Breaking News

RAYUWAR BALKISU 2

 💓💓💓🧕🏻💓🔐


Rayuwar Bilkisu

Part two

FREE BOOK

By

Nafeesat m.aliyu

(Feenah)

Bissimillahir rahmanir rahim

  • ('yar uwa kiyi sani cewa mutuncin ki yafu komai daraja agareki kada ki biyewa rud'in zamani ko san wani abun duniya wajen wofantar,da mutuncin ki,domin kare mutuncin ki tamkar kin kare darajar itayen kine,domin kuwa tabbas ahalin yanzu damuke ciki awannan rayuwa saimun jajirce sosai,wajen kare mutuncin mu,dama addu'oi sosai dafatan rabbi ya tsare mu ya tsaremana mutumcin mu ya bamu kariya,ya mana kyakkyawan karshe ameen ya hayyu ya qayyum🤲🏻)




♦️♦️♦️ Page 2


Sosai nakejin wani yanayi na daban atare dani musamman aduk lokacin da kalmar nazama mallakin sa tafado mun acikin zuciya,tabbas bansan wane yanayi zan fassara zuciyata take ciki awannan rana ba,saidai agaskiyar magana ayau zuciyata ta kuma dawowa sabuwa dal game da rashin jigon rayuwata danayi wato mahaifiyata,tabbas nasan zatafu kowa farin cikin ganin wannan rana agareni,tabbas ahalin yanzu addu'ata take buqata wacce nake mata akoda yaushe,tare da yin rayuwata cike da tsafta da biyyar aure domin ganim nima nasamu tawa aljannar kamar yadda nakejin mahaifina na yawan yabon mahaifiyata dare da rana akan rabbi ya mata rahama,ya kyautata mata kamar yadda ta da d'ad'a masa a rayuwa,wanda hakan ya samo asaline ta kyawawan halayen mahaifiyata,tabbas inaso nayi koyi da dukkanin halayenta domin nima ina fatan na dace a duniyata dama lahirata,(tabbas auren d'iyar mace tagari yakanyi naso ga zuri,arka koma sabanin haka domin ita zata kwaikwayi dabi'ar mahaifiyarta yayainda suma "yayan ta zasu kwaikwayi dabi'ar tasu mahaifiyar,haka ma miji shiyasa ake fatan ki auri namijin da kika aminta da tarbiyyar sa data ahalin sa domin tabbas hakan zaiyi naso ga zuri'ar ku,rabbi yasa mudace ameen) sosai naci gayuna cikin wata tsadaddiyar shadda wacce kallo Daya zaka mata ka fahimci akan kashe kudi masu yawa wajen siyanta,Inna maimuna ce tashigo tare da Inna Habiba matar Yayan mahaifina bakin su dauke da sallama,dago jajayen idanuna nayi ina amsa musu sallamar wanda kallo Daya zaka musu ka fahimci hawaye sun zuba  acikin su, murmushi Inna Habiba ta sakarmun yayinda muka hada idanu tare da karasowa gareni baki dayan su,sunkuyar da kaina nayi batare danace komai ba "'yata har yanzu kina nan zaune"daga kai nayi batare dana furta komai ba, murmushi Inna maimuna ta saki tare da fad'in "ai wannan 'yarta ki kam babu inda ta motsa tun dazu takenan zaune,amma yanzu dai kitashi haka Bilkisu ga ruwa cen nahada miki a bandaki kiyo wanka kizo kishirya sannan mahaifinki ma nason ganinki"cikin muryar kuka kuka da idanuna da suka fara kawo kwalla na kalli Inna maimuna da Inna Habiba"su Inna Shirin me zanyi?" Murmushi Inna maimuna ta saki tare da fad'in"'yata wannan tsoron da fargabar na menene ki kwantar da hankalin ki kinji,ki Sanya nutsuwa aranki kibi mijinki sau da kafa kiyi koyi da kyawawan halin mahaifiyar ki domin zama tauraruwa a wajen mijinki kuma sanyin idaniyar sa 'yata ki dubi maraicinki ki yiwa kanki gata dukda nasan Bilkisu tamkar Yayah Fatima ce babu abunda kika bari dangane da ita hakan yasa duk sanda na kalle ki tamkar naga 'yar uwata ne wacce ta kasance tilo agareni awannan duniya"Inna maimuna ta karashe maganar tare da sharce wasu zafafan hawaye masu gunar zuci dake zuba akan fuskarta.


Ganin hakan ne yasa Inna Habiba ta shiga rarrashin Inna maimuna tare dani dama yimana nasiha mai ratsa zuciya da sanyaya zuciya gamai sauraro,da haka naje nayi wankan kamar yanda Inna ta umarce ni,tare da shiryawa cikin wata hadaddiyar atamfa mai kalar copy da milk ba kuwa garamun karbata tayi ba kasance wata mai haske tare da gyaran Dana sha wajan Inna maimuna harma da gwaggwo ta,wanda hakan ya kara futo da hasken fatata,gurin su Abba Inna maimuna ta nufa dani,anan nasamu Mariya zaune da alamar ni ake jira.....


Rabbi kai mana kyakkyawan karshe ka biya mana buqatun mu ka amshi ibadin mu alfarmar annabi da al Qur'ani🤲🏻


Taku har kullum Nafeesat m.aliyu

(Feenah)


Karku manta more comment more typing🖊️

No comments