UWA UWACE 5
UWA UWACE...5
Batul Mamman💖
Assalam alaikum ma'abota bin wannan labari. Ina alfahari daku kuma ina godiya. Ayi min hakuri saboda dogon jinkirin da ake samu ba post. Yau da gobe sai godiyar Allah. In sha Allah duk lokacin da na samu dama zan dinga typing har komai ya daidaita na dinga yi a kai a kai.
Abu na gaba mutum biyu
sun ankarar dani cewa akwai wani littafin mai suna Uwa Uwace a manhajar okada.
Kasancewar sunansu daya coincidence ne. Nawa kyauta ne wancan kuma na kudi.
Saboda haka zan dinga kara inkiya a gaban nawa sunan domin a daina samun
rudani.
Ina godiya
Ina muku SonSo
Stay Safe
***
Kwana goma cif da
tarewar Nasima a gidan Tahir. Amarci suke irin wanda iyayen gida ke tsoron ayi
musu kishiya su ga irinsa. Kullum sabon nau'in fitsara da rashin kunya Nasima
ke kirkira wanda zai batawa Khadija rai. Abin da bata sani ba kuwa shi ne fitar
Tahir da aurensa kacokan daga zuciyar Khadijan. Zaman 'ya'ya take yi kamar
yadda matan aure da yawa suke yi. Bata da dogon buri ko hangen komai sama da
inganta musu rayuwa. Ba don su ba komai wuya da tuni ta koma gidan mahaifinta.
Sati guda ta sani
addini ya bawa amarya budurwa tayi tare da ango kafin a raba kwana tsakaninta
da ta gidan. A sati dayan sai take yi musu girki na kyautatawa ba don ta
burgesu ba sai don ta sami ladan rama sharri da alkhairi. Anyi satin an wuce
shiru Tahir bai yi mata maganar su raba kwana ba. Girki kuma bata ga alamun
Nasima za ta shiga kitchen ba sai ta cigaba da yi saboda yaranta.
Tana cikin wanke salad
Nasima ta shigo kitchen din dauke da kwalin sabon food flask. Tukunyar
shinkafar da Khadija ta bari ta karasa turara ta nufa kai tsaye. Khadija bata
nuna ta san da wanzuwarta a wurin ba sai da taji ta bude tukunyar. Don karfin
hali ma harda cokalinta a hannu ta danna shi kasa domin ta tabbatar ruwan ya
tsotse.
"Lafiya?"
Baki ta murguda mata
gami da fari da idanu "lafiya kamar ya?"
Ran ta ya soma baci
sai dai tayi alkawarin Nasima tayi kadan tayi fada da ita.
"Abincina naga
kina shirin budewa."
"Abincinki ko
abincin mijinmu? Naga dai shi ya saya don kin girka hakan ba ya nufin ba zamu
ci ba."
'Kar ki biye mata'
Zuciyarta ta kwabeta a lokacin da taji kamar ta mareta. Suturar jikinta da tun
tarewarta irinsu take sakawa ta kalla ta kawar da kai. Gajeren wando ne da bai
kai rabin cinyarta ba sai damammiyar vest. Anayi ne don ta tofa ace ta ce shi
yasa take bawa iska ajiyarta.
"Ki jira na
dibarwa yara tukunna."
Wani irin kallon raini
Nasima tayi mata ta soma cewa "ke kin i..." sai taji an bude kofa kuma
ta tabbatar Tahir ne. Langabe kai tayi ta kwantar da murya tana bubbuga kafa
duk jikinta na rawa "ni dai don Allah Anti Khadija ki karba haka nan.
Wayon hutawa kawai kike yi min kin barni inata fama ni kadai."
Kitchen din Tahir ya
shigo Nasima ta kwabe fuska tana yi masa shagwaba "Diya (Dear) wai kaji ta
kara mana satin amarci ba yanzu za'a fara rabawa ba."
Ko ita ta sarawa
kissar Nasima. Jinjina kai tayi harda 'yar dariya.
