Breaking News

RAYUWAR BILKISU Part 2 page 3

Rayuwar Bilkisu

Part two

By

Nafeesat m.aliyu

(Feenah)

Mutane na tambayata game da part 1 if kina buqatar shi kimun magana ta wannan no din 07062481557 nagode

Bissimillahir rahmanir rahim

(Tabbas awannan lokaci acikin rayuwar mu dole saimun kasance masu taka tsantsan game da wannan rayuwa dama gudanar da rayuwar tamu,domin tabbas yanayin rayuwa dama wayewar zamani na Kuma daduwa akowane

lokaci,tabbas saimun kula sosai ta hanyar yanda zamu tafiyar da rayuwar mu ta yadda zamu tsira da mutuncin mu dama tarbiyyar mu fatan dai shine Rabbi ya datar damu ya tsaremu ya tsare alummar musulmi baki Daya ameen summa ameen)



Yauwa insha Allah zamu cigaba da posting din wannan book na ratuwar Bilkisu har Allah ya nuna mana karshen wannan book saidai ina mai neman afuwar,masu karatu game da bazan iya yin update a kowace Rana ba,haka kuma duk bayan kwana biyun ma ina ganin abune mai wuyar yuwuwa saboda yanayin rayuwa da sabgogi,hakan yasa nake baku hakuri akan insha Allah zan nayin posting sau uku akowane week insha Allah kuma zan fadada muku kowane page insha Allah,next page zan sanar muku da ranakun dazanna posting,abunda nake buqata daga gareku Kuma shine comment da addu'oin ku domin suke bamu kwarin gwiwa akoda yaushe rashin hakan Kuma zai hana abubuwa tafiya yanda muke buqata,nagode👏🏻



♦️♦️♦️ Page 3


Tabbas iyayen mu sun mana nasiha mai matuqar shiga jiki da kashe jiki dama raunana zuciya musamman ma ni,da wannan nasiha ta kuma tunomun da Inna ta haqiqa awannan rana na shiga matuqar kewarta wacce ni kadai nasan halin da zuciyata take ciki dukda iya kokarin danake wajen danneta,sosai jikina yayi matuqar sanyi yayinda idanuwana ke zubar da hawaye babu sasssauci,koda muka taso daga wajen su Abban mu sosai nayi dauriya wajen kai kaina daki,saboda wani jiri dake dibata wanda hakan ya samo asaline da yadda kaina ke sarawa tamkar zai cire,ina shiga daki na zube bisa cinyar Inna maimuna tare da sakin wani sassan kuka yayinda nake runtse idanuwa kasan cewar kaina dake sarawa babu sassauci, Inna maimuna ce tashiga rarrashi na tare da gwaggwo jimmai cike da tausayawa,tare da karamun nasiha mai matuqar sanyaya zuciya cikin da Dadan kalamai Wanda hakan ya sanyaya mun zuciya matuqa tare da raqemun radadin da takeyi,cikin haka naji jirin motoci akofar gida Wanda naji tsayawar su tamkar a kahon zuciyata,hakan yasani lumshe idanu yayinda wasu zafafan hawaye ke Kuma sauka bisa kunci na,haka inaji ina gani aka futa dani bayan kaini gun Inna Asabe da Inna maimuna tayi da nufin tamun nasiha sannan muyi sallama Dan za'awuce dani,dukda bawata tarba nasamu daga gareta ba,haka dai aka dunguma Dani,yayinda alokacin nakejin ai antafi Kai mariya wacce zata tare abayan layin mu kasancewar mijinta Dan cikin unguwarmu.



Cikin nutsuwa motocin damuke ciki suka daidaita parking d'insu cikin tamfatse tsen compound din dake family house din nasu,dukda kaina na kasa babu abunda ke yawo bisa kuncina sai hawaye,da haka naji Inna maimuna ta kama hannun na tana fad'in nafito da bissimillah kamar yadda ta umarce ni kuwa hakance ta kasance, direct bangaren Hajiya Kaka aka nufa dani kamar yanda naji ance daga nan muka nufi bangaren Umman Dr. Sosai kuwa dangina dama ni kaina muka samu tarba ta musamman daga gareta,inda daga bisani dangina suka wuce bayan nasiha da suka Kuma yimun mai shiga zuciya,niko ina zaune kusa da Umma,kallo na Umma tayi cike da kulawa batare datace komai ba naga tadauki wayarta tare da kokarin kira, ringing Daya biyu aka daga"son kana inane inason ganinka"shine abunda tafada tare da yanke wayar.


Kallona Umma tayi tare da fad'in tashi muje 'yata ki cenza kayan nan kisa marasa nayi,mikewa nayi tare dabin baynta yayinda zuciyata ke cike da murnar Allah yasa anan din zan zauna kamar yanda zuciyata ke tunani,domin tabbas nafusan zama da Umman awannan lokacin.


Doguwar riga Umma tabani na cenza mara nayi tare da Dan kwanciyar bisa  capet din dake malale a Dakin kasancewar ina hutun sallah, murmushi Umma tayi wacce ta idar da sallar wutirin ta yayinda adaidai wannan lokaci akayi sallama abakin kofar tare da turowa cike da nutsuwa,ganin Wanda yake kokarin shigowa dakinne yasani saurin lumshe idanuna yayinda zuciyata ke wani irin buqawa, murmushi Dr.ya saki mara sauti ganin saurin lumshe idanu da tayi tare da karas

wa gefenta ya zauna yana fuskantar Umma cike da kulawa"yauwa dama neman danake maka matarka zaka kawowa magani naji jikinta akwai zazzabi" ta karashe maganar yayinda idanunta kekan Dr. "Toh Umma ya fada yayinda yake Kuma kallon Bilkisu dake gudundune cikin hijabi,jin karar rufe kofar danaji anyine yasani saurin bude idanuna domin azatona shine ya futa amma me ina bude idanuna karaf muka hada idanu......



Rabbi ka datar damu ka jikan iyayen mu🤲🏻

No comments