJI DAƊIN SA NAGA*_
*COMMENTS*
*SHARE ANEY GROUPS✍️*
No comments