"Sai fa ba Diya ba"
"Me ki ka
ce?" Tahir ya tambayeta ta da murmushin jindadi a zatonsa sun fara hada
kai ne.
"Ban ce komai
ba" sai ta mayar da dubanta ga Nasima "na baku wata guda don Allah
kada ki ce baki karba ba. Da so samu ne ma zan fi son karba idan ki ka fara
tofe-tofe da tashin zuciya."
Ta karasa maganar ne
tana dibar abinci. Da ta gama ta zo fita ta dakata a gaban Tahir.
"Af...Diya"
ta furta kalmar yadda Nasima ke fada da tsantsar rashin wayewa "na ce kada
ka manta yaba kyauta tukwuci. Zan zo amsar nawa idan mun gama cin abinci. Da
yake ma mu ba mayunwata bane idan za ka saurareni yanzu na san zasu iya
jira."
·
·
Ransa yake ji a
jagule. Dama gashi ta fara sire masa. Abin da yake doki ya riga ya samu har ya
fara tunanin komawa titi abin sa. Ga Khadija duk ta canja. Da yatsa ya nunata
kamar zai tsokane mata ido.
"Bar ganina haka
wadannan yaran basu da na biyu. Ina son abuna kuma idan kina neman zaman lafiya
a gidan nan dole ki so su."
Bai kara saurararta ba
ya tafi dakinsa ya banko kofa cikin bacin rai. Zama ya yi yana tunanin me
yasa yake ganin kamar Khadija ta daina sonsa? Ba haka yake so ta dinga yi masa
ba. Kishin da ya tsammaci gani wanda zai tabbatar masa da sauran matsayinsa a zuciyarta
duk babu. Baya mantawa kafin wata dayan nan da ta kara musu ya cika gabadaya
Nasima sai da ta gundure shi. Don ma yana jin sonta a zuciyarsa ne da bai san
me zai faru ba. Yana ta tuhumar kansa me yasa ya yi saurin aurenta. Da ya sani
kuruciyarta kawai ya mora ya bata abin da zai bata a waje. Yarinyar sam bata da
aji.
"Wai Diya...sai
kace wani dabba. Mtseww"
Tunawa ya yi Khadija
ma tana fada idan ta so cusa masa haushi ya yi dan murmushi. Tunda dai bata
tafi ba zai cigaba da lallaba abarsa. Da tsohuwar zuma ake magani. Mata nawa ya
nema bayan aurensu amma duk inda ya gama yawonsa wurinta yake dawowa.
Da yake ita keda girki
ranar da ya koma dakinta ta cigaba da yi masa komai yadda ta saba. Kallonsa
tayi yana ta biyewa yaransa suna wasa tayi kwafa. Ba za ta taba bari ya gane
kudurinta ba. Da kudinsa za tayi karatu. Burinta ta sami jari ko aiki a gaba
wanda za ta iya rike kanta da 'ya'yanta. Komai dadewar lokaci, komai tsufa, za
ta bar gidan Tahir.
Nasima kuwa ta dade a
tsaye inda Tahir ya barta. Tsoro ya gama mamaye zuciyarta domin ta kula ba tun
yau Tahir yake hantararta ba.
"Na rantse kayi
karya Tahir. Ni da kai yanzu muka fara zaman aure."
A ranar ta tambaye shi
zuwa gida ya amince. Washegari yana fita ta tafi wurin Laraba. 'Yan kudaden da
yake bata ta fiddo duka aka bawa wani malamin tsibbu. Ya hado mata magunguna da
bayanin cewa da basu zo ba a ranar zai saketa. Wai bokan Khadija ne yake musu
farraku.
"Laraba kin ji
ko? Na fada miki yanzu kamar bana burge shi ga yawan fada." Ta ce cike da
gamsuwar karyar bokan.
Kulle-kullen da ya
basu ta dauka ta tafi dasu gida tayi amfani dasu yadda ya ce.
