Rayuwar Bilkisu 1
💓💓💓🧕🏻💓🔐
Rayuwar Bilkisu
Part two
FREE BOOK
By
Nafeesat m.aliyu
(Feenah)
Ina yiwa "yan uwa musulmin dukkanin duniya barka da sallah dafatan munyi sallah lafiya,Rabbi ya amshi ibadin mu yasa muna daga cikin bayin da,aka 'yanta acikin wannan wata mai alfarma,ya maimaita mana.
♦️♦️♦️ Page 1
Bissimillahir rahmanir rahim
Haqiqanin gaskiya awanann rana zukatan mutane da yawa na cikin yanayi,daban daban yayainda zukatan wasu ke cike da farin ciki da annushuwa dama wadan da nasu zukatan ke dauke da akasin haka,toh abangaren Inna Asabe ma hakan ce ta kasance yayinda tama kasa fayyace asalin halin da zuciyarta ke ciki awannan rana,tabbas dai tasan tana cikin farin ciki mara misaltuwa kasan cewar awannan rana ta aurar da tilon 'yarta Mariya ranar da tayi shekara da shekaru tana jira,saidai tabbas ranar tazo mata dawani salo wanda shine sanadin gurbatar farin cikin ta awannan rana,wanda ya kasance abubuwa biyu ne ke dawainiya da zuciyarta tsantsar baqin ciki da kyashi Wanda harma yake kokarin mamaye farin cikin da zuciyar tata ke dauke dashi.
Murmushi talatu ta sakarwa Asabe yayinda suka hada ido tare da fad'in"nadai fada miki qawata ki cigaba da dannewa batare da ranar farin cikin ki ta lalace ba sanadin wannan irin tsiyar"daga mata Kai Inna Asabe tayi tare da cigaba da gudanar da shagalin bikinta tare da yiwa masu kidan kwarya liqi wanda suke zaune a tsakar gidan.
Dr.khamal na hango cikin aboka nansa Wanda suke kokarin tafiya gida,kallo Daya na masa na fahimci tsantar farinciki da wannan baya yake ciki awannan rana,tare da gayu dayaci na musamman cikin wata milk colour din shadda wacce daka ganinta kasan kudi yayi kuka wajen siyanta harma da d'inkin,direct gidan gonar alhaji Ahmad suka nufa inda zasu gabatar da gaya tacciyar walima ta musamman ayammacin wannan rana wacce zata samu halattar mutane da dama.
Kamar yadda Hajiya sauda ta tsara kuwa babu wani taro data,gabatar awannan Rana har sai zuwa lokacin tariyar Bilkisu kamar yadda ta tsara,itadai fatan ta shine Allah ya kauda futuna awannan zama, musamman daga bangaren Surayya wacce tasan futuna zata iya samu daga wajenta,domin tana lura da yadda Hajiya Hajara ta cenza tun lokacin da akayi maganar auren nan,kuma sarai tasan futunar Hajara hakan yasa take addu'ar Rabbi ya kauda futuna,wannan itace fatan ta game da wannan aure dama addu'ar ta.
**
Wani murmushin takaici Surayya ta saki wacce ke zaune a bangaren Hajiya Hajara,zuciyar nan tata jinta take tamkar ana kunna mata wuta acikinta,haqiqa ayau zuciyarta tana mata kuna fiye da kullum,kuma ayau ta Kuma tabbatarwa kanta zata iyayin komai akan mijinta,domin ita kadai tasan abunda takeji acikin zuciyarta mai wuyar fassaruwa,qarar ringtone din wayarta ne yayi sanadin dawo mata da hankalin ta kan wayar,bayan dogon tunanin da zuciyarta tayi nisa aciki,jajayen idanunta ta sauke akan screen din wayar tare da zubawa sunan dake yawo bisa kan wayar,cikin sanyi ta dauki wayar tare da karata bisa kunnenta"yanaji muryarki haka bakida lafiya ne?"
Murmushi Surayya ta saki tare da fad'in"Besty an daura fah"what? Kardai kicemun auren aka daurawa mijinki kike zaune"Besty ya zanyi wannan aure fah sai andaura shi,walahi bakiji yanda zuciyata ke tafasa ba na rasa mekemun Dadi awannan duniya amma,kema sanin kanki ne,ja da baya ga rago ba tsoro bane,wallahi babu shegiyar da zata shigo gonata ta zauna lafiya,wannan alqawari nane Kuma kema kinsan Surayya ba kanwar lasa bace musamman akan abunda nakeso" "haka yake Besty bansan ki da sanyi ba kuma ban sanki da dagawa duk Wanda ya shiga gonarki kafa ba koh kadan, sorry Besty bari nayi picking call zan kiraki letter"ta karashe maganar tare da yanke kiran baki daya,wani numfashi mai zafi ta busar tare da gyaya kishin gidarta tana jiran mahaifiyar tata wacce tun futar ta dazu bangaren Abban su shuru bata dawo ba.
Rabbi kazama gatanmu kai mana kyakkyawan karshe🤲🏻
Karku manta more comment more typing domin comment d'inku shine gwarin gwiwar mu akoda yaushe.
No comments