DIJA QAYA 25
🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋
*DIJAH QAYA*
*page* 2⃣5⃣
Sauda ta jawo mata kujera ta zauna tafara saving nasu, sai da tagama zuba na kowa ta zauna dai2 lokacin Mami ta gama wayan ta kalli Dijah ta ke takure acikin kujera "Kici Abinci Khadijah, nanfa gidankine kidaina d'ari2,Haka suka ci Abinci Mami tana musu Hira jifa2 takansako Dijah aciki dak'yar tad'an saki jikinta, Rana ta farko arayuwan Dijah data kwanta dasunan Barcin dare ad'aki ita d'aya gaba d'aya jitayi d'akin yamata mugun girma Allah sarki Bintalona ta fad'a tana share guntun Hawayen da yagangaromata, juyi ta dinga yi ahaka har bacci yayi gaba da ita.
Washi gari akaci gaba da shagalin buki yayinda Mami tad'auko masu Gyaran Amarya nagaske duk abunda akyi wa Amarya Mami tasa anyima Dijah,
Kafin yamma inkinga Amarya da k'anwanta bazaki ganesuba gaba d'aya kamanninsu ya canza, aharaban Gidan aka gudanar da tsararren Walima daya d'ibi maza da Mata,
Angoda da Amarya sai Haska waje suke kaman wasu taurari, sai daf Magriba aka tashi,
Duk abunda akeyi Dijah tana takure akan kujera dama ita ba gwanan shiga taroba, gawani Kwalliya da akamata gaba d'aya tana jin fuskanta yamata nauyi, tun daga nisa tajiyo Muryan sani yana k'wala mata k'ira ta tashi ta isoshi sai Kallonta yakeyi yana murmushi "Khadijah kece haka gaba d'aya banganekiba? Murmushi kawai tayi tace " ya Sani kaima ka ganka kuwa da muryanka kawai naganeka,
Kai da Bintalo sai kace ansakemu ku wani k'ira. Sani yad'an had'e rai "ke Daga yau nasoke wannan Sunan Aunty Fatima zaki dinga cewa ba Auntynki bace ba,
Dijah ta k'yalk'yale da Dariya "ok dariya ma nabaki? Insake jin sunan abakinki,
Zo muje kigaisa da su Hajiyata, yana tafe tana binshi abaya suka shiga pert d'i n da 'yan'uwansa suke, sosai Hajiya taja Dijah ajiki, tajima awurin suna Hira,
Harsaida Mami tanimeta.
Bayan Walima ba abunda aka kumayi awajen don Mami tace Albarka ake nima baza'ayi abunda yasab'a ma shari'a ba,
Sai washi gari aka kai Amarya gidanta tare da Rakiyan 'yan'uwata, Bakaramin kokari Mami tayiba
Wajen tsara gidan Amarya komi yaji saidai fatan Allah yaba da zaman lfy,
Washi garin kai Amarya ne 'yan'uwanta da 'yan'uwa Ango sukayi shirin komawa Garinsu, lokacin dasukazo tafiya and'an fafata da Dijah don tace sam Baffanta bai Amince ta zaunaba,
Harsai da Mami ta k'irashi awaya aka bata yace mata ta kwantar da Hankalinta zai zo ganin d'akin Amarya daganan sai su dawo tare (kamar yanda yake a Al'adan garunsu bayan Amarya tacika Sati Bab🙏🏼😭
anta yakanje ganin d'aki,)
Da kad'an kad'an Dijah tasaki jikinta da Mami sosai yanzu take jin dad'inzaman gidan haka tafannin abubuwa Sauda tana koyamata Sosai, tare suke shiga kicin da Mami suyi Abinci kasancewan dama Dijah bata da son jiki shiyasa ta dage kafin tacika wata uku ahanun Mami tuni ta goge ta iya abubuwa da dama, time to time takanbi Sauda suje gidansu nanma bak'aramin Experians take samuba, Mahaifiyar sauda tana bata kulawa sosai don haka tazamo bata da matsala
Dijah tana da wata Hud'u cif Mami tasamamata gurbiny karatu a Polytechnic,
Ita da kanta tad'auketa a mota takaita har cikin makaranta wajen Aminiyanta da take koyarwa a wajen takaita Malama Sadiya, a Office tasameta ta tareta da fara'a suka gaisa,
''yau wata Rana Hajiya Fati kece a Office d'ina?
Gaskiya baki da kirki gaba d'aya kingujeni,
Mami tayi dariya tace "yanzumma bahaka kawai nazoba nakawo miki Amanar 'yatace, gatanan tana nan Depertmen d'in Mass communication,
Malama Sadiya ta kalli inda Dijah take "Masha Allah Hajiya Fati 'yar waye?
"yatace pls don Allah inaso asamata Ido kinga Bak'uwace batasan kowaba kar abarta da k'awayen Banza,
"Ok bakomi akwai 'yata Nana zanhad'asu surik'a zama tare,
To nagode Mami ta fad'a tana mik'ewa dukansu tare suka fito suka tsaya ajikin Motan Mami,
Malama Sadiya tak'ira wayan 'yarta, ba'a jimaba sai gata tazo wajen, kallo d'aya tayi ma Dijah tahau yatsina fuska saidai tagai da Mami cikin girmamawa,
Nan mahaifiyarta tagabatar mata da Dijah amatsayin Sabuwar k'awa sannan ta gargad'eta da kar tabarta tayi k'awance da wasu shashashun k'awaye,
Mami tadafa kan Dijah tace "Khadijah kikula kinji? Kiyi abunda yakawoki, inkuntashi Driver zaizo ya d'aukeki akwai no. sa awayanki sai kik'irashi, cikin girmamawa tace mata "to"
Nana tana gaba Dijah tana baya ahaka suka isa ajin,
Nana tak'arasa wajen K'awayenta tad'an sukuya ta musu magana akunne gaba d'aya suka kwashe da dariya suna kallon Dijah suna nunata da yatsa,
Wani irin malolon bak'in cikine ya ziyarci Dijah...........................
*HAUSA NOVELS* 📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚📚
No comments