To gidan dai rayuwa
ake yau fari gobe tsumma. Khadija tana Zaria da yaranta sai dai Tahir ya
ziyarce su. Ko suna hutu sai ta fake da karatun yaran. Sai lokutan hutu
gama-gari take zuwa gidan. Karatunta take yi hankali kwance sannan tana sayar
da zobo da ginger. Tun tana kullasu a leda har ta koma yin na roba. Kasuwa ta
karbu har freezer ta kara saya da ribar cinikin.
***
"Ina cewa matarka bata da hankali ashe kaine babban mara hankalin. Inuwa!
Inuwa ka bani kunya." Mal. Sa'adu ya furta rai a bace.
Sunkuyar da kai Inuwa
ya yi kunya ta mamaye shi. Yayan nasa bai tashi yi masa tijara ba sai da yaga
sauran matan kannensa sun zo wucewa. Ai kuwa tsayuwa suka yi a fakaice aka gama
jin fadan.
"Amma saboda
Allah Yaya kana ganin irin mutuwar da Sani ya yi. Idan bamu yi wani abu ba shi
ma Abbatin haka zamu rasa shi"
Murya har dakuna
mafiya kusa ake jin fadan Mal. Sa'adu yana cewa "Wanda ya rasu a wurin
neman ilimi yana cikin jerin shahidai idan baka sani ba. Kuma tunda mutuwar ta
kuruciya ce idan an je lashirar ba kai da Marin za'a fara cewa ya ceto ba. Kila
ni da na assasa tafiyar ma sai ya gama daku zai ambaceni."
Inuwa dagewa ya yi shi
ma"Ni dai gaskiya zan dauko shi na saka shi a ta allo da boko a nan."
"Ahap...tushen
magana ya hito da za ka zauna kana yi min kwana-kwana. Daga makarantar 'yan
aljanna za ka kaishi ta 'yan wuta. Wai ma shin 'ya'yanka aka fara kaiwa ne?
Gidan nan kowa yana kaiwa. Don naka ya rasu sai ka kasa karbar kaddara?"
·
·
Fadan Mal. Sa'adu yaki
karewa. Inuwa tun yana mayarwa har ya kasa katabus. Sauran 'yan uwansa ne suka
hade masa kai aka fara yi masa nuni da cewa Mari tafi karfinsa kuma ita take
juya shi. Bahaushen mutum da jiji da kai da gudun raini sai yaji tsoron kada su
raina shi. Har kasan zuciyarsa ba ya so amma kuma rashin son ayi masa kallon
mijin-tace ya danne komai. Sun kunno shi sosai sannan ya shiga ciki ya hau Mari
da fada.
"Abbati ba zai
dawo gida ba kuma ban yarda ki je Kano ganinsa ba. Tunda dai zasu zo hutun
Takutaha nima ba zuwa zanyi ba."
Wani abu ta hadiye da
ya tokare mata wuya da kyar sannan ta daga kai ta kalle shi. An kusa wata biyu
da rasuwar Sani amma har yau ta kasa komawa daidai. Da ciwo mai raunana zuciya
da ruhi a tare da ita. Dashi take kwana dashi take tashi. Duniyar sam ta daina
yi mata dadi. Gani take ta gaza a matsayinta na uwa. Kwanakin farkon rasuwar
saboda ta sa abin a rai har mafarkinsa take yi yana tuhumarta da wulakanta
amanar Allah.
Shekararsa bakwai
kacal a duniya. Sa'anninsa da suke cikin gata wasu ko kyakkyawan tsarki basu
iya ba. Wasu su dawo daga makaranta suna bore suna ihun sun girma uwa ta kamasu
tayi musu wanka da kanta. Wasu a basu abinci a baki. Wasu uwa ta shagwabasu da
soyayya ba don su lalace a tarbiyya ba. Almajiri kuwa sai yadda Allah Ya yi. Ga
kuruciya, ga rashin gata kuma a haka cuta za ta kama shi. Babu magani babu
kuzarin yin bara sannan ba lallai a sami mai damuwa da halin da yake ciki ba
balle a taimaka masa. Idan da tsananin ciwo zai saka shi amai a makwancinsu
babu abin mamaki wurin samun masu yi masa tsawa da hantara kuma ace ya goge
wurin. Idan ya yi zawo a jikinsa sauran dalibai su toshe hanci su guje shi.
