SILAR ABAYA 1
🙆🏻♀️🙆🏻♀️🙆🏻♀️🙆🏻♀️🙆🏻♀️
🙆🏻♀️🙆🏻♀️🙆🏻♀️
🙆🏻♀️🙆🏻♀️
🙆🏻♀️
*SILAR ABAYA*
🤦🏼♀️🤦🏼♀️🤦🏼♀️🤦🏼♀️🤦🏼♀️
🤦🏼♀️🤦🏼♀️🤦🏼♀️
🤦🏼♀️🤦🏼♀️
🤦🏼♀️
By
Fatima umar kas
(Mummyn mihal)
*PAGE* 1️⃣
"Mamanmu pls ki taimakeni ki taimaki rayuwata ki saimin ABAYAR nan, dan allah"
Wata matashiyar budurwa ta fad'a kamar zatayi kuka,
D'agowa dattijiwar matar dake tankad'en garin tuwo tayi tana kallonta cike da mamaki akan fuskarta, ido ta zuba mata ganin yadda tai tsaye akanta tana turo baki,
Girgiza kai ta yi sannan tace,
"Yanzu wai Ameenah bazaki bar maganar Abayar nan ba? Kinyimin maganar tun tini na fad'a miki banda halin siya miki ita, kuma jiya da dare naji mahaifinki na miki fad'an abayar nan ta fita abakinki ki dainayi mishi maganar ta, kinje daga dawowarshi ko sannu da zuwa bakiyi maiba kin fara tambayarshi abaya, bayan yadda ya fita haka ya dawo, amman shine baki daddara ba kika kuma zuwa kinamin maganar ta yanzu ko?".
Ta fad'a tana hararra ta, ita kuwa kuma gyara tsaiwa tayi sannan tace,
" Nidai mamanmu ki tausayamin ko aron kud'ine kiyi ki sayamin bayan sallah a ware dan ni indai ban mallaki abaya ba ko k'ofar gida bazan lek'aba da sallahr nan,"
Kuma sakin baki mamanmu tayi tana kallonta ganin da gaske take har wani a tausaya mata take cewa sai kace in an saka abayar ganin annabi ce,
"Niba zan je na ranci kud'i saboda keba akan wata abar yayi, Abayar nan fa sallah na wucewa angama yayinta kenan, kuma naga yaron nan AMINU yayi miki d'inkin sallah amman bai ishekiba sai kin kwallafawa ranki wata abaya?"
Juyar da kanta gefe tayi sannan tace,
"Ni wallahi banason wannan kayan yanzu Abaya nakeso, kuma fa duk k'awayena an sai musu amman ace yadda akeyimin kallon babbar yarinya ni na kasa mallakarta, dan Allah mamanmu ko dashinki ne ki amsa ki saimin,"
"Na fad'a miki bazan siyaba, ko inada halinta balle yanzu mu ta abinci ma muke, kuma na k'uk'uta na tara kud'ina kikasan me zanyi dashi kawai sai na kwashe nayi miki abinda ranki keso? To wallahi karki kuma yimin maganar Abayar nan, in kika kuma kam ranki zai b'aci, danni yanzu har na fara jin haushin abayar ma,"
Jin abinda mahaifiyar tata tacene ya sanyata shigewa d'aki da gudu ta fad'a kan katifarta zuciyarta na Suya, janyo wayarta tayi ta kunna data tahau Facebook, tana hawa tai post da
*BAZAN TAB'A DAINA KUKA BA SAI AN SAIMIN ABAYA*😭😭😭
TK boy dake kwance a d'akinshi yanashan iskar fanka wayarshi ce rik‚e a hannunshi, ya hau online, ganin post din ne yasanyashi saurin mik'ewa zaune, hannunshi har rawa yakeyi gurin saurin shiga wajenta, yaci sa a kuwa hotonta ne ta d'ora kan dp d'inta, cike da zumud'i ya shiga cikin wajenta ya bud'e hoton,
Cike da maita yake k'are mata kallo bayan yayi zummin na hoton sosai, tabbas batada makusa ta had'u takoina dan kyakykyawa ce ta k'arshe, komawa yayi yayi searching na sunanta da ya gani MEENA BABY, yana shiga ya fara cin karo da hotunanta birjik a farfajiyarta, d'aya bayan d'aya ya farabi yana d'aukosu zuwa kan wauarshi, sai da ya gama sannan ya shek'e da wata shegiyar dariya da fad'in,
"Yarinya kin shigo hannu, badai abaya kikeso ba? Zaki samu ko kala ashirin kike buk'ata,"
Friend request ya tura mata sannan ya tsaya jiran ta amsa, wayar na hannunshi yanaci gaba da k'arewa surarta kallo..........!
*HILFAT*✍🏽✍🏽✍🏽
No comments