Breaking News

DIJA QAYA 23

 🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋🌿🦋

            *DIJAH QAYA*

             *page* 2⃣3⃣

  Dijah!  Wai gashi inji Baffa ki k'arasa shan maganinki, Dijah da take kwance akan k'atuwar katifan da ta gada awajen Kb 😆 yitayi kaman batajiba, dataga Bintalo zata matsamata sai ta d'aga k'afanta kaman irin agigin Baccinnan ta d'oramata awuyanta, Bintalo ta ture k'afan,  Dijah tasake d'agawa ta d'oramata akanta,  Afusace ta saiti cinyanta ta d'akamta duka "iyi kinga kin fara farfafad'owa Rashin mutuncinki yafara dawowa aifa banmanta abun da kikamin d'azuba.


Azabure Dijah ta tashi tana sosa wajen, ta tak'ark'are ta k'walla uban k'ara, 

"Wlh bazan yardaba sai na rama tana kuka takama Bintalo da kokuwa,


Nanfa kokuwa ya kaure, tun Bintalo tanabiyemata ta maida abun wasa har ta gaji tafara Bata hak'uri,


"Kiyi Hak'uri Dijah na kinga baki gama warkewaba, "Nidai sai na Rama ko kuma inje ince ma Baffah jiya naji kuna iskanci a waya keda yaya Sani.


"wai ke Dijah meyake damunkine?    Don kawai nace nima inasonshi shine iskancin?


"A'uzubillahi sake maimaitawa kikayi? 😳  narantse sai nafad'a tunma bakije birninba kin fara iskanci, ta fauce Hanunta acikin na Bintalo zata tafi Bintalo ta rik'ota kiyi Hak'uri Dijah ki rama dukan ince shikenan,  "nafasa Ramawa zanje kawai ingayama Inna kar akaiki Birni kije ki kwaso abun kunya.


Dariya Bintalo tayi sosai har tana sunkuyawa, kije kifad'a nima sai nafad'amata Hiran da naji kunayi keda Jebu jiya, daga Haka tafice tabarta agun.


Gyara kwanciya Dijah tayi akan katifa ta d'ora kanta akan pillow tana shak'an k'amshin turaren Kb dayazamo mata jiki, Don tun tafiyan su Kabir tamayar da d'akin wajen zamanta kwanane kawai batayi a wajen k'anshin turaren da yake fesawa har yanzu yana d'akin kaman yanzu ake fesawa itakuma a duniya k'amshin yana mata dad'i.



 Tun ana biki saura kwana Biyar Mami sukazo da kayan sayan baki dakuma d'inkunan da Amarya zata saka dasuran abun buk'ata kafin akaita, don dama Baffa yace a ajiye mata lefenta acan tunda nan za'a kawota.



Tun Randa Mami ta dirk'o take fafatawa da Baffa akan yabata Dijah sutafi fir yak'i amincewa.


Suna zaune da Dijah tana nunamata sakamakon Karatunta tafara wani tunani itadai tanason yarinyan aranta, tanason ta taimaka mata tasamu karatu mai inganci, "khadijah kinason kicigaba da karatunki? 


 Dijah ta d'ago tana kallonta, tace "Eh inason incigaba Hajiya wlh inason in zamo mai aiki gidan T.v Mami tad'anyi Murmushi tace nifa Mamin kece ba Hajiyaba, kinji? 


Ta gyd'a kai, 

"Kinason intafi dake kije kiyi karatunki acan?


 Dijah tazaro ido "Eh inaso amma Baffana bazai yardaba, "Karkidamu nasan Hanyan dazanbi lnsha Allah zai yarda dake za'azo bikin Fatima kinji? 


Kayan da tazomata dasu ta bata sannan ta nunamata yanda zatayi amafani da wasu.


Washi gari Mami da zata tafi tashiga wajen Baffa tajima kafin tafito jiki ba k'wari, Dijah tana ganin haka tasan Baffanta bai aminceba.


Ahaka tamusu sallama Har jikin mota suka rakata tafi.



  *Ranan Juma'a* shine Ranan da Baffa yasaka d'aurin auren Bintalo awannan Rana mutanen Rugan Juma sunga Abun Mamaki dayawa wasu kam sun sadauk'ar cewa Baffa yasayar da "yarsa mai Hankali yabar Mashiririciya agida sakamakon  Irin Motocin dasuka shigo garin wanda tsawon Rayuwansu da yawansu idonsu bai tab'a Ganinsuba, gasu fa tsaban yawa nanfa akafara gutsiri  tsoma hatta matan dasuke cikin Gida lbr yakaimusu haka wasu sukazo sunayima Bintalo kallon k'arshe kallon muhad'u a darussalam,  wasu  sai lbrai sukeyi wata wani yazo daga birni ya kashe kud'i mai yawa  ya aureta asai ba'asanta d'an yankan kaibane ana kaitan shikena haryau shekaru kaza ba lbr.