(Ke da yake da yake
yiwa shara, wanke-wanke ko zuwa aike idan ya yi fashi ki hau shi da fada. Cikin
dan albashin da kike bashi ki cire na kwanakin da bai zo ba. Ya wuni a rana
yana wanki ki bashi ragowar abincin jiya kila ko dumamawa baki yi ba. Hakika
tallafawa almajirai kafin gwamnati da masu ruwa da tsaki su dakatar da wannan
al'adar jihadi ne. Idan wani mahaifiyarsa tana da rai kuma ta yarda yazo wani
tasa uwar irin su Mari ce ko maraya ne. Idan wasu duniya ta lalatasu kamar
Abbati wani kuma is innocent kamar Sani.)
"Allah Ya kaimu
Takutahan" ta iya cewa kadai.
Watannin sun wuce a
yayin da bawa yake ta fadi tashin neman na kai. Wannan mummunar alfasha ta gama
shiga jikin Abbati da Munzali. Ranaku daidai ne basa haduwa. Shazali da
abokansa suka koma amfani dasu biyun. Saboda haka yanzu abincin Abbatin ma ko
bai hadu da Munzali ba zai samu a wurinsu. Ya murmure fiye da yadda ya zo daga
kauye. Ya kuma zama fitsararre mara kunya da kawaici. Babu mai saka shi
ko ya hana shi a makarantar saboda Shazali ya tsaya masa.
Malaminsu ya dade da
sallama su Shazali. Sun zame masa karfen kafa. Babu karatu kuma sun ki komawa
gidajensu.
Ana gobe hutun Abbati
ne tare da Munzali dasu Shazali a kangon suna cin abinci. Tsire ne da biredi
sai kwalbar lemo a hannun kowannensu.
Shazali ya kusa sati
yana juyayin gabatar musu da wata bukata amma yana gudun kada cikin surutu su
fadawa wani. Amininsa ne ya ankarar dashi cewa ďa zasu fada fa da tuni wancan
abu ya dade da yaduwa. Sai da ya kula duka suna jindadin abincin ya kawo
zancen.
"Da ace kullum ni
nake baku kudin abinci ko na baku ba gara ku dinga bina inda nake samowa ba ku
ma ku dinga shanawa da kyau."
"Al'Qur'an ko ma
ina ne ni dai zan bika." Cewar Abbati da zumudi.
"Kai fa
Munzali?"
"Abbati ma zai
yaje bare ni."
"A wurin irin
abin nan da muke yi zasu dinga yi daku sai a baku kudi. Idan ku ka fadawa wani
a take zaku mutu."
Wannan ba abin damuwa
bane tunda sun riga sun saba. Abbati bai ji dadi ba saboda dole sai bayan ya
dawo daga gida za'a kai shi.
Ranar da zasu tafi
'yan uwansa na wasu makarantun a Kano ne suka hadu da 'ya'yan makota duk 'yan
gari daya suka tafi tare. Yana shiga mota ya shafe shafin su Munzali.
Hankalinsa ya yi gida Baaba Marinsa yake son gani da kannensa. A nasa haukan
yake son ganin Sani ya fada masa abin da yake yi yana samun kudi da abinci.
·
·
Zancen zuci yake wanda
don dadin da abin ya yi masa har dan tsalle ya yi akan kujerar mota. 'Shi ma
idan ya yi mu tara kudi mu kai Baaba Makka da Madina'. Bai san abin da yake ya munana
ba. Ya dai san kila Mari tayi masa fada. Munzali ya ce manya ne kadai suke yi.
***
Mari tana yayyafawa itacen da ta gama yiwa Abbati miyar zabi taji muryarsa.
"Baaba. Baaba na
dawo. Baaba Sani ma ya zo?"
