Breaking News

SILAR ABAYA 2

 *SILAR ABAYA*    

        BY

   *HILFAT*


*PAGE* 2️⃣


Ita kuwa tanayin post din ta sauka sakamakon kiran da ya shigo wayarta, tsaki taja ganin mai kiran dan ita yanzu haushi yake bata, tana gani kiran ya katse, kashe datar tayi sannan tà ajiye wayar, wani kiran ne ya kuma shigo wa wayar tata, da kamar bazata d'agaba sai kuma ta d'auka, shiru tayi, shikuwa daga can bangaren yace,


"Amaryata ina jiranki a waje,"


Bai jira cewarta ba ya katse kiran, ajiye wayar tayi ta koma ta kwanta, can taji wayar na ruri, banza tayi da ita, mamanmu ce tace,


"Ameenatuu ba kiranki ake a wayaba kinaji,?"


"Inajinshi mama shareshi kawai,"


"Wane kike cewa a share d'in?"


"Ameen ne wai ke kirana ni kuma bazanje ba",


" Akan me zai tako yazo gunki kuma kice bazaki fitaba, ko kin manta ya kusa zama miji agareki?",


"Mama fad'a mukayi dashi shine kuma ya wanizo yau, to yadda yazo haka zai koma dan bazan fitaba,"


Girgiza kai kawai tayi sannan tace,


"Yanzu saboda kunyi fad'a shine bazaki fitaba, ai daman ana irin wannan fad'an dan haka ki tashi kije kinji dai na fad'a miki,"


Tashi tai ta janyo hijab d'in sallahrta ta zira ta fice tana zumb'ura baki,

Shikuwa har ya gaji da tsaiwa ya fara fitar da rai zata fito sai jin motsin fitowa yayi, hankalinshi ya maida kan k'ofar itace kuwa ta fito, da kallo ya biyota har ta k'araso gurinshi, ko sallama batayi mai ba ta juyar da kanta gefe,


Shikuwa murmushi yayi sannan yace,

  "Wai laifin me nayi aketa fushi dani haka?",


Shiru tayi bata bashi amsa ba,


" Dan Allah ki sanarmin kinsan banason ganinki cikin damuwa,"


Harararshi tayi sannan tace, 


"Au kai ka manta me kayimin kenan, to ai ni bazan manta ba dan kullum abin na raina dashi nake kwana nake tashi, dan haka indai bazakayimin abinda nakeso ba to kuwa ka dena ganin fara ata,"


Kanshi ne ya kulle dan har yanzu bai gane me take nufi ba, dan haka yace,


"Mene ya dameki din dahar kike kwana dashi ki tashi dashi?",


"ABAYA mana, nayi nayi kasaimin ita amman kaki, kuma ni yanzu babu abar da nake da burin mallaka sai ita, duk k'awayena samarinsu sun sai musu amman bandani saboda ni ba son farin cikina kakeyiba,"


Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke  sannan yace,


"Yanzu meenah har yanzu baki hak'ura da Abayar nan ba? ni yanzu banda kud'i, kinga biki ya taho tinda saba'ar watan sallah ne gashi ban kammala lefe ba ga gini, kuma na riga nayi miki d'inki sallah da sai in siya miki, kuma kinga tanada tsada da ace batafi dubu biyu ba sai in fasa ko wani abin nawane in saimiki amman ki kwantar da hankali ki insha Allah ko bayan mun yi aure ne zan sai miki kiyimin kwalliya da ita sai kinfi samun ladama,"


Ya k'arasa fad'a da fara'a akan fuskarshi, ita kuwa k'ara cukune fuska ta yi sannan tace,


"Ni wallahi yanzu nakeso, in ya wuce yanzu me zanyi da ita bayan an gama yayinta, ni kawai ka saimin ko ta dubu biyarce in saka a sallarnan in kuma ba hakaba karka kuma takowa guna sai da ita,"


tana gama fad'a ta juya ta shige ciki, da kallon ya bita yanajin ba dad'i aranshi, ada k'alau suke zaune da ita, har basason rabuwa da juna amman yau gashi SILAR ABAYA sun fara samun matsala, tin shigowar Abaya komai ya tab'arb'are musu, juyawa ya yi ya tafi cike da damuwa, ita kuwa tana komawa kai tsaye d'akinta ta shige, wayar ta d'auka ta kunna data ta hau online,



***A can d'aya b'angaren kuwa FEENAH ce zaune a 2 seater tana chatting, wasu tsala tsalan abayoyi ta gani an kuma turowa ana tallansu a wani group da azama ta bud'e su  ta kuma zuk'osu tana kallah, tini ta k'ara kwallafa ranta akan Abayar,


Shikuwa NAUFAL a gajiye ya k'arasa shigowa cikin parlour, yana shigowa ya zube kan kujera dan ya kwaso gajiya saboda anyi rana yau d'in, yanajin azumin sosai, Ajiye ledar da ya shig o da ita ya yi a kasa sannan ya fara sharce gumi,


Ita kuwa tin shigowarshi ledar hannunshi kawai take kallo, yana ajiyewa kuwa tamik'e kai tsaye ledar ta janyo ta bud'e, ganin ba abinda tai zata bane ya sanya ranta b'aci, juyowa ta yi ko sannu da zuwa batayi maiba ta hau fad'in,


"Wai kana nufin yauma baka siyomin Abayar ba,? wai me kake nufine,?"


ta fad'a tanayi mai wani mugun kallo, shikuwa a hankali ya bud'e idinshi jin maganar ta akanshi........!

No comments