Ire2 labarun da akeyi kenan agidan bukin wannan tanagamawa wancan taba dana ta,  Inna kam yitayi kaman batasan me suke nufiba dondama tasan za'afad'i abunda yafi haka.


 

Hakadai har 'yan kai Amarya sukafara shiga motoci, nanma ba kowa bace tayarda tashiga don sunce basu shirya kai kayikansu ma 'yan Birniba.


Sai Daf Magriba suka isa Gidan Mami aka kaisu kai tsaye,  wani k'aton pat aka ajiye Amarya da Bak'inta, Hidiman da aka musu ba'a magana, Mami tana idar da Sallahn Magriba ta shiga pert d'in Bintalo tana ganinta ta lullub'e fiska dariya tayi tace kwantar da Hankalinki Amarya ba gunki nazoba nazo niman 'yatace, tazauna agefe suka gaisa da jama'a annantace musu Ina Khadijah? Can ta hangota suna zaune dasu Ma'u Taje ta kamo Hanunta suka fita, bata ajiyeta ko inaba sai part d'inta,


Wani d'aki dayake cikin Falon k'asa ta kaita da alamu kayan ciki basufi sati dasawaba komi sabone dal ad'akin abakin k'ayataccen gadon dayasha gyara ta zaunar da ita,


Ta jawo stool d'in Mirrow ta zauna tana fuskantan ta.

 

"Haba Khadijah uwata!! Kinzo konimana bakiba kinacan cikin 'yan'uwanki kin shareni nikuma inannan ina d'okin ganinki,


 Murmushi Dijah tayi tana bin d'akin da kallo zuciyanta sai Harbawa yakeyi da sauri2 Haka kawai yau kuma taji wani iri game da Mamin Anyah kuwa Maganan mutanen garinsu bazai tabbataba irin wannan Gida? Ashe haka suke rayuwa shine har suke iya zuwa Rugansu suna zama. 


Gaskiya itama yaukam tana ganin sayar dasu za'ayi dukansu, 


Mami ta kamo hanunta kaman tasan abun da take tunani tace "ki kwantar da Hankalinki Khadijah Bazamu tab'a cutar dakuba insha Allah.


 kusa aranku kowa da yanda Allah ya tsaramasa Rayuwansa wannan shine banbancinmu daku ba wani abuba, kinji ko?  


Dijah ta gyad'a kanta tana cigaba da kallon d'akin a tsorace Mami tace ina zuwa ta fita Dijah ta tashi tana k'are ma d'akin kallo ahankali tana taku, har ta iso gaban Mirrow ta lek'a azatonta taga fuskanta sai kawai taga wata matashiya atsaye ta hard'e Hanunta tana kallonta gefenta kuma watace atsaye amma bata ganin fuskanta, arazane tasa tafin hannayenta ta Rufe Fuskanta ta tsala ihu mai tsanani da sauri Mami da sauda sukayo kanta  Mami ta rik'ota "Khadijah menene? 


"wayyo Allah na don Allah amaidani wajen Baffana wlh bazan sakeba Don Allah ku maidani,


"wai meye kimin bayanimana khadija??


Aljanu nagani acikin Madubi don Allah kukaini Baffa yamin Ruk'iya. 



  Mami ta dad'a rik'e Hanunta "ba Aljanu kika ganiba Khadija mune, 


"wlh banyardaba waima kud'in ta ina kuka shigo waiyo na shiga ukuna.


Duk maganan da takeyi idonta arufe takeyinsa cikin kuka,


Sauda ko me zatayi inba dariyaba, 


Dak'yar Mami ta shawo kan Dijah har ta yarda ta bud'e idonta, "Munshigo munsamu kina kallon d'kinki Khadijah shiyasa muka tsaya muna kallonki, Mu kika gani a madubin ba Aljanuba kinga wannan tanumata Sauda ita kikagani a mdubin ko ba itaba? 


"itace to amma ta ina kuka shigo?


"ta k'ofa muka shigo Khadijah ki kwantar da hanakalinki,


Nan d'akinkine ke kad'anki na kawomiki k'anwanki ta gwada miki yanda zakiyi wasu abubuwane, kallon sama da k'asa tayima Sauda sannan ta kalli Mami "Wannan gundu memiyance k'anwata?  


"Af Addanki ce na manta, Sauda ki nunamata yanda zatayi amfani da bayan gidan tayi wanka ga kayanta akan gado intafito tasa sai kuzo muci Abinci, daga Haka ta juya ta fita.


Sauda tana Murmushi tace  "zomuje Beutiful girl kina da kyau Amma don Allah karkisake yin irin wannan k'aran daga gani kinsaba da shine ko? Kanta ta girgiza har yanzu atsorace take cikin 'yan mintuna kad'an, sai ga Dijah ta koma Khadijah tare suka  fito suka tarar da Mami akan Dinining suna waya da Kabir,..........................






*HAUSA NOVELS* 📚

*HAUSA NOVELS* 📚📚

*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

No comments