Murnar da ta tashi da
ita sai ta nemi komawa ciwon rashin Sani. Murmushi tayi saurin yi domin kada ya
zata bata murnar ganinsa har ya iso gareta. Da murnarsa ya taho zai rungumeta
sai taji kunya. Tsakar gidan da mutane duk an zuba musu idanu. Yana isowa sai
zai riketa sai ta dafa kansa.
"Kun dawo lafiya?"
Bai biye mata ba ya
rungumeta yana dariya.
"Lafiya kalau Baaba. Ina Sani? Ya zo gida?"
Kwalla ta sake tarar
mata a karo na biyu ta kawar da kai gefe "Sani kadai ka sani ba ka cigiyar
sauran?"
Uwargidan Mal. Sa'adu
tana jinsu ta murmusa da gayya ta ce "Wai wane Sanin ake zance ne? Ko
marigayi?"
Mari ta dubeta cikin
bacin rai ganin Abbati ya juya da sauri.
"Haba Yaya Deluwa
kya dai bari ko abin ci ne yaci mana."
"Au, wai dama bai
ji labarin mutuwar kanin nasa ba?" Deluwa ta furta kamar bata ji me Mari
ta ce ba.
Abbati sai ya matsa
kusa da ita hankalinsa a tashe.
"Iya Deluwa wane Sanin ne ya rasu?"
Sauran matan gidan duk
sai suka fito aka dinga cewa "Allah Sarki" da karyewar murya mai cike
da alhini. Yanayin tashin muryarsu kadai sai yasa mutum yaji babu dadi.
"Sani ai ya kusa
arba'in biyu a kabari. Yaro yunwa da rashin gata suka yi ajalinsa." Inji
wata faccalar ta ta.
Deluwa ta cafe da
saurin kwabarta "ko kiyaye bakinki dai. Ah to. Malam ya ce mutuwar jahadi
ya yi tunda a bakin neman ilimi ne."
Wani irin kuka Abbati
ya saka yana zubewa a wurin. Mari da ta sami damar motsawa ba ita ta tsaya ba
sai a tsakar dakinta. Ita ma nata kukan take yi har Abbati ya shigo ta share
idonta da sauri.
"Zauna in zubo
maka abinci. 'Yan uwanka ma babu wanda yaci suna jiran dawowarka."
"Baaba da gaske
saboda yunwa Sani ya rasu?"
Tambayar ta daki
zuciyarta. Ta laluba ta rasa amsar da ta dace ta bashi.
"Bana son yawan
tambaya. Almajiranci ne anyi an gama. Ka dawo kenan ba za ka koma Kano
ba."
Nan fa Abbati ya yi
wuf ya mike yana mai tuno Munzali da abin da suke yi sannan da irin abincin da
suke ci wanda bai taba samu a kauyen.
"Ni dai zan
koma."
Bata kawo komai ba a
ranta illa gargadin da tayi tsammanin anyi masa akan kada ya zata ya gama
karatun kenan. Kannensa mata ta kira suka hadu su hudu ta zuba musu abinci a
babban farantin da ya kasance murfin fanteka. Shinkafa ta dafa musu wadda ta
kwana hudu tana tsinta. Sai miyar dage-dagenta da tasha naman zabi taji gishiri
da kafi zabo (vedan).
Farincikin ragowar
yaran a bayyane yake. Cikinsu babu wanda bai hadiyi yawu ba tun kafin ta ajiye
musu abincin. Naman ta saka musu yanka dai-dai shi kuma Abbati guda uku.
Abin dariya da ban
tausayi ya hade duka lokaci guda. Ci suke kamar mayunwata yau an sami shinkafa.
Abbati kuwa loma daya ya yi da kyar ya kasa ci. Ko kadan girkin da mahaifiyarsa
ta sha wahalar hada kayan yinsa da wahalar girkawa bai burgeshi ba. Salam
haka yake jin dandadon girkin. Miyar ma a idonsa bata yi kyau irin na wadda ya
saba ci ba. Ga kannensa suna ta wawa shi kuwa shinkafa ma har ta soma
gundurarsa.

No comments